Hikayata 2023: Labarin BAƘIN KISHI
Majaujawar baƙin kishi ne silar jan ta ga yin saƙa da mugun zare, musamman da ya kasance ta yi amanna da zaƙin bakin mijinta kan cewa daga ita babu ƙari.
Kwatsam! Ta yi arangama da abin da ba ta yi zato ko tsammani ba daga gare shi, hakan ya sa ta ɗaukar matakin da ya je fa ta komar da na sani.
Taƙaitaccen tarihi:
An haifi Aisha Abdullahi Yabo a 1993, a garin Gusau na jihar Zamfara., ta kuma fara karatu a makarantar Shehu Balarabe Zawiyya Gusau.
Aisha marubuciya ce sakamakon yawan karance-karancen da ta yi a shekarar 2017.
Tana son labarai waɗanda suka danganci soyayya da zamantakewa ta yau-da-kullum, da kuma labarai na abubuwan da suke faruwa a rayuwarmu.








