Jirgin Ukraine ya kai wa jirgin ruwan Rasha hari a Bahar Aswad

Jirgin ruwan Rasha da aka hara

Asalin hoton, Ukraine Military

Bayanan hoto, Rasha ta tabbatar da kai harin amma Ukraine na cewa ta yi wa jirgin ɓarna
    • Marubuci, Daga James Waterhouse da Kathryn Armstrong
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Harin da jirgin Ukraine maras matuƙi ya kai ya lalata wani jirgin ruwan Rasha a tekun Bahar Aswad (Black Sea), a cewar wasu majiyoyi a Ukraine.

Rahotanni sun ce an kai harin ne a kusa da gaɓar ruwan Novorossiysk ta Rasha, wata babbar mashigar kayayyaki da ƙasar ke amfani da shi.

Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce ta daƙile wani harin Ukraine da jirage marasa matuƙa biyu a kan sansaninta na sojan ruwa.

Sai dai majiyoyi a hukumomin tsaron Ukraine sun ce harin da aka kai wa jirgin Olenegorsky Gornyak ya yi nasara har ma an yi masa ɓarna sosai.

Sun faɗa wa BBC cewa wani jirgin ruwa maras matuƙi ne ya kai harin ɗauke da ababen fashewa masu nauyin kilogiram 450kg.

Rasha ba ta bayyana wata ɓarna ba a nata rahoton.

Bidiyon da wata majiya ta aiko wa BBC ya nuna ya nuna jirgi maras matuƙi yana tunkarar wani jirgi da ake zaton Olenegorsky Gornyak ne.

Bidiyon ya nuna wani ƙaramin jirgi ya je har kusa da jirgin ruwan kafin daga baya ya katse, sakamakon ɓarnar.

Wani bidiyon da ba a tantance sahihancinsa ba ya nuna jirgin ya jirkice a ɓangare ɗaya.

Ukraine ba ta ɗauki alhakin kai harin ba a hukumance.

An dakatar da zirga-zirgar jirage a gaɓar ruwan Novorossiysk na ɗan lokaci bayan harin, a cewar kamfanin Caspian Pipeline Consortium, wanda ke lodin man fetur a gaɓar ruwan.

Jiragen ƙanana ne kuma marasa matuƙa waɗanda ke yawo a sama ko kuma ƙasan ruwa.

Binciken da sashen BBC Verify ya yi ya gano cewa Ukraine ta kai aƙalla hari 10 da jiragen ruwa marasa matuƙa - inda take harar jiragen ruwan soja da kuma sansanin Rasha a Sevastopol da Novorossiysk.

An samu bayananan ne daga sanrwar da Rasha da Ukraine ke fitarwa da kuma rahotannin kafofin labarai na ƙasashen. Majiyoyin tsaro a Ukraine sun faɗa wa CNN cewa da jiragen ruwa marasa matuƙa aka kai hari kan Gadar Kerch zuwa Crimea a watan Yuli.

Novorossiysk na cikin manyan tashoshin jiragen ruwa a Bahar Aswad.

Fafatawa a tekun ta ƙaru a 'yan makonnin nan bayan Rasha ta fice daga yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya da ta ba da damar fitar da hatsin Ukraine ta cikin ƙasashen biyu.