Birnin Johannesburg na fama da tarin lalatattun gidaje yayin da ake shirin taron G20

Hoton Sinqhiwe Goodman Sithole wanda ke rayuwa ba ruwan famfo da wutar lantarki a wani tsohon lalataccen gida a Johannesburg
Bayanan hoto, Sinqhiwe Goodman Sithole na rayuwa ba ruwan famfo da lantarki a wani tsoho kuma lalataccen gida a Johannesburg
    • Marubuci, Ayanda Charlie & Hollie Cole
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye
  • Lokacin karatu: Minti 7

Cikin ƙasa da mako biyu, shugabanni daga wasu daga cikin manyan ƙasashen da suka fi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya za su haɗu a babbar cibiyar tattalin arziƙi ta Afirka ta Kudu wato, Johannesburg, domin taron ƙungiyar manyan ƙasashe masu arziƙi G20.

To amma 'yar tazara kaɗan daga inda za a yi wannan taron ƙoli na shugabanni, wurin da aka tanadi tsaro na gaske da kuma ƙawata shi - a tsakiyar birnin akwai wasu wurare da suka zama matattara ta miyagu da ɓata-gari da kuma ƙazanta, inda hukumomi ke faman ganin sun inganta tare da tabbatar da tsaro.

Hukumomin na fuskantar babban ƙalubale na tsaftace lalatattun gidajen da ke wurin sama da 100, waɗanda suke kamar kangwaye, inda yawancinsu ke cike da shara da bahaya a fili, wasu ma kuma gungun miyagu da ɓata-gari ne ke zaune a cikinsu.

"Bindigogi, ga miyagun ƙwayoyi, ga karuwai, kusan komai ga shi a nan," in ji Nelson Khetani, wani mazauni ɗaya daga cikin gidajen da ake kira MBV1, da ke Joubert Park.

Rashin kula da rashin gyara sun sa an sace kusan dukkanin kayan gidajen, kuma ga bayana na gudana a bangaren da ake wani na gidajen .

Mr Khetani ya gaya wa sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Afirka, cewa ɓata-gari sun mamaye gidajen na MBV1, inda suke karɓar kuɗin haya, a wani lokacin ma hakan ya zama wata hanya ta bayar da damar aikata miyagun ayyuka.

BBC ta gano tare da tabbatar da cewa akwai irin waɗannan gidaje tsofaffi da aka yi watsi da su har 102 a tsakiyar birnin na Johannesburg, a wani yanki da ya kai faɗin murabba'in kilomita 18, to amma wasu kafafen ƴada labarai na cewa yawan gidajen ya fi haka, kuma ba su dace da rayuwar mutane ba.

Yadda shara da kashin mutane suka mamaye matattakalar yawancin gidajen
Bayanan hoto, Yadda shara da kashin mutane suka mamaye matattakalar yawancin gidajen

Halin da birnin ke ciki ya ɗauki hankalin Shugaba Cyril Ramaphosa, a lokacin da yake magana da hukumar birnin a watan Maris, kan taron ƙolin na G20 a watan Maris.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Na ga birnin na cikin ƙazanta," in ji shi.

"Abin baƙin ciki ne ka bi tsakiyar birnin… ga tarin gidaje nan da aka yi watsi da su, gidajen da aka mamaye, waɗanda ba sa biyan kuɗin hayarku da haraji."

Kamar yadda shugaban birnin na Johannesburg Dada Morero ya faɗa a lokacin da birnin ya shirya karɓar baƙuncin taron na G20".

A watan da ya wuce, cikin tsare-tsaren tsaftace birnin na Johannesburg, hukumar birnin ta ce za ta mayar da hankali kan tsakiyar birnin wajen kawar da miyagun ayyuka da rashin bin doka da oda da mamaye gidaje ta haramtacciyar hanya da sauran miyagun abubuwa na saba doka".

To amma ƙalubalen da ke gaban babban taron ƙolin na duniya yana da yawa.

Wata gobara da ta tashi a ɗaya daga cikin tsofaffin gidajen da ta kashe mutum 76 shekara biyu da ta wuce, ta ce a ce ta zaburad da hukuma ta tashi tsaye, to amma lamarin bai sauya wani abu ba sosai.

BBC ta ziyarci wani ginin na tsakiyar birnin, wanda ake kira, Vannin Court, inda za a ga dakuna cike da kazanta da shara. Ginin sai warin kashi kawai yake fitowa daga cikinsa da ka doshi wajen.

Wani mazaunin gidan, Sinethemba Maqoma ya gaya wa BBC cewa ginin mallakar hukumar birnin ya fada hannun wasu, kuma a kan haka hukuma ta yanke ruwan fanfonsa.

"Hukumar birnin ta damu a kan miyagun abubuwan da ake aikatawa a ginin ... shi ya sa hukuma ta yanke ruwan," in ji wani mazaunin gidan, Sinqhiwe Goodman Sithole.

Hoton wata tukunyar gas da robar ruwa da sauran kayayyakin gida
Bayanan hoto, Saboda rashin wutar lantarki da gas a gidajen, mazaunan wurin na amfani da gas na tafi-da-gidanka don girki

Hukumar birnin na Johannesburg ba ta amsa buƙatar BBC ta bayar da bayani kan katse ruwan famfo na gidajen na Vannin Court ba.

Babu wutar lantarki in ji, Mr Maqoma, inda ya ƙara da cewa suna amfani da gas ne da wutar sola (mai amfani da hasken rana).

Yanke ruwan famfo da wutar lantarki da gas da hukuma ta yi a gidajen ya sa dole mazauna wajen su y amfani da gas na tafi-da-gidanka, wajen girki.

To amma rashin ruwa ko abubuwan kashe gobara a kusa, hakan na tattare da haɗarin babbar gobara.

Ruwan kashi ya mamaye wajen da wasu tsofaffin motoci suke a ƙarƙashin gidajen.

Mr Maqoma ya nuna wa BBC wani banɗaki mai duhu, mai ƙazanta, da ya ce yana zuba ruwan bokiti ya kora bahaya.

"Idan ka kora ruwan yana kwaranyawa ya je can ƙasan ginin, nda yake kwanciya'' in ji shi.

Hoton shara a wani ɗaki a Vannin Court.
Bayanan hoto, Yawancin ɗakunan gidajen Vannin Court, a lalace suke

Matsalar gidaje ta birnin ba wai yanzu ta fara ba.

Tun bayan da aka kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata na tsiraru a 1994, baƙaƙen fata da barbarar yanyawa sun yi ƙaura daga garuruwa na waje inda suka koma zuwa cikin birnin kusa da wuraren aikinsu.

Wannan gagarumar ƙaura ta jama'a ta haifar da matsalar samar da isassun gidaje.

Rashin gina sababbin gidaje da kuma ƙaurar yawancin attajirai masu gidajen haya, wannan ya sa aka yi watsi da gidaje da dama, hakan kuma ya sa wasu suka zama matattara ta ɓata-gari da aikata miyagun abubuwa.

Wani mutum da muka sauya sunansa da Joseph,(domin tsaro) ya yi wa BBC bayani bisa sharaɗin ɓoye sunansa, ya ce shi a da yana daga cikin 'yan kama-wuri-zauna a gidajen.

Ya ce, wasu ɓata-gari ne na wajen suka ɗauke shi haya, don ya riƙa shara da tsaftace ginin, sannan ya riƙa kafa takardu na tallata hayar gidajen cewa na haya ne.

''To amma ba ainahin abin da suka ɗauke ni na yi ba kenan,'' in ji shi.

"Babban abin da nake musu shi ne dafa miyagun ƙwayoyi da ake kira Nyaope'' ya ce. "Wannan shi ne abin da ake yi a yawancin gidajen da aka mamaye a Jo'burg."

Nyaope ƙwaya cemai ƙarfin gaske da ke bugarwa wadda ake siyarwa a unguwanni da kwararo a Afika ta Kudu, wadda yawanci ana haɗa ta ne da hodar ibilis ta hiroyin da wiwi da kuma maganin rage kaifin cuta mai karya garkuwar jiki, kuma wasu ma har da maganin kashe ɓera suke haɗawa.

Tana iya sanya ciwon baya, da matsaloli na numfashi da kuma damuwa.

Joseph ya ce yana cike da damuwa kan abin da ya samu mutanen da a dalilin abin da ya yi suka gamu da matsala.

"A wasu lokutan idan ina bacci, sai na riƙa ganin mutane.Mutane sun mutu a ginin nan. Wasu mutanen sun ɓata. Ina nadamar muguwar hanyar da na ɗauka a rayuwata," ya gaya wa BBC.

Joseph ya ce ya bar wannan gungu ne saboda ya fahimci cewa wani gungun na neman kashe shi, inda ya ƙara da cewa ya ji daɗin watsi da wannan rayuwa ta miyagun ayyuka.

To amma ya bayar da dalilin da ya sa yake ganin ɓata-gari na kame iko da irin waɗannan gidaje kuma hukumomin ba sa tashin waɗannan mutane, inda ya ce rashawa ce.

Joseph ya yi iƙirarin cewa ba a fitar da mutane daga waɗannan gini-gine ne saboda, ''kyakkyawar alaƙa da hukumomin birnin da 'yansanda,'' abin da, ''magana ce ta kuɗi'' cin hanci.

Lokacin da aka tuntuɓi hukumar birnin kan zargin haɗa baki da masu kama ginin su zauna, mataimakin darektan sadarwa na birnin Johannesburg, Nthatisi Modingoane, ya ce hukumar ba ta da wasu bayanai masu inganci da ke nuna ana aikata wani abu da ya saɓa doka.

A dangane da kama masu aikata miyagun ayyuka a gine-ginen, kakakin ya ce suna yin ayyuka inda suke kama masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi da haramtattun makamai, abin da ya ce 'yansandan Afirka ta Kudu na gudanar da bincike.

Mr Modingoane ya ƙara da cewa hukumar za ta tsananta matakan rana birnin da miyagun ayyuka".

Hukumar 'yansanda ta Johannesburg ba ta ce komai ba dangane da bayanin da BBC ta nema a kan zargin cin hanci da rashawa kan lamarin gidajen.

Fitar da mazauna waɗannan gine-gine tsofaffi kuma lalatattu kusan ita ce hanyar magance wannan matsala a taƙaice.

Yin hakan zai iya sa a samu cigaban da ake matuƙar buƙata a birnin. To amma aiki ne da zai ci kuɗi sosai, kuma a hukumance ba za a iya yinsa ba kai tsaye cikin sauƙi saboda wasu dokoki.

Da farko dai kundin tsarin mulkin Afirka ta Kudu ya kare 'yancin mutane su samu gida.

Wannan na nufin da zarar mutum ya zauna a gida, kuma zai iya gamsar da hukuma cewa ba shi da inda zai koma, to ba za a iya fitar da shi da ƙarfi ba, sai dai idan gwamnati ta sama masa wani waje da zai iya zama.

Wani gini da aka yi watsi da shi
Bayanan hoto, Mutane da ba su da mafita suna kama irin waɗannan gine-gine da aka yi watsi da su, su zauna a ciki

Babban jami'in doka na birnin Johannesburg, wanda aikinsa ya shafi wani ɓangare na tsakiyar birnin, ya ce ba za a iya aikin fitar da mutane da yawa daga gidajen ba, kuma akai-akai saboda matsala ta kuɗi.

Aikin Marks Mangaba shi ne aiwatar da umarnin kotuna, wanda ya haɗa da fitar da mutane daga gine-gine da zarar mai wannan gini ya samu takardar izinin fitar da mutanen.

Dole ne mai gida - ɗan kasuwa ko kuma gwamnati, ya biya kuɗin ɗawainiyar kwashe mutane daga gidansa idan ya samu wannan umarni na tashin mutanen. To amma Mr Mangaba, ya ce yin wannan gagarumin aiki abu ne da zai ci maƙudan kuɗade.

To amma ko da hukumar birnin Johannesburg za ta iya fitar da tarin mutane daga irin waɗannan gine-gine, za ta haifar da wata babbar matsala ne ta rashin muhalli ga ɗimbin mutane, kuma dole ne ta samar da muhalli da mutanen.

A watan Maris shugaban ƙasar ya nuna muhimmancin gyara waɗannan gidaje na Johannesburg da mutane ke kamawa su zauna, ta yadda za su dace da rayuwar jama'a, rayuwa ta mutunci.

To amma mazaua gidajen da dama na ganin maganar shugaban a matsayin ta fatar baka kawai.

Mr Khetani wanda ke zaune a ginin MBV1 ya ce tun 2008, ya ke gidan, duk da cewa zama ne na wucin-gadi.

Hukumar birnin ta gaya masa cewa babu gidaje na dindindin, ''da za ta je ta sanya mu a ciki,'' in ji shi.

"Birnin ba shi da kuɗi kuma ba wanda ya damu."