Abu huɗu da suka sa Faransawa zaɓen jam'iyyar masu ƙyamar baƙi

Marine Le Pen, ɗaya daga cikin jagororin haɗakar jam'iyyu masu tsattsauran ra'ayi na National Rally - RN

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Marine Le Pen, ɗaya daga cikin jagororin haɗakar jam'iyyu masu tsattsauran ra'ayi na National Rally - RN
    • Marubuci, Alexandra Fouché
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Jam'iyyar masu ƙyamar baƙi ta Faransa National Rally (NR) ta samu kashi 33 cikin ɗari na sakamakon zagayen farko na zaɓen ƴan majalisar dokoki da aka gudanar a ƙasar, ranar Lahadi.

Gamayyar jam'iyyu masu sassaucin ra'ayi na New Popular Front (NPF) ce ke biye mata da kashi 28 cikin ɗari na sakamakon, yayin da haɗakar jam'iyyu ta Shugaba Emmanuel Macron ta zo a mataki na uku da kimanin kashi 21 ciki ɗari.

Mista Macron ya yi kira ga jam'iyyu masu sassaucin ra'ayi da masu matsakaicin ra'ayi su haɗa kai domin ganin sun hana masu tsattsauran ra'ayi samun rinjaye a majalisar.

To amma mene ne wasu daga cikin dalilan da suka sanya masu kaɗa ƙuri'a suka karkata goyon bayansu ga jam'iyyar masu ƙyamar baƙin wadda ke ƙarƙashin jagorancin Marine Le Pen da Jordan Bardella?

Shahararren mai sharhi kan lamurran ƙasar Faransa Alain Duhamel ya ce tarihi ya taka muhimmiyar rawa.

1) Harkokin cikin gida da matsalolin tattalin arziƙi

Babban abin da masu kaɗa ƙuri'ar suka yi la'akari da shi ne matsalar tsadar rayuwa, wanda ke ƙara raunana nauyin aljihun mutane, akwai kuma ƙarin farashin makamashi, da na kula da lafiya da kuma fargabar ƙazancewar matsalar tsaro.

Duk da cewa matsalar tattalin arziƙin Faransa ba ta yi muni ba, mutane a yankunan karkara sun shaida wa BBC cewa suna ganin gwamnati ta yi watsi da su, inda gwamnati ta fi mayar da hankali da kuma kashe kuɗi kan birane, yayin da rashin aikin yi a wasu yankuna ya ƙaru zuwa kimanin kashi 25 cikin ɗari.

Wasu mutanen ƙasar ba su da ƙarfin samun muhalli, haka nan a wasu yankunan makarantu sun rufe sanadiyyar tsuke bakin aljihu, kuma wasu na cikin tashin hankali kasancewar wasu asibitoci a yankunan karkara sun rufe inda aka mayar da hankali kan manyan asibitocin da ke cikin birane.

Farfesa Thomas Pickety ya shaida wa BBC cewa mutanen da ke ganin an bar su a baya yanzu sun karkata goyon bayansu ne ga jam'iyyun masu tsattsauran ra'ayi.

Aurélie ta ce ta yi murna a lokacin da Macron ya zama shugaban ƙasa kasancewar ya fito ne daga yankin Amiens - amma yanzu ya ba ta kunya
Bayanan hoto, Aurélie ta ce ta yi murna a lokacin da Macron ya zama shugaban ƙasa kasancewar ya fito ne daga yankin Amiens - amma yanzu ya ba ta kunya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Patrick, wani mazaunin garin Pontault-Combaut a gabashin Paris, ya zaɓi jam'iyyar National Rally a zaɓen Turai, ya shaida wa BBC cewa: "Mutane na neman sauyi, kuma sun zaƙu su kaɗa ƙuri'a.

Ba su jin daɗi musamman idan suna fargaba kan tsaron lafiyarsu yayin da suke tafiya a titunan ƙasar nan."

Ita kuwa Aurelie, mai shekara 37 wadda ke da ɗa mai shekara biyu da haihuwa a garin Amiens, arewacin Faransa, inda Shugaba Macron ya girma ta ce dalilin da ya sa ta zaɓi jam'iyyar NR shi ne saboda tana da fargaba game da rashin tsaro a ƙasar.

Sai kuma wani abu da mutane ke la'akari da shi, shi ne batun fansho bayan da Shugaba Macron ya sanya hannu kan dokar tsawaita shekarun yin ritaya daga 62 zuwa 64.

Mutane da dama sun nuna adawa mai ƙarfi da dokar.

Haka nan ma tashin gwauron zabin da farashin lantarki, da gas wanda mutane ke amfani da su wajen ɗumama gida ya yi ya zamo babban lamari a zaɓen.

Haka nan kuma jagoran jam'iyyar NR, Jordan Bardella ya ce zai mayar da hankali wajen rage harajin sayen kayan masarufi na VAT wanda ake karɓa a ɓangaren makamashi da kuma wasu abubuwan buƙatu guda 100, kuma ya ce zai soke dokar tsawaita shekarun yin ritaya cikin watanni kaɗan.

2) Rashin gamsuwa da gwamnati

Al'umma na ganin cewa tamkar gwamnatin yanzu ta watsar da su, kuma suna ganin cewa ya kamata a ba jam'iyyar NR dama, kasancewar ba ta taɓa kasancewa cikin gwamnati ba, suna ganin hakan zai taimaka.

Jean-Claude Gaillet, mai shekara 64 a duniya, wanda ke zaune a yankin Henin-Beaumont, inda Marine Le-Pen ke da farin jini ya ce: "Na gamsu cewa muna buƙatar sauyi".

"Abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata, muna buƙatar gyara abubuwa."

Wani magoyin bayan jam'iyyar NR mai suna Marguerite ta ce jam'iyyar ta samu nasara ne kasancewar "mutane sun gaji da halin da ake ciki". Yanzu mutane na ganin ba su damu ba za su yi zaɓen "duk abin da zai faru, ya faru".

Sai dai wata da ke zama a garin Oignies, Yamina Addou ta ce ta ji mamakin nasarar da jam'iyyar NR ta samu.

Ta ce an yaudari masu zaɓe, inda suka kaɗa wa jam'iyyar NR mai tsattsauran ra'ayi ƙuri'a, kuma wannan al'amarin zai iya janyo rarrabuwar kawuna tsakanin al'ummar Faransa.

Mutane da dama na ɗora laifin halin da ƙasar ta fada a ciki kan shugaban ƙasar Emmanuel Macron.

Mutane da dama na ganin cewa Shugaba Macron ne ya jefa Faransa cikin ruɗanin siyasa da take ciki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane da dama na ganin cewa Shugaba Macron ne ya jefa Faransa cikin ruɗanin siyasa da take ciki

3) Magance matsalar baƙi

A tsawon shekaru, jam'iyyar Marine Le Pen ta NR ta yi fafutukar ganin ta samu shiga a wajen talakawan Faransa.

Jam'iyyar ta kasance mai bin ra'ayin talakawa, wadda babban abin da ta mayar da hankali a kai shi ne kare muradun asalin ƴan ƙasa da kuma adawa da shigar baƙi ƙasar.

Shugaban jam'iyyar, Jordan Bardella ya ce yana son haramta wa ƴan ƙasar masu takardun zama a wata ƙasar daga riƙe wasu muƙamai masu muhimmanci, inda ya bayyana irin waɗannan mutane a matsayin waɗanda "ba cikakkun Faransawa ba".

Yana kuma son taƙaita shirye-shiryen kula da al'umma da ƴan ci-rani ke cin gajiya tare kuma da soke bai wa yaran da aka haifa a Faransa - waɗanda iyayensu ba haifaffun Faransa ba ne - takardar zama ƴan ƙasar kai-tsaye.

Sai dai ya bayyana cewa babu batun haramcin yafa mayafi a ajandarsu ta nan kusa.

Jam'iyyar na bin masu ra'ayin cewa ƴan ci-rani, musamman Musulmai, ba lallai ne su saje da al'umma da al'adun ƙasar ta Faransa ba.

Misali, ɗaya daga cikin ƴan takaran jam'iyyun masu tsattsauran ra'ayi ta shaida wa BBC cewa, jam'iyyar za ta ɗauki mataki kan baƙi waɗanda ke fifita dokokin addinansu kan dokokin ƙasar.

Jandarmomin Faransa a kan doki na dakon Musulmai da ke fitowa daga masallacin birnin Paris bayan kammala sallar idi a ranar 16 ga watan Yuni 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mai sharhi ya ce ra'ayin mutane da dama a Faransa ya karkata kan ƙyamar baƙi a cikin shekara 10 da suka gabata

4) Yaɗa manufa ta shafukan sada zumunta

Shugaban jam'iyyar NR, Jordan Bardella sananne ne wajen yaɗa manufa a shafin Tiktok

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban jam'iyyar NR, Jordan Bardella sananne ne wajen yaɗa manufa a shafin Tiktok

Jam'iyyar NR ta yi kamfe kan abubuwa biyu, fargabar al'ummar ƙasar na zagwanyewar al'adunsu da kuma da kuma tsadar rayuwa.

Sun yi amfani da shafukan sada zumunta wajen yada manufofinsu har ta kai ga masu kada kuri’a suka amince da su.

Vincent LeBrou na jami’ar Université de Franche-Comté da ke Faransa ya bayyana wa BBC cewa “a Faransa ana yi wa Jordan Bardella take da ɗan siyasan TikTok kasancewar shi ɗan siyasa ne wanda yake jin daɗin yaɗa manufa a shafin na TikTok”.

“Yana cikin abubuwan da ya ƙara masa farin jini”.

Charles Culioli, wani ɗan takara a jam’iyyar mai sassaucin ra’ayi ta NPF, wanda ke adawa da jam’iyyar NR, ya ce “Mutane da dama ba masu nuna wariyar launin fata ba ne, kawai dai sun gaji ne da tsarin tafiyar da mulki irin na Macron, sun gaji da duk irin alƙawurran da aka yi musu.”