Mece ce sabuwar cutar Langya da aka gano a China?

Asalin hoton, Getty Images
Wata tawagar ƙwararru kan kimiyya sun sanar da ɓullar wata ƙwayar cuta dangin Henipavirus, wani rukuni da ke haddasa annobar cutuka masu saurin kisa a tsakanin mutane.
A cewar tawagar binciken, ƙayar cutar Langya henipavirus (LayV) ta harbi mutum 35 a China daga 2018 zuwa 2021.
Wani rahoto da Mujallar New England ta wallafa a ranar 4 ga watan Agusta ya ce ƙwararru sun bayyana cewa babu alamun mutane sun yaɗa cutar LayV a tsakaninsu.
Suka ƙara da cewa akwai yiwuwar tana yaɗuwa ne daga dabbobi. Tawagar ta ce akwai hujjar da ke nuna jaɓa ce ke ta fi yaɗa Langya, amma dai har yanzu akwai buƙatar tabbatar da wannan bincike da ƙarin wasu binciken.
An iya nazartar mutum 26 sosai cikin 35 da suka harbu da cutar, ind aka gano cewa dukkansu na fama da zazzaɓi, a wasu lokutan kuma da gajiya (kashi 54 cikin 100), da atishawa (kashi 50), da ciwon kai (kashi 35), da amai (kashi 35).
Haka nan, an gano yadda zuciya ke aiki ba bisa tsari ba (a cikin kashi 35 cikin 100 na marasa lafiyar) da ƙoda (kashi 8). Sai dai babu bayani game da mutuwa.
Ƙwararrun da BBC ta tattauna da su sun ce hakan ba ya nufin lallai wata annoba na shirin ɓarkewa a duniya, amma gano cuta a irin wannan rukunin na Henipavirus abu ne mai haifar da damuwa saboda sauran 'yan uwanta sun haddasa annoba iri-iri a yankunan Asiya da Oceania.
'Cutar ba ta da ƙarfi a yanzu'
Waɗannan annoba-annoba "dangin" LayV ne da ake kira Hendra henipavirus (HeV) da Nipah henipavirus (NiV).
Ba a fiya harbuwa da Hendra ba amma fa yawan kisan da take yi ya kai kashi 57 cikin 100, a cewar hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Amurka (CDC).
Ita kuwa Nipah, cikin annoba-annoba da aka ruwaito daga 1998 zuwa 2018 ƙiyasin waɗanda suka mutu sun kama daga kashi 40 zuwa 70 cikin 100. Dukkan ƙwayoyin na haddasa matsalolin numfashi da na ƙwaƙwalwa.
Ƙasar Indiya na cikin waɗanda suka yi fama da annobar Nipah a 2018, inda ta kashe mutum 17 daga cikin 19 da aka tabbatar a Jihar Kerala.

Asalin hoton, Getty Images
Abu ne mai wuya a iya kwatanta yadda waɗannan cutuka ke kashe mutane ba da kuma korona saboda bayanan da ƙasashe suka fitar da kuma lokutan da suka fitar da shi.
Jansen de Araujo, wani farfesa a sashen binciken sabbin ƙwayoyin cuta a Jami'ar Sao Paulo, yana ganin gano cutar Langya ba ya nufin wata annoba na shirin ɓarkewa a duniya ganin yadda ƙwararru suka shafe lokaci suna bin diddigin cutar.
"Abin da aka lura da shi shi ne babu wani yanki da za a ce shi ne cibiyar cutar kamar yadda aka samu lokacin korona," a a cewar Farfesa Araujo.
Ian Jones, farfesan binciken cutuka a Jami'ar Reading da ke Birtaniya, ya ce Langya ba ta nuna wasu alamun za ta iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum ba.
'Babu alamun rikiɗewar cutar'
"Abu mafi muhimmanci, daga Hendra har Nipah babuw wadda ta nuna alamun zama annoba," kamar yadda ya faɗa wa BBC.
"Babu alamu ƙarara da ke nuna suna iya rikiɗewa zuwa wasu nau'ukan duk da cewa za su yi tunanin ita ma Langya haka take," a cewar Farfesa Jones.
Duk da haka, masanan biyu sun yi amanna cewa hakan wajibi ne don a dinga sa ido kan yaɗuwar Langya.

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar da ta gano Langya ta ce dukkan waɗanda suka kamu da cutar 'yan yankunan Shandong ne da Henan na China. Dukkansu ba su taɓa haɗuwa da juna ba kuma ba su taɓa bi ta wani wuri ɗaya ba.
Akasarin masu cutar manoma ne, abin da ya sa ba a yi mamaki ba saboda da ma cutar na yaɗuwa ne a cikin mutane ta hanyar mu'amala da dabbobi.
Da suke neman asalin cutar Langya a jikin dabbobin gida da na daji, ƙwararru sun gano cewa jaɓa na da kashi mafi yawa na samun cutar - fiye da kashi 25 cikin 100 na ɓerayen da aka nazarta na ɗauke da ƙwayar cutar.
Jemagu matattarar cuta

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An san jemagu da zama matattarar ƙwayoyin Hendra da Nipah. A cewar CDC, har yanzu ba a san inda wani mutum ya harba wa wani mutum ƙwayar Hendra ba, wadda ake iya ɗauka daga ruwan jikin jiki kamar ko kashi ko kuma dawakai da ke ɗauke da cutar.
A gefe guda kuma, ƙwayar Nipah, a cewar CDC, an san ta da yaɗuwa idan mutane suka taɓa dabbobin da ke da cutar ko kuma ruwan da ke fita daga jikinsu, ko kuma yin mu'ala ta kusa sosai da mutumin da ke da NiV.
Sai dai Farfesa Jones ya yi imanin cewa babu wani dalilin da zai sa a tayar da hankali.
"A tunanina, Nipah ba ta da wata barazanar haddasa annoba. Ƙwayar cutar na nuni da wasu ƙalubale ga ɗan Adam, amma za a iya kare kai daga su ta hanyar iliminatarwa, sama da a ce an ƙirƙiri riga-kafi," in ji shi.
Masanin ya kuma ce cutar ta fi ratsa sassan ɓargon mutum, abin da ya sa mutum ba ya iya yaɗa wa mutum, ba kamar korona ba wadda ke ratsa hanyoyin numfashi.
"Abu mafi muhimmnanci shi ne kada a firgita idan an ga wata sabuwar ƙwayar cuta. A kullum ƙwararru na bin sawun ƙwayoyin cuta kuma hakan ya ƙaru bayan afkuwar annobar korona," kamar yadda Farfesa Jones ya ce.
"Akwai ƙwayoyin cutuka mafiya haɗari amma hakan ba ya nufin za mu kamu da su."











