Shin talauci na raguwa a duniya?

    • Marubuci, Pablo Uchoa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Ranar Yaƙi da Talauci: Shin talauci raguwa yake yi?

Wata mata a India tana tsintar ƙirare a kan bola

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bankin duniya ya ce India ta fitar da sama da mutum miliyan 250,000 daga talauci tsakanin 1990 zuwa 2015

Bankin duniya ya ce sama da mutum biliyan 1.1 aka 'tsamo daga ƙangin talauci' cikin ƙasa da zamani guda.

Babu shakka wannan na ɗaya daga cikin labari ne mafi daɗin ji game da ci gaban al'umma a wannan ƙarni.

Tsakanin shekarun 1990 da 2015 yawan mutanen da ke rayuwa cikin talauci (ƙasa da US $1.90 a rana) a fadin duniya ya ragu daga mutum biliyan 1.9 zuwa miliyan 735.

Haka na nufin cewa wasu daga cikin mutanen da ake wa kallo matalauta sun ragu daga kashi 36% zuwa 10% a wannan lokaci.

To amma hanyar tabbatar da waɗanda ke ciki ko kuma suka fita daga talauci ba ɗaya ba ce, mutumin da ya fito da wannan tsari ya shaida wa BBC cewa tsare-tsaren kawo ci gaba na gwamnatoci ke fitowa da su "ba su isa ga waɗanda ke cikin baƙin talauci yadda ya kamata".

Martin Ravallion, wanda tsohon daraktan bincike ne kuma babban mai taimaka wa shugaban bankin duniya, ya ce "ƙaruwar rashin daidaito tsakanin al'umma ita ce babbar matsalar da za a fuskanta nan gaba a ɓangaren yaƙi da talauci da ci gaban walwalar al'umma.

'Sauri da jan-ƙafa'

Bankin Duniya ya ce rashin janyo dukkanin ɓangarori a harkar ci gaba, da tafiyar hawainiya na ci gaban tattalin arziƙi, da kuma rikce-rikce a baya-bayan nan sun yi tarnaƙi ga ci gaban al'umma a wasu ƙasashe.

Yayin da a China da India, jimillar mutum biliyan ɗaya suka fita daga talauci, yawan mutanen da ke cikin baƙin talauci a ƙasashen nahiyar Afirka ya zarta yadda yake a shekaru 25 da suka gabata.

Carolina Sánchez-Páramo, daraktar yaƙi da talauci da kawo daidaito ta Bankin Duniya, ta ce "A cikin shekaru 10 da suka gabata duniya tana tafiya ne kan tafarki biyu."

Kuma ta shaida wa BBC cewar abubuwa huɗu ne suka haifar da hakan.

1. Banbancin ci gaban tattalin arziƙi

"Ci gaban da ake samu a ƙasashen Afirka da na nahiyar Amurka ta Kudu bai kai na ƙasashen gabashi da kudancin nahiyar Asiya ba, a tsawon wannan lokacin.

Sannan idan aka alaƙanta hakan da yawan haihuwa da ake samu a ƙasashe da dama, za a ga cewar hakan yana haifar da ƙarin ƙarancin kuɗaɗen shiga na al'umma.

"Yana da wahala a samu nasarar yaƙi da talauci matuƙar ba a samun ci gaban tatali arziki a ƙasashe.

Saboda duk wani ci gaba yana faruwa ne sanadiyyar zagayawar arziƙi tsakanin al'umma, wanda hakan zai zamo da wahala."

2. Janyo kowa da kowa cikin harkar ci gaba

Darakatan na bankin duniya ta ce duk da cewar ana buƙatar ɗorewar ci gaban tattalin arziki wurin yaki da talauci, to amma ba shi kaɗai ne abin da ake buƙata ba.

A ƙasashe da dama, ba kowa ne ke cin gajiyar ci gaban da ake samu ba, saboda tsadar kafa masana'antu abin da ke haifar da ƙarancin guraben aikin yi - kamar a ƙasashen kudu da hamadar sahara na Afirka.

Ms Sánchez-Páramo ta ce: "Aikin yi shi ne babbar hanyar samun kuɗin shiga ga talakawa.

Saboda haka idan babu guraben ayyukan yi ga talakawa, to zai yi wahala a samu ci gaba wajen yaƙi da talauci."

Ma'aikata a wani kamfani a China

Asalin hoton, Getty Images

3. Samun abubuwan more rayuwa

Ba samun tsabar kuɗi ne kawai ke haifar da ci gaba ba, dole sai al'umma na da damar samun ilimi da kuma abubuwan more rayuwa da za a iya gani a zahiri.

Ms Sánchez-Páramo ta ce matuƙar babu irin wadannan, to hakan zai yi zagon ƙasa ga ci gaban al'umma baki ɗaya a lokaci ɗaya.

Ta ƙara da cewa, misali, a Malaysia da kuma gabashi da kudancin nahiyar Asiya, "aƙalla ana samun wadatar waɗannan abubuwa ga kowa a lokaci guda."

A bisa mizani na duniya, babu talauci a Malaysia tun daga shekarar 2013 - duk da cewa ba hakan ba ne a mizanin ƙasar.

Amma idan aka kwatanta da Brazil, wadda ta yi nasara a ɓangaren hada-hadar kuɗi, talauci ya ragu daga kashi 21% a shekarar 1990 zuwa 2.8% a shekarar 2014 - amma ta zaɓi wasu inda ta kai kashi 4.8% (wanda ya shafi mutum miliyan 10) a 2017.

4. Rikice-rikice

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ƙarshe, a shekarun baya-bayan nan rikice-rikice na siyasa da na ƙiyayya sun mayar da hannun agogo baya a kan ci gaban da aka samu a shekarun baya. a wasu ƙasashen.

Ms Sánchez-Páramo ta ce "A lokaci guda, talauci na yin kane-kane a ƙasashe da ke cikin hali na rashin tabbas da kuma waɗanda ke cikin rikici, saboda sauran ƙasashen sun yi nasarar ciyar da kansu gaba."

A shekarar 2015, rabin al'ummar da ke fama da fatara na jibge ne a ƙasashe biyar - India, da Najeriya, da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Congo, da Ethiopia, da kuma Bangaladesh.

Amma kiyasi na baya-bayan nan ya nuna cewa ko dai Najeriya ta zarce India ko kuma tana gab da zarce ta a matsayin ƙasar da ta fi kowace yawan mutanen da ke rayuwa cikin ƙangin talauci - dukkaninsu na da kusan mutane miliyan 10 da ke fama da talauci.

Nan da shekara ta 2030, duk da cewar wasu ƙasashen Afirka za su yi koƙari sosai wurin yaƙi da talauci, kusan mutum tara cikin 10 za su rinƙa rayuwa ne kan ƙasa da $1.90 a ƙasashen Afirka.

Wasu labaran masu alaƙa

Kai wa ga masu fama da fatara

Kawar da talauci ɗaya ne daga cikin ƙudurorin tabbatar da ci gaba na Majalisar Ɗinkin Duniya, to amma rahotonta na watan Juli ya yi hasashen cewar kashi 6% na al'ummar duniya za su rinƙa rayuwa ne cikin ƙangin fatara.

Bankin Duniya na da wani shiri na rage masu fama da talauci zuwa ƙasa da kashi 3% na al'umma, to amma idan aka yi la'akari da yadda abubuwa ke tafiya a yanzu, da wuya a cimma wannan ƙuduri.

Mr Ravallion ya ce shirye-shiryen ci gaba da ake da su a yanzu na aiki ne a kan mutane da ke cikin talauci, amma ba ya aiki a kan mutanen da ke cikin baƙin talauci.

Amma ya yi amannar cewa shirin bai yin tasiri kan waɗanda ke cikin matsanancin talauci yadda ya kamata.

Yara kan titi a Manilla

Asalin hoton, Getty Images

Matsalar rashin daidaito

Mr Ravallion ya bayyana cewar an yi taka-tsan-tsan wurin yin amfani da $1.90 a rana a matsayin ma'aunin talauci wajen gwada ci gaban da ake samu a ƙasashe matalauta.

Ya ce "Muna ganin yadda ake samun raguwa a yawan mutanen da ke fama da talauci bisa ga mizanin da aka ayyana (dala 1.90 a rana), amma ana samun ƙaruwar mutanen da ke fama da talauci idan aka yi la'akari da ƙasashensu.

Ya ƙara da cewa "ƙaruwar rashin daidaito shi ne babban ƙalubale da za a fuskanta a nan gaba game da samu nasarar yaki da talauci da ci gaban walwala."

Ms Sánchez-Paramos ta ce daidaito ba ya nufin ta fannin kuɗaden shiga kawai, har ma da daidaito wurin samun dama, ta hanyar bai wa kowa dama, ta yadda duk talaucin mutum zai iya samun aikin yi da kuma zuba jari."

Ta kara da cewa "kuma mun gano cewar rashin samun dama shi ne babban abin da ya fi illa a kokarin da ake yi na yaki da talauci."

*Ƙarin bayani: Fernando Duarte