Bikin rawa da mai wasa da wuƙa cikin hotunan Afirka

j

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Talata, Mutanen Habasha na bikin Shuwalid da ake yi bayan kammala azumi da iyaye da kakanni ke yi a birnin Harar ko wacce shekara
A

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Juma'a wata mai sha'awar zane-zane ke ɗaukar hotunan zanen da wata kwararriyar mai zane Thandiwe Muriu ta yi, yayin bikin makon zane da aka yi a Italiya....
S

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai wasan ninƙaya 'yan asalin Italiya da Najeriya Sara Curtis mai shekara 17, ta yi nutso a ranar Talata yayin da take shirin tunkarar gasar Olympics ta 2024.
G

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai wasan tsalle a kan talakmin taya dan Kenya kenan ke wasa a ranar Asabar a Nairobi babban birnin ƙasar.
P

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A dai wannan ranar, mutanen Afrika sun je bikin rawa da aka yi na 'yan Kongo a tsakiyar Amurka.
P

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Juma, wata mota da aka yi wa ado da hoton Sarkin mawaƙa a Abigjan babban birnin Ivory Coast. An sanya wa wani ƙauye sunan Micheal Jackson a ƙasar lokacin da ya kai ziyara a 1992.
d

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tawagar kurame masu rawa daga Burkina Faso na rawa a ranar Laraba yayin wani wasan nishaɗi da kasuwancin fasaha da aka yi a Ivory Coast.
B

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mai rini na runa fatan dabbobi a birnin Fez da ke arewacin Morocco a ranar Laraba.
H

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu gudu a saman ruwa a Afrika Ta Kudu da safe na shirin fara wasa a bakin ruwa a ranar Alhamis.
H

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mai wasa da wuƙa a bikin Dipri a ranar Asabar. Irin wannan wasa na daga wani ɓangare na al'adun mutanen kudu maso gabashin Ivory Coast.
O

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Litinin a Masar, Ana yi wa wani ɗan Sudan aski a wani shago a birnin Alƙahira. Kimanin 'yan Sudan dubu dari biyar ne da suka tsere daga ƙasar suka shiga Masar tun bayan ɓarkewar rikicin ƙasar shekara guda baya.
r

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Asabar a Kamaru, an zagaye masarauta da ke kan mulki....
o

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An fara wasan harbin bindiga a birnin Foumban a sabon gidan tarihin Bamoun.