Yadda Taliban ke bibiyar rayuwar miliyoyin al'umma ta kyamara

Ana amfani da dubban kyamarori domin bibiyar rayuwar al'ummar Kabul
Bayanan hoto, Ana amfani da dubban kyamarori domin bibiyar rayuwar al'ummar Kabul
    • Marubuci, Mahjooba Nowrouzi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afghan Service, Kabul
  • Lokacin karatu: Minti 5

A cikin wani babban ɗaki, da manya-manyan talabijin maƙale a kan bango, cikin tunƙaho, ƴansandan Taliban na bayyana sabbin kyamarorin tsaro guda 90,000 da suka sayo a bayan-bayan nan, waɗanda suke amfani da su wajen bibiyar rayuwar miliyoyin mutane.

"Muna bibiyar dukkanin abubuwan da ke faruwa a birnin Kabul daga nan," in ji Khalid Zadran, mai magana da yawun shugaban ƴansandan Taliban, yayin da yake nuna wani makeken talabijin.

Hukumomi sun ce maƙasudin hakan shi ne domin yaƙi da aikata laifuka, sai dai wasu na ganin cewa za a yi amfani da su ne wajen gallaza wa masu bambancin ra'ayi da kuma sanya ido don tabbatar da kowa ya bi, sau da ƙafa, tsauraran dokokin sanya sutura na gwamnatin Taliban mai tsattsauran ra'ayi ƙarƙashin tsarinsu na shari'a.

BBC ce kafar yaɗa labarai ta farko da aka bari ta ga yadda ake tafiyar da wannan lamari.

A cikin ɗakin tafiyar da lamurran sanya idon, jami'an ƴansanda na zaune suna lura da abubuwan da ke faruwa ta akwatunan talabijin masu ɗauko hoto ka-tsaye daga dubban kyamarorin tsaro, inda suke bibiyar rayuwar mutane miliyan shida da ke birnin Kabul.

Ana lura da komai, kamar lambar motoci da fuskokin mutane.

"Idan muka tsinkayi wasu gungun mutane a wata unguwa suna wani abu da muke tunanin shan ƙwaya ne ko kitsa aikin laifi ko wani rashin gaskiya, sai mu tuntuɓi jami'an ƴansanda da ke kusa da su," in ji Zadran.

"Sai ƴansanda su dira wurin da wuri su binciki ko mene ne ke faruwa."

A lokacin tsohuwar gwamnati, Kabul birni ne da ke fuskantar hare-hare daga ƙungiyoyi irin su Taliban da IS, sannan ana samun aikata laifuka kamar garkuwa da mutane da satar motoci. Lokacin da Taliban ta ƙwaci mulki a 2021, sun ci alwashin dukar mataki kan masu aikata laifi.

Ƙaruwar kyamarorin tsaro masu yawa cikin ƙanƙanin lokaci a babban birnin ƙasar wata alama ce ta ƙarin ingancin yadda Taliban ke ƙoƙarin tabbatar da doka da oda.

Kafin dawowar Taliban, kyamarorin tsaro 850 ne kacal a babban birnin, in ji wani mai magana da yawun gwamnatin da aka kora.

Sai dai kuma a cikin shekara uku da suka gabata, hukumomin Taliban sun kawo tsauraran dokokin da ke taƙaita ƴancin al'umma, musamman mata. Har yanzu babu wata ƙasa da ta amince da gwamnatin Taliban a hukumance.

Mai magana da yawun Taliban, Khalid Zadran ya ce ana amfani da tsarin bibiyar rayuwar al'umma wajen yaƙi da ɓarna
Bayanan hoto, Mai magana da yawun Taliban, Khalid Zadran ya ce ana amfani da tsarin bibiyar rayuwar al'umma wajen yaƙi da ɓarna
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsarin bibiyar abubuwan da ke faruwar da aka nuna wa BBC na da tsarin bibiyar mutum ta hanyar amfani da surar fuskarsa. A wata ƙusurwa, akwai wani akwatin talabijin da ke bayyana fuskokin mutane bisa la'akari da shekara da jinsinsu, da kuma bayanin ko suna da gemu ko kuma a'a.

"Idan yanayin gari babu hazo, za mu iya janyo fuskar mutumin da ke da nisan kilomitoci kusa-kusa," in ji Zadran, inda yake nuni da da wata kyamara da aka kafa ta a kan wani titi mai yawan hada-hada..

Taliban na bibiyar hatta jami'anta. A wani wurin bincike na kan titi, sa'ilin da wasu sojoji suka tare wata mota suka buɗe bayanta, masu kula da kyamarorin sun janyo hoton kyamarar domin ganin abin da ke ciki.

Ma'aikatar cikin gida ta ƙasar ta ce kyamarorin "sun taimaka sosai wajen inganta tsaro da rage ayyukan laifi da kuma taimakawa wajen kama masu laifi". Sai dai ba a iya tantance sahihancin wannan iƙirari ba.

Sai dai ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama na nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da aikin, wane ne ake bibiya kuma tsawon wane lokaci?

Amnesty International ta ce sanya kyamarorin na CCTV "bisa kafa hujja da dalilai na tsaro zai iya zama wani tushe na ganin Taliban ta aiwatar da tsauraran manufofinta da za su take hakkin al'ummar Afghanistan - musamman mata".

Dokar ƙasar ta tanadi cewa bai kamata mata su ɗaga muryoyinsu ba a wajen gidajensu, duk da cewa ba a iya tabbatar da aiki da dokar. An haramta wa yara mata zuwa makarantun sakandire da manyan makarantu. An haramta wa mata yin ayyuka da dama. A watan Disamba matan da ke samun horo kan aikin ungozoma da ma'aikatan jinya sun faɗa wa BBC cewa kada su koma makaranta.

Duk da cewa ba a haramta wa mata zirga-zirga a kan titunan Kabul ba, amma an wajabta musu rufe fuskokinsu.

Fariba na nuna damuwa kan cewa za a yi amfani da kyamarorin wajen ƙaƙaba wa mata dokokin sanya tufafi masu tsauri
Bayanan hoto, Fariba na nuna damuwa kan cewa za a yi amfani da kyamarorin wajen ƙaƙaba wa mata dokokin sanya tufafi masu tsauri

Fariba, wata matashiya wadda ta kammala karatun digiri kuma take zama tare da iyayenta a birnin Kabul, ta gaza samun aikin yi tun bayan da Taliban ta karbe mulki. Ta shaida wa BBC cewa “akwai damuwa kan cewa za a yi amfani da kyamarorin tsaron wajen bibiyar mata wadanda ba su sa hijabi.”

Gwamnatin Taliban ta ce ‘yansanda ne kawai ke aiki a wajen da ake lura da abubuwa ta kyamarorin, kuma ta ce jami’an hukumar hisbah ba su amfani da su.

Amma Fariba na fargabar cewa kyamarorin za su kara jefa wadanda ra’ayinsu ya sha bamban da na Taliban cikin hatsari.

Ta ce “al’umma da dama, da tsofaffin sojoji, da masu hankoron kare hakkin bil’adama, da mata masu adawa da dokokin Taliban ba su iya walawa, kuma kodayaushe suna cikin boyo.

Kungiyar Human Rights Watch ma ta ce Afghanistan ba ta da kwararan dokokin kare bayanan al’umma da ake tattarawa da kyamarorin.”

‘Yansanda sun ce ana ajiye bayanan da ale tattarawa na wata uku ne kawai, sannan kuma ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce kyamarorin ba su da hadari domin ana lira da su ne a wani wuri mai tsaro bisa kulawar kwararrun jami’a.

Da alama an kera kyamarorin ne a kasar China. Akwaitunan talabijin din da ke cikin dakin wadanda BBC ta gani na dauke da sunan ‘Dahua’, wani kamfani da aka ce yana da alaka da China.

Wasu bayanai sun nuna cewa yunkurin da hukumomin suka yi na kulla alaka da kamfani Huawei na China, bai yiwu ba.

Gwamnatin Taliban ba ta amsa tambayar da BBC ta tura mata kan inda ta samo kayan na.

Haka nan kuma ana tatsar mutane kudi sanadiyyar aikin samar da kyamarorin.

Shella ta bayyana cewa an sanya ta biyan kudin gyara hanaya.
Bayanan hoto, Shella ta bayyana cewa an sanya ta biyan kudin gyara hanaya.

Mutanen da dama na cikin yanayi a Kabul da kuma fadin kasar Senegal bayan kwashe shekaru ana yaki.

Tattalin arIkin kasar na cikin matsala, to amma an dakatar da mafi hawa na cikin kudaden tallafi da kasar ke samu daga waje tun bayan da Taliban ta karbe mulki.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan 30 ne ke bukatar tallafi

“Idan mutane suka ki biyan kudin sayen [kyamarori] sai a rika yi masu barazana ta hanyar katse musu lantarki da kuma ruwa,” in ji Shella.