'An yi min auren dole ina da shekara 12'

Tamara

Asalin hoton, Yousef Eldin/BBC

    • Marubuci, By Megha Mohan and Yousef Eldin
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC 100 Women

An yi ƙiyasin cewa ana aurar da ɗaya cikin kowane mata biyar kafin su kai shekara 18 a faɗin duniya. Hatta ƙasashen da ke da dokokin kare haƙƙin yara kan gaza wajen aiwatar da su.

Amma an fara samun sauyi a ƙasar Malawi.

Karo na uku da muka ziyarci Tamara, an faɗa mana cewa ta fita zuwa gona don yin huɗa.

Duk da tana ɗauke da cikin wata tara, babu hutu a wajen matashiyar mai shekara 13 da haihuwa.

Mijin Tamara (ba sunanta na gaskiya ba ne) mai shekara 20 da ɗoriya ya gudu ya bar ta, abin da ya sa ta koma zama a wurin 'yar uwar mahaifinta tsawon watanni.

Ya ji labarin cewa hukumomi na shirin zuwa don kuɓutar da Tamara daga auren da aka yi ba bisa ƙa'ida ba, sai ya gudu kafin su ƙaraso, wanda ya sa ta koma ƙauyen 'yar uwar mahaifin nata.

Abubuwa da yawa sun sauya a rayuwar Tamara. Yarinyar da aka haifa a ƙauyen Malawi da ke gundumar Neno, iyayenta na rayuwa cikin ƙasa da ƙiyasin talauci na gwamnatin ƙasar, kamar dai kashi 65 cikin 100 na mazauna yankin.

Lokacin da iyayen Tamara suka kwanta rashin lafiya kuma suka rasu, sai iyayen mahaifiyarta suka riƙe ta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amma bayan wata ɗaya, bayan Tamara ta dawo daga makaranta wata rana, kakar tata ta ba ta wani labari.

"Ta faɗa min cewa ya kamata na yi aure," in ji ta. "Har ma wani mutum ya kawo mata kuɗi."

Mutumin da Tamara ba ta taɓa haɗuwa da shi ba, shi ne ya biya kuɗin aure 15,000 na kuɗin Malawi Kwacha - kusan dala $9 ke nan.

Tuni kakarta ta kashe kuɗin wajen sayen masarar ciyar da gida, kuma mutumin ya fara nuna gajen haƙuri. Yana son a ba shi yarinyar da ya biya kuɗinta - wato matarsa - ta bar makaranta don ta zauna da shi.

An haramta auren yara a Malawi tun 2017, amma an daɗe ana yin sa a matsayin al'ada kuma har yanzu ana yin sa a ƙauyuka kamar na su Tamara, inda kusan kashi 85 na 'yan ƙasar ke zaune.

Ana aurar da sama da kashi 40 cikin 100 na yaran matan Malawi kafin su kai shekara 18, a cewar ƙungiyar Girls Not Brides.

"Rayuwar ta yi tsauri saboda mijin ya girme ni sosai," in ji Tamara. "Ya dinga duka na duk lokacin da na yi wani kuskure."

Ta zauna tare da shi wata uku, har sai da wani ya tsegunta wa hukumar kula da zamantakewa. Bayan an fara shirin mayar da Tamara makaranta, sai ta lura da wani abu. Ba ta ga jinin hailarta ba na 'yan wasu watanni.

Shekararta 12 a lokacin da ta ɗauki cikin.

grey line

Wani rukunin matasa mata da ba su wuce shekara 20 da ɗoriya ba sun taru a ɗakin yaɗa labarai na gidan rediyon Radio Mzati kuma suna shirin fara yin maagana kai-tsaye.

"Alo! Alo! Barkanmu da sake haɗuwa a sabon shirin Ticheze Atsikana," kamar yadda ma gabatarwa Chikondi Kuphata ta fara, "shirin da ke ba mu mu mata damar tattauna lamurran da suka shafe mu!"

Kuphata da abokiyar gabatarwarta Lucy Morris na magana ne da Ingilishi da kuma harshen Chichewa - sunan shirin na nufin "mu tattauna" a harshen Chichewa. Shiri ne na mako-mako da ƙungiyar AGE Africa ta ɗauki nauyi don ƙarfafa wa 'yan mata na ƙauye gwiwar ci gaba da karatu a Malawi.

Lucy Morris ta ce idan yara mata suka san 'yancinsu za su guji auren wuri

Asalin hoton, Yousef Eldin / BBC

Bayanan hoto, Lucy Morris ta ce idan yara mata suka san 'yancinsu za su guji auren wuri

Yaran da ake aurarwa da ƙuruciyarsu

  • Kusan miliyan 650 na matan da ke raye ana aurar da su kafin su kai shekara 18, in ji asusun yara na MDD Unicef
  • Nahiyar Kudancin Asiya ne ya fi yawan yaran da ake yi wa auren wuri da kusan kashi 40 cikin 100 na duka ƙasashen duniya, sai kuma yankin Saharar Afirka da ke biye masa da kashi 18
  • A faɗin duniya, kusan kashi 21 na yara mata na yin aure suna yara, a cewar ƙungiyar ba da agaji ta World Vision
  • Auren wuri ya ragu a Asiya da Afirka cikin shekara 10 da suka wuce, amma a Latin Amurka da Caribbean ba a samu wani cigaba ba tsawon shekara 25, in ji ƙungiyar Girls Not Brides

Mako biyu da suka wuce, bayan ziyarar da Michelle Obama ta kai Malawi, Amal Clooney, da Melinda Gates, Shugaba Lazarus Chakwera ya sanar da ƙarin kuɗi wajen yaƙi da auren wuri.

Bayan wani shiri na hukumar kula da yawan al''umma ta MDD a 2020, sama da sarakunan gargajiya 100 ne a Malawi - kusan ɗaya cikin huɗu ke nan a ƙasar -suka yi alƙawarin yaƙar auren wuri a garuruwansu. Duk da haka babu abin da za su iya yi idan iyalai na bai wa tsofaffi 'ya'yansu.

Tamara ta ci gaba aiki a gona duk da cewa tana ɗauke da cikin wata tara

Asalin hoton, Yousef Eldin / BBC

Bayanan hoto, Tamara ta ci gaba aiki a gona duk da cewa tana ɗauke da cikin wata tara

Sarakuna biyu a gundumar Neno ta su Tamara, sun faɗa mana cewa ba za su ce ba a gudanar da auren wuri cikin sirri ba a gundumominsu.

“Wasu iyayen kan zo wurinmu da batun amma mukan ki amincewa da irin wadanann aurarraki,” in ji John Juwa, shugaban wata al’umma mai yawan mutane sama da 2,000.

“Wasu iyayen kan nace kan cewa yaran nasu na da lafiya kuma sun isa aure, amma mukan bukace su su kawo takardunsu na asibiti domin tabbatar da shekarunsu.”

George Mphinda, wani shugaban al’umma, ya ce: “Ba za mu ce ba a aurar da yara ba amma koda ana yi to ana boye mana.”

To amma nauyin hana aurar da yara a hannun wane ne yake?

Bayan ya yi shiru na wani dan lokaci, Mr Juwa ya ce, “Nauyinmu ne a matsayinmu na shugabannin al’umma, tare da hadin kan iyalai.”

grey line

Tamara ta haifi lafiyayyen danta namiji.

Wata karamar kungiya mai zaman kanta a Malawi da ake kira People Serving Girls At Risk, ce ta biya wani mai keke domin ya kai ta asibiti a lokacin da ta fara nakuda.

Sun kuma rika duba ta a kai-a akai.

An ci sa’a nakudar Tamara ta zo cikin sauki.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce matsalolin nakuda da na daukar ciki su ne manyan silar mace-macen mata, saboda haka dole ne a yi taka-tsantsan.

Mata 100