Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kafa haɗakar ƙasashen AES bai razana Ecowas ba - Tuggar
Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya ce babu abin da ficewar haɗakar ƙasashen AES wato Nijar da Mali da Burkina Faso zai yi wa ECOWAS.
Ministan na magana dangane da ranar cikas ƙungiyar ta Ecowas shekaru 50 da kafawa.
A ranar 28 ga watan Mayun 1975, shugabannin ƙasashe 15 da suka ƙunshi Najeriya a lokacin, Janar Yakubu Gowon suka haifar da Ecowas da nufin ƙarfafa hadin kai da bunƙasar tattalin arziƙi da ƴanci da walwala ga al'ummar yankin na shige da fice tsakanin ƙasashen.
Kungiyar ta taka rawa musamman a yaƙin basasa a Liberia da Saliyo inda ta tura dakaru wato Ecomog domin wanzar da zaman lafiya.
To sai dai kuma ƙungiyar ta ECOWAS, tana fuskantar ƙalubale musamman na samar da kuɗin bai-ɗaya matakin da ake ci gaba da tattaunawa yayin da kuma a yanzu shekara 50 da kafuwarta.
Ecowas na fuskantar barazanar wargajewa bayan juyin mulki a ƙasahen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar, lamarin da ya kai ga ficewarsu daga Ecowas tare da kafa tasu ƙungiyar.
Ana ganin kamar ficewar waɗannan ƙasashe daga ƙungiyar zai ja mata babban koma baya, to amma cikin wata hira da BBC, ministan harkokin waje na Najeriya, Amb Yusuf Maitama Tuggar, ya ce ba haka ba ne.
" Ana zuzuta ficewar waɗannan ƙasashen, idan aka tuna ƙasashe 15 ne a cikin wannan ƙungiya sai kuma ƙasashe uku suka fice, to ai akwai ƙasashe 12 da suka rage, amma sai mutane su rinƙa nuna kamar waɗannan ƙasashe ukun da suka fice sun yi rinjaye."
Ministan harkokin wajen na Najeriyar ya ƙara da cewa " ya kamata mutane su sani ƙasashe 12 da suka rage a cikin ECOWAS a yanzu, su ne waɗanda suke da teku su ne suke cinikayya ta zamani tare da sauran ƙasashen duniya, ga kuma irin arziƙin da ake samu daga ƙasashen wanda har ya kai ga gina zamanancin da ake ciki."
"Akwai wasu kasashe da dama daga cikin kasashe 12 da suka rage a ECOWAS, da ke kusa da tekun atlanta, inda ake harkokin cinikayya sosai." In ji ministan.
Kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar sun fice daga ECOWAS ne sakamakon takunkuman kariyar tattalin arziki da Ecowas ta ƙaƙaba mu su bayan juyin mulki da sojoji suka yi a ƙasashen.
Ƙasashen Mali da Niger da Burkina Faso dai na zargin cewa babu abin da zamansu a Ecowas ya tsinana musu.