Ɗan sanda 'ya kashe' abokin aikinsa da almakashi a Kebbi

Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi a Najeriya ta ce tana ci gaba da bincike kan mutuwar wani jami'inta, ASP Shu'aibu Sani Malumfashi, bayan faɗa da takwaransa mai muƙamin ASP.

Rundunar ta ce, a ranar 19 ga watan Oktoban 2022, ne da rana jami’anta biyu da ke aiki a ofishinsu da ke Argungu, wato ASP Abdullahi Garba, da kuma ASP Shu’aibu Sani Malumfashi, suka samu saɓani kuma a dalilin haka ne suka kaure da faɗa.

Rundunar, ta bakin jami’in hulɗa da jama’a SP Nafi’u Abubakar, ta shaida wa BBC cewa, bayan ‘yan sandan sun kaure da faɗa ne sai ASP Abdullahi Garba, ya yi amfani da almakashi ya soki abokin aikin nasa a haƙarƙari.

SP Nafi’u Abubakar, ya ce bayan soka masa almakashin ne sai ya yanke jiki ya faɗi a ƙasa, a nan ne DPO ya bayar da umurnin garzayawa da jami'in zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

ASai dai a tattaunawarsa da BBC, Sani Shua’aibu Malumfashi, mazaunin garin Kaduna, wanda shi ne mahaifin marigayin ya ce “an caka masa wuƙa a zuciyarsa, an caka masa wuƙa a gefen haƙoransa, sannan kuma aka murɗe masa wuya har sai da wuyan ya karye.”

Ya ƙara da cewa sun gano hakan ne a lokacin da suke yi wa gawar mamacin wanka kafin bizine shi.

Ya kuma buƙaci hukumomi da su bi kadin abin da ya faru “muna son a bi mana haƙƙinmu, idan aka bi haƙƙinmu ba zai dawo da marigayi Shua’aibu ba, amma zai iya hana afkuwar ɗan sanda ya kashe ɗan uwansa ɗan sanda.”

A ci gaban tattaunawarsa da BBC, SP Nafi’u Abubakar, ya ce bayan afkuwar wannan lamari a yanzu an kai wannan batu zuwa babban ofishin binciken manyan laifuka da ke Birnin Kebbi wato CID, domin a gudanar da bincike a kan ainihin abin da ya faru a tsakanin jami’an nasu da har suka kaure da faɗa aka kuma samu asarar rai.

Ya ce,” Wanda ake zargin wato ASP Abdullahi Garba, na nan a tsare a yanzu haka har sai an kammala bincike kafin daga bisani kuma a kai shi kotu.”

Jami’in hulɗa da jama’ar ya ce, sakamakon afkuwar wanann iftla’i a yanzu kwamshinan ‘yan sandan jihar ta Kebbi ya gargaɗi jami’an ‘yan sandan da ke aiki a jihar da su zauna lafiya da junansu.

Sannan kuma na shawarce su da idan har wani daga cikin su ya yi wa wani ba daidai ba, to akwai in da za su iya kai ƙara a cikin ofisoshinsu, ba sai sun ɗauki doka da hannunsu ba.