Fari a Zimbabwe: Yadda ake tona ramuka a cikin kogi don neman ruwa

- Marubuci, Shingai Nyoka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kurima village
- Lokacin karatu: Minti 5
Yankin kudancin Afirka na fukantar ɗaya daga cikin fari mafi mufi a tarhin duniya, inda fiye da mutum miliyan 70 ke rayuwa ba tare da wadataccen abinci ko ruwan sha ba.
A gundumar Mudzi da ke arewacin Zimbabwe, jama'a ne da dabbobinsu ke taruwa a wani kogi da ya ƙafe domin tonon ƙananan ramuka da nufin samun ruwan sha.
Kogin na Vombozi kan riƙe ruwa a kowane yanayin shekara, to amma a halin yanzu rairayi ne ya cika kogin iya ganin idonka.
Mutanen yankin kan riƙe shebur da bokitai, inda suke tonon tsakiyar kogin, cike da fatan samun ruwan da za su jiƙa maƙoshinsu.
Koguna da madsatsun ruwa sun ƙafe a wasu yankunan gundumar, sakamakon hakan ne mutanen yankin ke tururuwa zuwa ƙauyen Kurima da nufin tono don samun ruwa.
Tsakiyar kogin cike yake da ƙananan ramukan ruwan jira da mutane suka tona.
Idan ruwan ya taru mutanen kan yi amfani da su ta hanyoyi daban-daban, ƙanannan yara kan yi wanka, mata su wanke tufafinsu, yayin da manya ke bai wa dabbobi ruwa.
Gracious Phiri, mahaifiyar yara biyar, na daga cikin matan da ke wanki a wannan ƙafaffen kogi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Matar mai shekara 43 ta shaida wa BBC cewa a yanzu takan yi tafiya mai tsawo fiye da yadda ta saba domin ɗebo ruwa.
Ms Phiri ta zura ƙaramin bokitinsa cikin ƙaramin ramin da ta tona domin ɗebo ruwan mai launin ruwan ƙasa bayan ya taru.
Tana cikin fargabar yiwuwar yaranta su kamu da cuta.
“Kamar yadda kuke gani, ga dabbobi nan na ta shan ruwa daga inda muke diba domin amfanin kanmu. Fitsarinsu kan iya shiga cikin ramukan, wanda kuma hakan na da matsala ga lafiyarmu,'' in ji ta.
"Ban taɓa ganin abu irin wannan ba."
An samu raguwar shigar da abinci a Zimbabwe , inda mutum miliyan 7.7 ke fuskantar barazanar yunwa.
A gundumar Mudzi yawan iyalan da ke samun wadataccen abinci mai gina jiki ya ragu da fiye da rabi idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kamar yadda hukumomin lafiyar ƙasar suka bayyana.
Lamarin ya shafi ƙananan yara da dama - Inda aka samu ninkuwar ƙananan yaran da ake kwantarwa a sibitocin yankin tun cikin watan Jarairu.
Mutanen ƙauyen sun ɓullo da shirin ciyarwar bai ɗaya domin magance matsalar. A kowane mako matan yankin kan taru a wani wuri, inda suke zuwa da abin da suke da shi, domin dama wani nau'in fate, mai cike da sinadaran gina jiki, don shirin ciyarwar ga yara 'yan ƙasa da shekarar biyar.
Gyaɗa da wake da ƙuli-ƙuli da na'in ganyayyaki, na daga cikin abubuwan da ake dafa faten da shi, domin ƙara masa sinadarai.
Gwamnatin ƙasar tare da haɗin gwiwwar cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya irin su Unicef sun fara tallafa wa al'ummar ƙauyen kan shirin ciyarwar, inda daga baya ake ciyarwar aƙalla sau uku a kowane mako.
“Amma yanzu saboda farin El Niño, sau ɗaya kawai ake ciyarwar a mako," in ji Kudzai Madamombe, jami'in lafiya na gundumar Mudzi.
"Sakamakon rashin ruwan sama, mun fuskanci asara amfanin gonarmu da kashi 100'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa shirin na fuskantar barazanar dakatarwa a wata mai zuwa sakamakon ƙarancin abincin a yankin.
Asibitocin yankin da ke taimaka wa mutane sun fuskanci koma-baya, hatta tuƙa-tuƙan da ke samar wa asibitocin ruwa sun ƙafe, in ji Mista Madamombe.
Kuma ruwan da ya rage a babbar madatsar ruwan gundumar bai fi na amfanin wata guda ba.
Sakamakon haka, an dakatar da shirye-shiryen noman rani, ciki har da wanda ke tallafa wa manoman yankin fiye da 200.
Matsalar ta shafi ko'ina. Tambudzai Mahachi, mai shekara 36 ta ce ta shuka masara da waken suya da farin wake a gonarta.
Amma duk da wahalar da ta yi a gonar, babu abin da ta samu, hatta bishiyar kukar da ke gonarta ba ta yi ko ɗa guda ba.

Ms Mahachi ta ce, a duk lokacin da shekara ta yi kyau, takan yi safarar abinci zuwa kasuwannin Harare, babban birnin ƙasar, amma yanzu tana cikin miliyoyin 'yan ƙasar da ke hannu baka hanu ƙwarya.
A yayin da ƙauyen ke haɗa hannu don ciyar da yara sau guda a kowane mako, 'ya'yanta na buƙatar samun abinci a kowacce rana.
Mun tarar da ita a gidanta, ta girka wa 'ya'yan nata tsabar alƙama domin su yi karin kumallo. Wata ƙungiyar agaji ce dai ta samar musu da alƙamar.
“Mun daina cin abin da muke so, kuma mun koma taƙaita abincin da za mu ci,” in ji Ms Mahachi.
“Ita babbar ta ɗan fara fahimtar halin da ake ciki, inda take haƙura da kowane irin fate, amma ƙaramar sai ta yi ta kuka, idan na bata abin da ba ta so.”
An samu tsaikon ruwan sama a ƙasashen yankin kudancin Afirka, yankin da mafi yawa aka dogara da ruwan sama wajen noma, maimakon noman rani.
Matsalar fari ta tilasta wa kashi ɗaya bisa uku na ƙasashen yankin kudancin Afirka ayyana dokar taɓaci kan matsalar. Kusan mutum miliyan 68 ne ke buƙatar tallafin abinci a yankin.

Ƙungiyar ci gaban ƙasashen yankin kudancin Afirka ta (SADC), ta yi kiran buƙatar tallafin dala biliyan 5.5 a watan Mayu, domin yaƙi da matsalar fari, kuma kawo yanzu tallafin da suka samu bai taka kara ya karya ba.
“Idan ka je ko'ina a kudancin Afirka, rumbuna hatsi da dama sun yi fayau, kum masara - wadda ita ce nau'in abinci mai ƙara kuzari da mutanen yankin suka fi amfani da shi - ta yi tsada ta yadda mutane ba za su iya saya ba," kamar yadda Tomson Phiri, kakakin shirin samar da Abinci na MDD, WFP da ke kula da shiyyar kudancin Afirka ya shaida wa BBC.
"Yanayin zai ci gaba da munana a nan gaba."
Shirin Samar da Abinci na MDD, WFP ta samu kashi daya cikin biyar na dala miliyan 400, da ake buƙata don tallafin gaggawa, yana mai cewa kudancin Afirka na fama da raguwar masra mafi muni cikin shekara 15.
Kuma har yanzu ba a kai tsakiyar whalar abinci da ruwan sha a yanzin ba - Watan oktoba shi ne mafi zafi kuma mafi bushewa a shekara.
Idan har aka samu saukar ruwan sama a watan Nuwamba ko Disamba, wanda shi ne lokacin saukar damina a yankin, dole ne manoma su jira har zuwa watan Maris domin girbin masara.











