Me ya sa 'yan daban Kano ke zubar da makamai da rungumar zaman lafiya?

Weapons seized in Kano

Asalin hoton, Kano state police command

Mazauna birnin Kano na bayyana shiga wani sabon yanayi na raguwar rikici da hare-haren 'yan daba, masu haddasa tashin hankali da kuma ƙwacen waya.

Matasan da ake zargi da aikata irin waɗannan ayyukan tarzoma, a yanzu suna ƙara amsa kiran hukumomi, suna rungumar wani shirin zaman lafiya a jihar.

Rundunar 'yan sandan Kano ta ce a baya-bayan 'yan daba 43 sun sake ajiye makamansu, inda suka yi alƙawarin tuba da kuma neman afuwar al'umma da hukuma.

Wannan dai wani ɓangare ne na wani sabon tunanin da 'yan sanda suka ɓullo da shi, don tunkarar rikici da hare-haren 'yan daba.

Masu lura da al'amura a Kano, na cewa duk da kame da ɗaurin da hukumomi ke yi, matsalar tarzomar 'yan daba ta ci gaba da ƙaruwa a jihar, cibiyar kasuwanci da yawan mutane a arewacin Najeriya.

'Yan sanda sun ce kafin rukunin 'yan daban da suka tuba na baya-bayan nan, akwai wasu 100 da su ma suka sanar da ajiye makamai tare da rungumar zaman lafiya.

"Adadin yanzu ya kai 143, na waɗanda suka tuba."

"Mafi yawan waɗanda suke ajiye makamai, sukan yi alƙawari za su yi aiki tare da 'yan sanda domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Kano," in ji sanarwar 'yan sanda.

Jihar dai ta yi ƙaurin-suna da 'yan daba, masu amfani da wuƙaƙe da gariyo da barandami da ƙaho da adda da ɗanbuda da fafalo wajen yanka da sara da suka, don raba mutum da wayarsa ko wata dukiya.

Cikin manyan tashe-tashen hankulan 'yan daba ke haddasawa, akwai faɗan 'yan daban wannan unguwa da na wata unguwar, wanda mafi yawa kan ritsa da waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Da wuya a iya cewa, ga adadin mutanen da 'yan daba suka jikkata ko suka nakasa ko ma suka kashe tsawon misalin shekara ɗaya a jihar Kano.

fg

Asalin hoton, KIYAWA

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shirin wanda 'yan sanda ke bugun ƙirjin cewa ya cimma nasara mai yawa zuwa yanzu, ya fara ne cikin watan Mayun 2023.

Rundunar ta wallafa sunayen wasu da ta yi zargin cewa riƙaƙƙun 'yan daba ne da mafarauta, inda ta ayyana nemansu ruwa a jallo.

Wasu a ciki babu jimawa, suka miƙa kansu da kansu. Akwai wasu ma, waɗanda babu sunayensu, amma dai suka yi tunanin karɓar tayin zaman lafiya na 'yan sanda inda suka kai kansu, tare da ayyana tuba, tare da rungumar zaman lafiya.

Hakan dai, kamar yadda 'yan sandan Kano suka yi iƙirari, ta janyo raguwar hare-haren 'yan daba a kan mutanen gari.

"Babban abin da na sanya gaba shi ne tabbatar da tsaro da kuma aminci a faɗin jihar Kano", in ji Kwamishinan 'yan sandan Kano, Mohammed Usaini Gumel.

Amma har yanzu akwai wasu riƙaƙƙun 'yan daba da rundunar ke ci gaba da nema, saboda sun ƙi rungumar shirin zaman lafiyar.

"Muna ci gaba da neman wasu yara biyu ruwa a jallo, mun sanya ladan kuɗi ga duk wanda ya iya kawo su.

Za mu ba da tukwicin N500,000 a kan kowanne ɗaya daga cikinsu."

Me zai faru bayan ajiye makamai

fg

Asalin hoton, KIYAWA

Da yawan waɗannan 'yan daba ba a tursasa musu ba, suka ajiye makamansu, kamar yadda kwamishinan ya jaddada.

Tsare-tsaren 'yan sanda suka ɓullo da su na janyo 'yan daban da suka tuba a jiki, na cikin abubuwan da ke jan hankulansu wajen rungumar shirin.

'Yan sanda sun ce sun riƙa gudanar da maƙalolin wayar da kai ga waɗanda suka tuba, ta yadda za su ƙauracewa muggan tunani, da shan ƙwaya, da ke kai su ga aikata miyagun laifuka.

Sun ce suna gwada misali da wasu tsoffin riƙaƙƙun 'yan daba, waɗanda ƙarshen rayuwarsu bai yi kyau ba, wajen tausar zukatan matasan game da buƙatar ajiye makamai da zama mutane nagari.

Rundunar 'yan sanda ta kuma ce ta riƙa shirya wasannin ƙwallon ƙafa na sada zumunta don nishaɗantar da tubabbun matasan da hana su zaman kashe wando.

Haka kuma, 'yan sanda sun riƙa amfani da wannan dama wajen gabatar da tubabbun ga al'ummomin unguwanninsu da suka uzzurawa, inda sukan nemi afuwarsu tare da bayyana musu cewa da gaske za su koma zaman lafiya da kowa.

fg

Asalin hoton, KIYAWA

Rundunar 'yan sandan Kano ta kuma ce tana bai wa tubabbun 'yan daba damar yin aiki tare da kuma sauraren ƙorafe-ƙorafensu a ko da yaushe.

Ana zargin 'yan siyasa da hannu wajen rura wutar tarzomar 'yan daba a Kano, inda ake amfani da su a matsayin 'yan bangar siyasa don far wa abokan hamayya.