Shekarar 2022 a cikin hotuna

Wasu zaɓaɓɓun hotuna masu ƙarfi da kamfanonin dillancin ɗaukar hotuna suka tattaro a faɗin duniya na wasu abubuwan da suka faru a shekarar 2022.

A woman from the Kirat community wearing traditional attire dances during the Sakela festival in Kathmandu, Nepal, 1 January 2022.

Asalin hoton, Rojan Shrestha/NurPhoto/Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata daga al'ummar Kirat sanye da kayan al'adar yankin tana rawa a yayin bikin al'ada na Sakela da aka yi a Kathmandu da ke Nepal.
Aerial view of cars and rubble after the Rio das Velhas overflowed on 12 January 2022 in Honorio Bicalho, Brazil.

Asalin hoton, Pedro Vilela / Getty Images

Bayanan hoto, Yadda zaftarewar ƙsa da ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya jawo nsuka kashe a kalla mutum 15 a kudu maso gabashin Brazil. Fiye da mutum 28,000 ne suka bar muhallansu a jihar Minas Gerais, inda koguna suka tumbatsa har suka cinye garuruwa.
Two people scream while dancing, as protests against coronavirus vaccine mandates continue, in Ottawa, Canada - on 17 February 2022.

Asalin hoton, CARLOS OSORIO / reuters

Bayanan hoto, Mutane sun yi zanga-zangar adawa da allurar riga-kafin cutar korona a kusa da majalisar dokokin Canada a Ottawa. Jihar Ontario ta ayyana dokar ta ɓaci a wani mataki na hana zanga-zangar da direbobin manyan motoci suka shafe sati biyu suna yi.
Fireworks form the Olympic rings during the opening ceremony of the 2022 Beijing Winter Olympic Games at the National Stadium in Beijing, 4 February 2022.

Asalin hoton, Future Publishing / Getty Images

Bayanan hoto, Beijing ya zama birnin na farko da ya ɗauki baƙuncin wasannin gasar Olympic biyu, na lokacin bazara da na hunturu, inda aka buɗe wasannin hunturun a fitaccen filin wasanna nan na Bird Nest, wato mai siffar sheƙar tsuntsaye a babban birnin Chinar.
Will Smith hits Chris Rock during the 94th Academy Awards in Hollywood, Los Angeles, on 27 March 2022.

Asalin hoton, BRIAN SNYDER / Reuters

Bayanan hoto, Will Smith ya wanke Chris Rock da mari a wajen bayar da kyaututtukan karramawa na gasar Oscars a Hollywood da ke Los Angeles, bayan da Rock ya zolayi matar Smith wato Jada Pinkett Smith. Lamarin ya zamo abin da ya mamaye komai a wajen bikin. Daga baya Smith ya bai wa Rock haƙuri, yana mai cewa "zolayar da ya yi din ba mai kyau ba ce kuma ba za a yarda da ita ba."
People cross the river via a makeshift bridge as they flee the frontline town of Irpin, near Kyiv, Ukraine - 7 March 2022.

Asalin hoton, ROMAN PILIPEY/EPA-EFE

Bayanan hoto, Dakarun Rasha sun ƙaddamar da hare-hare kan maƙwabciyarta Ukraine a ƙarshen watan Fabrairu. A nan, wasu fararen hula ne ke tsallake wani kogi ta saman wata gada, yayin da suke tsere wa yaƙin da garin Irpin da ya zama fagen fama, a kusa da babban birnin ƙasar Kyiv.
A man pushes his bike through debris and destroyed military vehicles on a street in Bucha, Ukraine - 6 April 2022.

Asalin hoton, Chris McGrath / Getty Images

Bayanan hoto, A nan wani mutum ne ke tura kekensa a cikin tarkacen kayan yaƙi a Bucha, wani gari da ke wajen birnin Kyiv. A watan Afrilu, ƴan jaridan da suka shiga garin inda ake fafatwa tsakanin dakarun Rasha da na Ukraine - sun ga gawarwakin fararen hula birjik a kan tituna.
A group of Samburu women making traditional Samburu ornaments and jewellery out of beads in Sera Conservancy, Samburu County, Kenya on 10 May, 2022.

Asalin hoton, LUIS TATO / AFP

Bayanan hoto, Matan Samburu suna haɗa jigida da tsakiyoyi da duwatsu a yankin Samburu County. Suna sayar da kayayyakin ga masu yawon buɗe nido inda suke samun kudin kashewa su da iyalansu ta wannan hanyar, musamman a lokacin da suke fama da matsalolin sauyin yanayi.
US actress Kristen Stewart poses during a photocall for the film Crimes Of the Future, at the 75th edition of the Cannes Film Festival in southern France, on 24 May 2022.

Asalin hoton, CHRISTOPHE SIMON / AFP

Bayanan hoto, 'Yar fim Kristen Stewart ta hakince ta ɗauki hoto a yayin bikin fina-finai na Cannes Film Festival a Faransa.
Abortion rights protesters gather at the Utah State Capitol, after the United States Supreme Court ruled in the Dobbs v Women's Health Organization abortion case, overturning the landmark Roe v Wade ruling - 24 June 2022.

Asalin hoton, JIM URQUHART / REUTERS

Bayanan hoto, Masu neman ƴancin zubar da jiki sun taru a majalisar dokoki a jihar Utah a birnin Salt Lake, bayan da Kotun Ƙolin Amurka ta sauya hukuncin Roe v Wade na shekarar 1973, wanda ya halatta zubar da ciki a fadin Amurka.
Migrants from Central and South America are registered by border patrol agents in Roma, Texas, having crossed the Rio Grande river into the United States from Mexico - 13 June 2022.

Asalin hoton, ADREES LATIF / Reuters

Bayanan hoto, Masu kula da kan iyaka a Roma da ke Texas na yi wa ƴan ci rani rijista, bayan da suka tsallake kogin Rio Grande daga Mexico. Ana ci gaba da samun kwararar ƴan ci rani cikin Amurka daga Mexico, inda lamarin har ya fi na shekarar 2021. Fiye da ƴan ci rani 50 ne suka mutu a watan Yuni, a cikin wata babar mota da ta maƙale a kan babban titin Texas: shi ne lamari mafi muni na mutuwar ƴan cira ni da aka taɓa samu a Amurka.
Rescue workers perform CPR on a mother elephant after it fell into a manhole in Khao Yai National Park, Nakhon Nayok province, Thailand, 13 July 2022.

Asalin hoton, TAANRUUAMCHON / Reuters

Bayanan hoto, Masu aikin ceto sun ceto wata giwa da jaririyarta da suka faɗa wani rami a Thailand.
Aymara indigenous women play football during a championship in the Aymara district of Juli in Puno, southern Peru, on 16 July, 2022.

Asalin hoton, CARLOS MAMANI / AFP

Bayanan hoto, Mata ƴan ƙabilar Aymara na wasan ƙallo a gasar zakaru da gundumar Aymara da ke Jli a Puno, a kudancin Peru.
People visit the site of the newly erupted Fagradalsfjall volcano in Meradalir valley, outside the town of Grindavik - on 6 August 2022.

Asalin hoton, Sergei Gapon/Anadolu Agency/Getty Images

Bayanan hoto, Mutane sun yi ta ziyartar yankin da aka samu ruftawa sanadiyar aman wutar dutse na Fagradalsfjall a tsaunin Meradalir, a wajen garin Grindavik. Dutsen ya rufta ne ran 3 ga watan Agusta bayan shafe makonni da aka yi ana ƙwarya-ƙwaryar girgizar ƙasa a yankin.
A view of pagodas on Louxingdun Island during a regional drought in Lushan, Jiangxi province, China - 24 August 2022.

Asalin hoton, THOMAS PETER / Reuters

Bayanan hoto, Tsibirin Louxingdun kenan, a yayin da Kogin Poyang ya kai ƙololuwar ƙafewa a yayin wani matsanancin fari a yankin Jiangxi na China.
Pall bearers carry the coffin of Queen Elizabeth II, with the Imperial State Crown resting on top, into St. George's Chapel, Windsor - on 19 September 19, 2022.

Asalin hoton, Jeff J Mitchell / Getty Images

Bayanan hoto, Wannan kuma na ɗauki hoton ne ranar 8 ga Satumba lokacin da aka ɗauki gawar Sarauniya Elizabeth zuwa cikin Majami'ar St. George a Fadar Windsor. Sarauniyar ta rasu tana da shekara 96.
Former Brazilian President and presidential candidate Luiz Inacio Lula da Silva attends a rally in Curitiba, Brazil, 17 September 2022.

Asalin hoton, UESLEI MARCELINO / Reuters

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Brazil kenan Luiz Inacio Lula da Silva lokacin da ya halarci wani gangami a Curitiba a ƙasar yayin zaɓen shugaban ƙasa na 2022, inda ya yi nasara kan abokin hamayyarsa shugaba mai ci Jair Bolsonaro.
A man demands the resignation of Prime Minister Ariel Henry after he put up road barricades during a general strike in Port-au-Prince, Haiti, September 28, 2022.

Asalin hoton, RICHARD PIERRIN / AFP

Bayanan hoto, Manyan jami'ai sun yi kira ga kwantar da hankali bayan shafe kwanaki ana zanga-zangar adawa da gwamnati a Haiti. Masu zanga-zangar sun nemi Firaminista Ariel Henry da ya yi murabus, bayan da ya soke biyan rarar man fetur da gwamnati ke yi, lamarin da ya sa farashin fetur da na dizel ya yi tashin gwauron zabi.
A woman cuts off her hair during a protest against the Iranian government in Istanbul, Turkey. October 2022.

Asalin hoton, dia images / Getty Images

Bayanan hoto, Mata a fadin duniya sun yi zanga-zangar adawa da gwamnatin Iran ta hanyar yanke gashinsu - kamar yadda ake gani ya faru a birnin Santambul. An fara boren ne sakamakon mutuwar wata matashiya Mahsa Amini a hannin jami'an tsaro, bayan kama ta da suka yi bisa zargin ta da laifin ƙin sa hijabi.
A mother cradles her child suffering from severe malnutrition in the ICU of Bay Regional Hospital in Baidoa, Somalia on 9 November 2022

Asalin hoton, GUY PETERSON / AFP

Bayanan hoto, A nan wata uwa ce ke jijjiga danta don rarrashi, wand ake fama da matsananciyar tamowa a wani asibiti da ke Baidoa a Somaliya. Kenya da Somaliya da Habasha na fama da matsanancin fari bayan shafe shekara hudu babu ruwan sama. Shi ne fari mafi muni da aka taɓa samu cikin shekara 40 a yankunan.
Nasa's next-generation Moon rocket, the Space Launch System (SLS) rocket with the Orion crew capsule, lifts off from launch complex 39-B, in Florida, USA, on the unmanned Artemis 1 mission to the moon -16 November 2022.

Asalin hoton, GUY PETERSON / AFP

Bayanan hoto, Hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka Nasa, ta ƙaddamar da wata roka mafi ƙarfi mai suna Artemis 1 a watan Nuwamba. An harba rokar mai fadin mita 100 ne daga Florida, a wani ƙoƙari na zuwa duniyar wata.
A model poses with a creation by Victoire Kouroupe, a local designer and head of "KJV creation", ahead of the first Central African Fashion Week at the Ledger Hotel in Bangui, 17 December 2022.

Asalin hoton, BARBARA DEBOUT / AFP

Bayanan hoto, Nan wata mai tallar kayan ƙwa ce ta sha ado da kayan kaba, gabanin taron kayan ƙawa na Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.
Lionel Messi, of Argentina, celebrates with the World Cup trophy after winning the 2022 final in Qatar - at Lusail Stadium on 18 December 2022.

Asalin hoton, Shaun Botterill / FIFA / Getty Images

Bayanan hoto, Lionel Messi kenan yake murna bayan da ƙasarsa Ajantina ta lashe gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar. Wannan ne karo na farko da ƙasar ta ci gasar tun shekarar 1986 da Diego Maradona ya ci.
People wearing Santa Claus outfits take part in a charity race to raise funds to help vulnerable families bringing up children, in Madrid, Spain - 18 December 2022.

Asalin hoton, ISABEL INFANTES / Reuters

Bayanan hoto, Mutane sanye da kayan fada kirsimas suna wani gangami don tara wa iyalan da ke cikin matsaloli kuɗaɗen tallafi.