Matashiya mai zane-zane da ta fi karfin masu sukarta

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

Nujuum Hashi, wacce ta jure wa nuna bambancin da al'umma ta yi mata don zama mai zane-zane abar girmamawa a Somaliya, ta sa wa ranta zama mai zane a kan yashi tun tana da shekara bakwai, a Mogadishu, babban birnin ƙasar.

Iyayenta ba su da matsuguni a wannan lokacin da yaƙin basasa ya yi ƙamari a shekarun 1990 da farko shekarun 2000.

Sun yi ta ƙaura daga wannan waje zuwa wancan, amma a ko yaushe Hashi kan nemi yashi su yi zane a kai.

"Zane shi ne abin da a ko yaushe ke samar min nutsuwar zuciya," in ji Hashi.

"A lokutan da yaƙi ya yi ƙamari, zane-zanen yanayin zaman lafiya kan kwantar min da hankali.

"Sannan kuma zane ya taimaka min bayan da yaƙin ya lafa.

"Malamin da ke koya min kur'ani ya kasance mai matuƙar zafin rai da mugunta. Yana dukan mu. Ina matuƙar jin tsoron sa.

"Idan aka tashi daga makarantar na kan tsaya a hanya in yi zane a kan yashi don na samu nutsuwa.

"Ina amfani da fensurana na makaranta na zana birni kwacakom a kan bangon ɗakina, na kan yi ta zanuka salo-salo.

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

Hashi ba ta taɓa halartar makarantar koyon zane ba. "Babana ne malamina. Ba gwanin zane ba ne amma yakan yi zane-zane a lokacin da ba ya aikin komai.

"Nakan ce masa ya kkoya in zane. Amma ya rasu tun ina ƙarama."

Sai dai mahaifiyarta ba ta goyon bayan burinta na zama mai zane-zane. Balle kuma maƙwabtansu da suke yi mata kallon wacce take abin da Musulunci bai yarda da shi ba.

Yawancin Musulmai sun yi amannar cewa zane mutane da dabbobi haramun ne.

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

"Sun tursasa min daina yin zane. Na yi watsi da harkar zane kwata-kwata na fara karantar koyon aikin jinya. Amma sai na ji duk ya ginshe ni.

Wata rana sai na yanke shawarar cewa ba zan taɓa barin zane-zane ba, duk abin da mutane za su faɗa sai dai su yi."

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

A yanzu Hashi na samun abin rufin asiri daga harkar zane-zanentya har ma tana taimaka wa ƴan uwa da danginta.

Matashiyar mai shekara 26 na zaune a Hargeisa, babban birnin ƙasar Somalilanda wadda ta ayyana kanta a mai cin gashin kai, tana kuma samun ayyuka daga hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin ƙasashen duniya da ma ɗaiɗaikun mutane.

Ma'aikatar Ilimi ta Somaliland ta neme ta da ta yi zanuka da za a yi amfani da su a shirinta na aika yara ƴan mata makaranta.

"Wannan yarinyar na yin aikinta na gida da aka ba ta a makaranta, a yayin da take kula da awakin da suke kiwo, bayan komawarta gida.

"Ina so na nuna cewa yara mata za su iya haɗa karatu da ayyukan gida."

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

Ta samu wani aikin zane a kwana nan daga wata kafar yaɗa labarai ta mata zalla ta Bilan, da aka kafa ta a baya-bayan nan a Mogadishu.

Aikin ya nuna yadda wata ƴar jarida take ɗaukar bidiyon mata a yayin da suke ayyukansu na yau da kullum.

Idan aka kalli ƙarƙashin bishiyar sisau za a iya ganin Hashi na zanen hoto.

Samun kayan aikin zane na da wahala a Somalia da Somaliland, don haka sai dai ta nemi ƙawayenta daga Kenya da Djibouti ko sauran wurare su aika mata.

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

A hankali ayyukan Hashi na samun karɓuwa ta yadda har wasu kafafen yada labarai kan yi amfani da ayyukanta.

A ƙalla mutum biyar aka kashe a wajen wani rikici da dakarun tsaro a zanga-zangar adawa da aka yi a watan Agusta a Somaliland

"Na ga hoton wata mace tana ɓuya a bayan kujera a lokacin da wani ɗan sanda ya buɗe wuta. Na kasa cire abin daga raina."

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

"Wani minista ya halarci jana'izar ɗaya daga cikin masu zanga-zangar da ya mutu, ba tare da an gayyace shi ba. Wasu mutane sun ji haushin hakan har wata mata ta tunkuɗe shi ta baya.

"A yanzu ana ganinta a matsayin wata gwarzuwar ƴar adawa!"

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

Yunwa da matsanancin fari da ake fama da su a yankin ya sa ƴan Somaliya da dama na cikin matsanancin hali.

"Ƴan siyasa ne roƙon ƙasashen duniya su aika kuɗaɗe ga masu fama da yunwa," a cewar Hashi. "Amma sai su maƙale su a aljihunsu."

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

Fari da bushewar muhalli na daga cikin abubuwan da suka ja hankali wajen yin zane-zane.

Wannan zanen da ke ɗakin aikinta a Hargeisa na nuna yadda ƙasa ta bushe da kuma yadda aka sare bishiyoyi don a samu itace.

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

Da yawan zane-zanen Hashi na nuna yadda mutane ke yin harkokinsu na yau da kullum ne.

"Wannan hoton na sama na nuna yadda wasu iyalai makiyaya ke sauraron wani shirin rediyo na sashen BBC Somali da fitaccen ɗan jarida Ahmed Hassan Awke ke gabatarwa."

Sai dai abin takaici tuni ya rasu. Mutane na ƙaunarsa sosai, musamman ma muryarsa mai jan hankalin masu sauraro."

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

Wasu zane-zanen kuma takan yi kan abin da ya shafe ta kai tsaye.

“Wannan hoton na nuna ni ina fama da cutar korona. Na yi rashin lafiya sosai har ta kai na fara tunanin zan mutu kamar yadda ta kashe wasu mutanen da na sani.

Bayan da na zana hoton nan, sai mutane suka fara kira suna tambayata shawarwari a kan matakan da na bi na warke.

NUJUUM HASHI

Asalin hoton, NUJUUM HASHI

Ɗaya daga cikin lokutan da Hashi ta fi so shi ne ta je wajen gari, musamman Tsaunukan Sheikh masu ban sha’awa da ke Somaliland.

“A wannan lokacin ina tafiya ne tare da ƙawayena wdanda ba su iya zane ba. Sai na basu kayan aikina kuma kafin rana ta faɗi sai ga shi sun yi zane-zane masu ban sha’awa.

“Zane na ba ni damar nuna wasu fannonin rayuwa na Somaliya, ba abubuwan da aka san ƙsar da su ba kamar yaƙi da yunwa da fari da cututtuka.

Dukkan hotuna suna da haƙƙin mallaka.