Yadda Tinubu ya naɗa Abdullahi Pakistan a matsayin sabon shugaban NAHCON

Asalin hoton, Classic Photography
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sallami shugaban hukumar alhazai ta ƙasar, Malam Jalal Arabi, kwana huɗu bayan hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta kama shi.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Litinin ta tabbatar da naɗa Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin sabon shugaban hukumar.
Sallamar tasa na zuwa ne bayan zargin shugaban da yin almundahanar wani ɓangare na naira biliyan 90 da gwamnatin Najeriya ta bai wa hukumarsa ta National Hajj Comission of Nigeria (Nahcon) a matsayin tallafi ga aikin Hajjin 2024 da aka kammala.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilin da ya sa aka cire Arabi daga muƙamin ba.
"Farfesa Usman shahararren malami ne da ya samu shaida daga mashahuran cibiyoyin Musulunci - a Jami'ar Madina da kuma Jami'ar Peshawar da ke Pakistan," a cewar sanarwar.
Ya taɓa shugabantar hukumar alhazai ta jihar Kano da ke arewacin ƙasar, "abin da ke nufin ya jagoranci hukuma mai alhazai mafiya yawa a ƙasa," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sai Majalisar Dattawan Najeriya ta amince kafin naɗin farfesan ya tabbata.
Dalilin da ya sa EFCC ke tsare da Jalal Arabi

Asalin hoton, Nahcon
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar Juma'a da ta gabata ne wata majiya mai ƙarfi a EFCC ta tabbatar wa BBC cewa hukumar na tsare da shi tare da sakataren hukumar, Abdullahi Kontagora.
Hukumar ta yi iƙirarin cewa an gano kudin da yawansu ya zarta Riyal 300,000 a hannun shugaban da wasu manyan jami’an hukumar Hajjin ta Najeriya. Sai dai ba su mayar da martani ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Majiyar ta ce binckensu ya gano shugaban hukumar ya yi amfani da wani ɓangare na naira biliyan 90 ɗin da gwamnatin Najeriya wajen biyan kansa da manyan jami’an kuɗaɗen da suka wuce kima.
Kazalika, hukumar ta ce a kasafin kudi na bana ainihin kudaden da aka ware wa kwamishinoni da manyan daraktoci da ma’aikatan hukumar sun saɓa yadda suka tsara nasu, tare da wawure kaso mafi yawa daga abin da aka ƙayyade wa kowanennsu.
Majiyar ta EFCC ta ƙara da cewa ana zargin Jalal Arabi da ware wa kansa Riyal 50,000 maimakon 15,929 da aka ware masa a hukumance, yayin da kwamishinonin hukumar uku da aka ware wa 15,929 kowanensu sun karɓi 40,000 kowanne.







