Matar da ta fara samun arziƙin dala biliyan 100 a duniya

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Annabelle Liang
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar kasuwanci
Matar da ta gaji kamfanin L'Oréal, Françoise Bettencourt Meyers ta zama wadda ta fara tara dukiyar da ta kai dala biliyan 100 (a canjin naira sun zarce tirliyan ɗaya), kamar yadda jerin lissafin mutanen da suka fi kuɗi a duniya, ya nuna.
Bafaranshiyar mai katafaren kamfanin harkar kwalliya da kakanta ya kafa, tana kan matakin nasara ne saboda harkokin hannun jarin kamfaninta tsawon shekaru gommai, suna matuƙar garawa.
Hannayen jarin L'Oréal sun yi tashin da ba a taɓa gani ba a tarihi, ranar Alhamis.
Kasuwa ta sake buɗewa ga kayan kamfanin, bayan annobar korona, lokacin da mutane ke amfani da kayan kwalliya kaɗan, saboda zaman kulle.
Tsagwaron dukiyar Francoise Bettencourt Meyers, 'yar shekara 70, ta zarce dala biliyan 100 a jerin lissafin biloniyoyi na jaridar Bloomberg, abin da ya sa ta zama, ta 12 mafi kuɗi a duniya.
Har yanzu akwai nisa tsakaninta da takwaranta Bafaranshe Bernard Arnault, wanda shi ne na biyu a jerin masu kuɗin duniya da tsabar dukiyar da ta kai dala biliyan 179b. Mista Arnault shi ne mai LVMH, gungun kamfanonin kayan alatu mafi girma a duniya, wanda ya mallaki kamfanonin sarrafa rantsattsun kaya masu tsadar gaske irinsu Fendi da Louis Vuitton.
L'Oréal nan take bai amsa buƙatar BBC ta yin martani ba.
Miss Bettencourt Meyers ita ce mataimakiyar shugaba a hukumar gudanarwar kamfanin. Kuma ita da 'ya'yanta ne a dunƙule suka mallaki hannun jari mafi girma a L'Oréal da kaso kimanin 35%.
Ta kasance mai tashen da ci gadon L'Oréal daga wajen mahaifiyarta, Liliane Bettencourt, wadda ta rasu a 2017.
Liliane, wadda aka riƙa bayyana ta a matsayin matar da ta fi kowa kuɗi a Faransa, tana da alaƙa ta ƙuƙut da shugabannin ƙasar, kuma ta riƙa ɗaukar hankalin kafofin yaɗa labarai.
A shekarun ƙarshe na rayuwarta, ta ruguntsume da faɗa a bainar jama'a tsakaninta da Françoise, 'yarta ƙwaya ɗaya ƙwal a duniya, wadda ita kuma ta zargi wani mai ɗaukar hoto kuma ɗan ƙwalisa da ci da gumin raunin lafiyar ƙwaƙwalwar mahaifiyarta.
"'Yata tana iya jira cikin haƙuri har sai na mutu maimakon ta je tana yin duk abubuwan da za su iya ingizo ta," ta ce a lokacin wata hira a talbijin.
A 2011 ne, wata kotun Faransa ta yanke hukunci cewa Liliane tana da wani nau'in cutar tsananin mantuwa, kuma ta bai wa 'yarta Françoise ikon juya dukiya da kuɗaɗen shigar uwar. Sai kuma wani dangin nata, aka ɗora masa alhakin kula da lafiya da nagartar jikin Liliane.

Asalin hoton, PASCAL LE SEGRETAIN
An ce Misis Bettencourt Meyers ta fi son rayuwar kaɗaita a kan halartar bukukuwan da masu arziƙin duniya suka saba zuwa.
An san ta da kiɗan fiyano tsawon sa'o'i a kullum sannan ta rubuta littattafai guda biyu - wani nazari a kan Littafin Bayabul da kuma salsalar allolin Girka.
"Ta fi son rayuwa ƙunshe a cikin kura-tandunta. Akasari ta fi son zama cikin rukunin danginta," cewar Tom Sancton, wanda ya rubuta littafin rayuwar mai arziƙin, The Bettencourt Affair.











