'Yadda na ga jikin Rebecca ƴar wasan tsere na ci da wuta'

Agnes Barabara a zaune kusa da wata bishiya a gidanta da ke Kenya
Bayanan hoto, Agnes Barabara ta ce ta yi ƙoƙarin taimakawa maƙwabciyarta, Rebecca Cheptegei
    • Marubuci, Celestine Karoney
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
    • Aiko rahoto daga, Kitale
  • Lokacin karatu: Minti 4

Warning: Wannan maƙalar na ƙumshe da bayanan da za su iya sosa zukatan wasu masu karatu

An jera furanni a kan ƙonanniyar ciyawar ƙofar gidan da Rebecca Cheptegei ke zaune, inda ƴar wasan tseren ta riƙa juyi domin kashe wutar da ke ci a jikinta.

Ƴar wasan tseren gasar Olympics ɗin mai shekara 33 ta mutu a ranar Alhamis ne saboda ciwon da ta samu, wanda ake zargin tsohon saurayinta ne ya watsa mata fetur, ya kuma cinna mata wuta, lokacin da take zaune gida tare da ƴaƴanta mata biyu.

Cikin hawaye, Agnes Barabara, maƙwabciyar Ms Cheptegei ta shaidawa BBC cewa: “Ina cikin gida kawai sai na ji mutane suna ihu, 'wuta'. Lokacin da na fito sai na ga Rebecca to doshi gidana a guje, ga wuta na ci a jikin ta, tana ihun 'a taimake ni''

“Lokacin da tafi domin nemo ruwa kuma ina ihun neman ɗauki, sai kuma wanda ya kashe ta ya biyo ta, yana ƙara watsa mata fetur har shima wutar ta kama jikinsa sannan ya gudu cikin lambu domin neman yadda zia kashe wutar da ta kama shi. Mu kuma sai muka garzaya domin taimakawa Rebecca.

Ms Barabara ta ce bata taɓa ganin an ƙona mutum da ransa ba sai a wannan karon. Kuma ta shafe kwanaki bata ko iya cin abinci.

“Maƙwanciyar arziki ce, ko kwanannan sai da ta yi mani kyautar masarar da ta noma.”

Ƴan sanda sun ce mutuwar ta kisan kai ce, kuma sun bayyana sunan tsohon saurayin nata a matsayin wanda ake zargi da aikata laifin.

Hukumomi a yankin sun ce mutanen biyu suna rikici ne a kan wani fili da Ms Cheptegei ke zaune, kuma ba a kai ga yanke hukunci a kan jayayyar tasu ba.

Za a gurfanar dashi gaban ƙuliya idan ya murmure daga jinyar ciwon da ya samu a lokacin da abin ya faru.

“Mun yi nisa da bincike a kan lamarin,” Inji jami'in binciken manyan laifuka na ƴan sandan yankin, Kennedy Apindi.

Mahifiyar Rebecca, Agnes Cheptegei tana zaune a ƙofar gida
Bayanan hoto, Mahifiyar Rebecca, Agnes Cheptegei tana tuna ɗiyarta
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mahaifiyar Ms Cheptegei, Agnes ta ce ɗiyarta "ta kasance ɗiyar ƙwarai mai biyayya da raha, a iya rayuwarta".

Emmanual Kimutai, wani aboki kuma maƙwabcin Ms Cheptegei wanda suka halarci makaranta ɗaya ya bayyana ta a matsayin "mai kirki da raha" kuma "mai mayar da hankali ga abin da ta sanya a gaba".

“Ko a firamari, ta kasance ƴar wasan tsere da ta yi fice, ita ce gwarzuwar mu," inji Mr Kimutai.

An haifi ƴar wasan Olympics ɗin a Kenya, a kusa da kan iyakar Uganda domin haka da ta gaza shiga tawagar Kenya sai ta tsallake ta wakilci Uganda, a gasar wasannin motsa jiki.

Bayan ta fara wasanni motsa jiki kuma sai ta shiga cikin dakarun tsaro na Uganda People’s Defence Forces a 2008, kuma har ta kai matsayin sergeant.

Daga cikin wasannin da ta yi harda na gasar Olympics ta bana, a birnin Paris inda ta zo matsayi na 44 a tseren marathon, kuma duk da haka mutanen yankin su suna kiran ta a matsayin ''gwarzuwa''

Ta yi rayuwa a Chepkum, wani ƙauye a cikin Kenya mai nisan kilomita 25 daga kan iyakar ƙasar da Uganda, ƙauyne da ya dogara ga noma a matsayin hanyar bunƙasar tattalin arzikin jama'ar.

Yankin da ake kira Trans-Nzoia county, ya yi fice a matsayin yankin da ya fi kowanne samar da masara, wadda jama'a da dama na amfani da ita a matsayin abinci a ƙasar.

Mutanen da ke kasuwanci a wani rukunin shaguna kusa da gidan ta sun riƙa yabon ta, suna tuna yadda take wuce su lokacin da take gudu.

Wasu mutane sun taru suna kuka da jera furanni a kusa da hoton Rebecca Cheptegei
Bayanan hoto, Jama'a na jimamin mutuwar ƴar wasan tseren a gidanta

Yayin da ake alfahari da ita a matsayin ƴar wasan motsa jiki, a gefe guda kuma rayuwar ta tana cikin damuwa. Tsohon ɗan ajin su ya ce rashin taka rawar ganin da ta yi a gasar Olympics tana da alaƙa da rashin zaman lafiya tsakaninta da tsohon saurayinta, rikicin da aka fara a bara.

“A baya suna zama tare ne a gida ɗaya, amma a bara sai suka fara samun matsala saboda kuɗi," inji ɗan uwanta, Jacob. "Ya tambayi ƴar uwata: me kike yi da duk kudin da kike samu?"

Ƴan sanda sun shaidawa BBC cewa a baya ma masoyan biyu sun kai ƙarar juna kan rikicin tsakanin su, a ofisoshin ƴan sanda daban-daban, amma kuma duk sun janye ƙarar tasu da kansu.

Yayin da iyalan Ms Cheptegei ke jiran a yi masu adalci, suna ci gaba da shirin jana'izar ta. Za a yi mata jana'iza a ranar 14 ga watan Satumba, a ƙauyen iyayen ta da ke Bukwo, a Uganda.

Itace ƴar wasan motsa jiki ta uku da aka kashe a Kenya cikin shekara uku da ta gabata, kuma ƴan sanda na zargi masoyan su da hannu a kisan. Ƙungiyar ƴan wasan motsa jiki ta Tirop’s Angels ta ce dole a kawo ƙarshen wannan mummunan yanayi.

“Abin takaicin shi ne yadda ƴaƴanta na kallo aka aikata abin da aka yiwa mahaifiyar tasu," inji Joan Chelimo, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar Tirop’s Angels.