Messi zai je Gasar Cin Kofin Duniya karo na biyar a tarihi

Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi zai ja ragamar tawagar Argentina a Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Qatar, kuma karo na biyar a jere da zai walici kasar.
Mai taka leda a Paris St Germain wanda shi ne kyaftin din tawagar, yana cikin jerin 'yan wasa da na Premier League biyar da za su wakilci Argentina.
Kociya, Lionel Scaloni ya hada 'yan wasan da ke da kwarewa kamar Messi mai shekara 35 da Angel di Maria mai shekara 34 da matasa, ciki har da mai taka leda a Manchester Ciyy, Julian Alvarez.
Messi wanda ya fara buga Gasar Cin Kofin Duniya a Jamus a 2006 ya je ta Afirka ta Kudu a 2010 ya kuma halarci ta Brazil a 2014 da wadda aka yi a Rasha a 2018.
Cikin wadanda Argentina ta bayyana har da Paulo Dybala, mai shekara 28, wanda ke jinya, wanda rabon ya taka leda tun ranar 9 ga watan Oktoba.
Argentina za ta fara wasan farko a rukuni na uku da Saudi Arabia ranar 22 ga watan Nuwambar, sannan ta fuskanci Poland ta kuma kara da Mexico.
Argentina wadda ta lashe Copa America a barra ta buga wasa 35 tun daga lokacin a jere ba a doke ta ba kawo yanzu.
Kofin duniya da ta dauka na karshe shi ne a 1986 a Mexico, sannan ta yi ta biyu a gasar 1990 a Italiya da wadda aka yi a Brazil a 2014.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Za a buga gasar cin kofin duniya a Qatar tsakanin 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.
Tawagar Argentina da za ta je buga Kofin Duniya:
Masu tsaron raga: Emiliano Martinez (Aston Villa), Franco Armani (River Plate) and Geronimo Rulli (Villarreal)
Masu tsaro baya: Gonzalo Montiel (Sevilla), Nahuel Molina (Atletico Madrid), German Pezzella (Real Betis), Cristian Romero (Tottenham Hotspur), Nicolas Otamendi (Benfica), Lisandro Martinez (Manchester United), Juan Foyth (Villarreal), Nicolas Tagliafico (Olympique Lyonnais), Marcos Acuna (Sevilla)
Masu buga tsakiya: Leandro Paredes (Juventus), Guido Rodriguez (Real Betis), Enzo Fernandez (Benfica), Rodrigo De Paul (Atletico Madrid), Exequiel Palacios (Bayer Leverkusen), Alejandro Gomez (Sevilla), Alexis Mac Allister (Brighton & Hove Albion)
Masu cin kwallaye Paulo Dybala (AS Roma), Lionel Messi (Paris St Germain), Angel Di Maria (Juventus), Nicolas Gonzalez (Fiorentina), Joaquin Correa (Inter Milan), Lautaro Martinez (Inter Milan), Julian Alvarez (Manchester City).











