An zartar da hukuncin kisa kan matan da suka kashe mazajensu a Iran

 Iran ta kashe mata a wannan shekarar fiye da kowacce kasa a duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iran ta kashe mata a wannan shekarar fiye da kowacce kasa a duniya

Hukumomi a Iran sun zartar da hukuncin kisa kan mata uku ranar Laraba wadanda ake zargi da hannu a kisan mazajensu, a cewar wata kungiyar kare hakkin dan adam.

Kungiyar Iran Human Rights Group ta ce matan uku suna cikin mutum 32 da aka zartawar hukuncin kisa a cikin mako guda.

Wata yarinya da aka taba yi wa auren wuri, na cikin wadanda aka zartarwa hukuncin na kisa bayan samunta da laifi wurin kashe mijinta.

An yi amannar cewa hukumomi a Iran sun kara kaimi wurin zartar da hukuncin kisa, inda a wannan shekarar suka ninka mutanen da suka kashe idan aka kawatanta da bara.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun bayar da rahoton cewa kasar Iran ta kashe mata a wannan shekarar fiye da kowacce kasa a duniya, kuma akasarinsu ana zarginsu da kashe mazansu ne.

Ranar Laraba, kungiyar the Iran Human Rights Group ta ce an rataye wadda aka yi wa auren wurin Soheila Abadi a gidan yari bayan an same ta da laifin kashe mijinta bayan sun yi aure shekaru 10 da suka wuce a yayin da take da shekara 15 da haihuwa.

Bayanai daga kotun da ta zartar mata da hukuncin kisa sun nuna cewa ta kashe mijin ne bayan wata "rashin jituwa da ta faru a tsakansu".

Su ma sauran matan biyu da aka zartarwa hukuncin kisa ranar Laraba an kama su ne da laifin kashe mazansu, a cewar kungiyoyin kare hakkin dan adam.

Masu fafutuka sun ce yawancin shari'o'in sun shafi batun cin zarafi a cikin gida amma kotunan Iran suna yawaita yin watsi da irin wannan batu idan sun zo yanke hukunci.

Babu cikakkun alkaluma kan mutanen da aka zartarwa hukuncin kisa domin kuwa hukumomi a Iran ba sa sanar da dukkan bayanai game da zartar da hukunce-hukuncen kisa a kasar.