Yadda rikicin Gaza ya jefa ‘yan wasan motsa jiki a tsaka mai wuya

    • Marubuci, Kevin Hand
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa

Ya kamata martanin Mohamed Salah game da rikicin Isra'ila da Gaza ya zama manuniya kan yanayin wasannin motsa jiki a nan gaba, a cewar wani tsohon wakilin 'yan wasa kuma malami.

Dan wasan gaba na kumgiyar Liverpool dan asalin kasar Masar ya yi kira ga "shugabannin duniya da su taru domin hana ci gaba da kashe rayukan da ba su ji ba ba su gani ba" sakamakon wani mummunan harin da aka kai a asibitin birnin Gaza a watan jiya.

Dan wasan mai shekaru 31 a da haihuwa yana daya daga cikin ’yan wasa da dama da ke da dimbin mabuya a shafukan sada zumunta da suka yi tsokaci kan rikicin da ke faruwa tsakanin Isra’ila da Hamas, wanda gwamnatocin Birtaniya da Amurka suka ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci.

Rikicin na yanzu ya zo ne bayan da 'yan bindigar Hamas suka kaddamar da farmakin da ba a taba ganin irin salhi ba a Isra'ila, a ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe fiye da mutum 1,400, yayin da kai hare-haren ramuwar gayya a Gaza ya yi sanadin mutuwar sama da mutum10,000, a cewar ma'aikatar kiwon lafiyar da ke karkashin ikon Hamas.

"Salah misali ne na wani da aka matsa masa lamba don ganin ya goyi bayan wani bangare saboda, sanadiyyar asalinsa," Ian Bayley, wanda a yanzu babban malami ne a fannin aikin jarida a jami'ar Staffordshire, ya shaida wa BBC Sport Africa

"Amma ya yi nazarin lamarin ya ce: 'Abin da na tsaya a kai shi ne zaman lafiya da kuma kawo karshen wahala'."

Bayley ya yi nuni da cewa kalaman Salah “bai gamsar da wasu mutane ba” wadanda suke ganin ya kamata dan wasan da ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika sau biyu, ya kamata ya yi amfani da dimbin tasirinsa wajen daukar “matsayi na siyasa”.

"Da ya fitar da sako daga baya, mutane da yawa sun yaba masa saboda yanayin kalamansa na jin kai, amma duk da haka wasu na ganin ya kamata ne a ce matsayinsa ya fi goyon bayan Larabawa da Falasdinawa," in ji Bayley.

"Amma ba zai iya yin hakan ba saboda hakan zai iya cin kari da manufofin sada zumunta na kulob dinsa."

A lokacin da tauraruwar Tennis 'yar kasar Tunisia, Ons Jabeur ta yi magana kan batun a farkon wannan watan, matsayinta bai tayar da irin wannan kurar ba.

"Na yanke shawarar bayar da wani bangare na kudaden da na ci a gasa don taimaka wa Falasdinawa," in ji wadda ke a matsayi na bakwai a duniya a wasan karshe na WTA da aka kammala a Mexico.

"Ba sakon siyasa ba ne, batun bil'adama ne, ina son zaman lafiya a duniya."

Bayley ya kuma yi maraba da sakon Jabeur, yana mai cewa "duk wani matakin da zai taimaka wajen saukaka wahalhalun da 'yan’adam ke fama da su, dole ne a yaba masa, matukar dai an yi shi ne don taimaka wa bil'adama ba siyasa ba".

Ya kara da cewa "Batu mafi wahala shi ne rikicin ya jawo rarrabuwar ra'ayi ta yadda duk wani matakin da aka dauka, kuma duk kyakykyawan manufa da niyyar da ake da ita, babu makawa zai jawo yabo da kuma suka," in ji shi.

To ko mene ne martanin Salah, da Jabeur da manyan ‘yan Afirka suka fada mana game da matsayin siyasa da ‘yan wasa suka samu kansu a ciki? Kuma wadanne hatsari ne ke tattare da amfani da dandalinsu wajen bayyana ra’ayoyinsu kan manyan batutuwa?

Dandalin sada zumunta 'abu mai kawo canji'

Tun lokacin da aka fara yakin a ranar 7 ga watan Oktoba, an yi ta nuna goyon baya ga al'ummar Falastinwa a tsakanin kungiyoyin wasanni da 'yan wasa da magoya bayansu a fadin Afirka, musamman a arewacin Afirka.

Gabanin wasan sada zumunci da Cape Verde a ranar 12 ga watan Oktoba, 'yan wasan kwallon kafar Aljeriya sun shiga filin wasan sanye da wani kyalle da ake kira keffiyeh, rawanin da ke da alaka da gwagwarmayar Falasdinawa, a inda 'yan wasan tare da kyaftin Riyad Mahrez suka rika kada tutar Falasdinawa a filin wasan.

"A gaskiya ba a samu wasu fitattun 'yan Aljeriya da ba su yi magana akalla ba don nuna tausayi game da wahalhalun da Falasdinawa ke fama da su," in ji dan jaridar kwallon kafa na Aljeriya Maher Mezahi.

"Abin da ya kamata ku fahimta shi ne cewa Faransa ta yi wa Aljeriya mulkin mallaka na tsawon shekaru 132 sannan kuma Turawa sama da miliyan daya sun zauna a Aljeriya a shekara ta 1962, don haka da dama daga cikin 'yan Aljeriya na ganin halin da Falasdinawan ke ciki a matsayin abin da ya faru da su a baya."

Mezahi ya bayyana kalaman Salah a matsayin "mafi ban sha'awa game da yadda ake tursasa wani fitaccen jarumin da ya yi magana" , yayin da Carole Kimutai, kwararriya kan harkokin yada labarai na zamani a Kenya, ke cewa matsin lamba ya na cikin abubuwan da zamani ya kawo.

"Lokacin da batutuwa kamar wariyar launin fata, da jinsi, da rikici, da addini, zubar da ciki da sauransu suka taso, taurarin wasanni na iya zabar ko za su yi magana a bainar jama'a ko kuma su yi shuru," kamar yadda ta shaida wa BBC Sport Africa.

"Amma lokacin da batun ya yi kusa kusa da gida, jama'a za su sa ran mutum ya yi magana. Gaza na kusa da Salah. Wannan ya nuna a fili cewa dole ne 'yan wasa da ke da hannu a al'amura da yawa irin su Salah su gwamutsa wadannan abubuwan da sana'arsu ta wasanni."

Don haka da tauraron Liverpool, wanda garinsa Nagrig na kasar Masar bai wuce nisan kilomita 350 daga Gaza ba, ya bukaci a daure domin kare rayukan Falasdinawa, ko an yi mamaki lokacin da kulob din Crystal Palace na Premier ya fito ya goyi bayan Isra’ila?

Ba haka ba ne a ra'ayin wani babban farfesa fannin wasanni da tattalin arziki.

"Biyu daga cikin masu kulob din Yahudawa ne, na ukun kuma Ba'amurke ne wanda ke da kusanci da al'ummar Yahudawan Amurka," in ji Simon Chadwick na Makarantar Kasuwancin Skema.

"Mallaka da al'adun kulob din suna da matukar muhimmanci, don haka muna samun wadannan ra'ayoyi daban-daban."

A Isra'ila, dan wasan Brazil Felipe Kitadai, wanda ya lashe lambar yabo ta Olympics a shekarar 2012, ya nuna wa kasar "kauna da dukkan goyon baya" duk da cewa an ce yana neman barin kasar da ta kasance wurin zamansa na baya-bayan nan yayin da dan wasan kwallon kafa Manor Solomon na cikin wadanda suka soki Hamas a shafukan sada zumunta.

Yayin da ya dandana yadda ya ji take lokacin da ya kasance a Kyiv a ranar da Rasha ta mamaye Ukraine, dan wasan Tottenham Hotspur Solomon ya ba da labarin yadda danginsa da abokansa suka shiga cikin "mawuyacin hali" sakamakon rikicin Isra'ila da Gaza.

"Shafukan sada zumunta su muhimman masu sauya fasalin al'amura ne," in ji Bayley.

"In da wannan rikici ya faru ne shekaru 30 da suka gabata, za a iya cewa 'yan wasan kwallon kafa ba za su fuskanci matsin lamba ba sakamakon abin da ke fitowa a shafukan sada zumunta."

"Ba abu ne mai yiwuwa ba, yanayi ne na tsaka-mai-wuya ga kowane ɗan wasan ƙwallon ƙafa a cikin yanayi kamar yadda muke ciki yanzu, wanda kusan ba a taɓa ganin irin sa ba.

Haduran bayyana ra'ayi

Shekara uku da suka gabata, Jabeur ta fuskanci barazanar kisa a shafukan sada zumunta bayan ta zabi mayar da siyasa gefe guda ta hanyar buga wasa da Isra'ila, kasar da gwamnatinta ba ta amince da ita ba, a gasar wasan tennis ta kasa da kasa.

Shiga fagen siyasa, ko na duniya ko akasin haka, ya zama mai haɗari ga wasu cikin kwanakin nan.

Fitaccen dan wasan kwallon kwando Lebron James ya sha suka daga mutane da yawa bayan ya yi rubutu don nuna goyon baya ga Isra'ila bayan harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba.

Bayan da ya fito ya nuna goyon bayansa ga Isra'ila, babban dan damben boksin Floyd Mayweather shi ma ya fuskanci irin wannan caccakar, sannan kuma akwai 'yan wasan kwallon kafa da dama da suka fuskanci hukunci daga kungiyoyinsu kan matsayarsu.

Kungiyar Nice ta dakatar da dan wasan baya na kasar Aljeriya Youcef Atal, inda kungiyar ta Faransa ba ta gamsu da wani rubutu da ya yi ba, wanda ya goge tare da bayar da hakuri, lamarin da ake ganin ta soki Yahudawa. A karshe hukumar da ke kula da gasar Ligue 1 ta Faransa ta dakatar da dan wasan mai shekaru 27 na wasanni bakwai.

Noussair Mazraoui ya fuskanci suka bayan ya wallafa wani bidiyo mai goyon bayan Falasdinawa a shafinsa na Instagram, inda kulob dinsa na Bayern Munich ya tattauna da dan wasan na Maroko wanda daga baya ya ce zai ci gaba da adawa da kowane irin ta'addanci, kiyayya da tashin hankali. .

A Jamus a makon da ya gabata, Mainz ta soke kwantiragin dan wasan kasar Holland Anwar El Ghazi saboda wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta game da rikicin Isra'ila da Gaza wanda kulob din na Bundesliga ya dauka a mtasayin goyon bayan Falasdinawa.