'Da za mu yi zaɓe da mun zaɓi zaman lafiya a Dimokuraɗiyyar Kongo'

Musa Bi
Bayanan hoto, Musa Bi ke nan a sansanin Bushagala da ke arewacin Dimokuraɗiyyar Kongo
    • Marubuci, Mercy Juma & Samba Cyuzuzo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Goma & Nairobi

Lokacin da take tsere wa harin mayaƙan ƙungiyar M23 na baya-bayan nan a ƙauyensu da ke gabashin Dimokuraɗiyyar Kongo, Musa Bi ta yi tafiyar kwana bakwai tare da 'ya'yanta shida - dukkansu 'yan ƙasa da shekara tara - har sai da ta kai wani sansanin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

Matar mai shekara 42 na cike da damuwa saboda ba ta san halin da mijinta ke ciki ba da kuma wasu 'ya'yanta biyu, bayan hare-haren 'yan tawayen ya raba su da juna.

Ba ta wani damu da zaɓen shugaban ƙasar da za a yi ranar 20 ga watan Disamba ba - kuma ba za a gudanar da zaɓen ba a yankuna da dama na da ke lardin Arewacin Kivu saboda rikicin.

"M23 sun zo. Suna fafata yaƙi da sojojin gwamnati. Sai muka fara guduwa, amma waɗanda suka kasa guduwa an kashe su," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Bayan sun yi sa'ar tsira, Bi da 'ya'yanta sun dinga yada zango a wasu ƙauyuka har sai da suka kai sansanin Bushagala, inda suka koma kwanciya a filin Allah, wani zubin ma a cikin ruwan sama.

Lokacin da BBC ta haɗu da su, sun shafe kwan shida a sansanin suna jiran hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta yi musu rajista don su samu tanti.

Sai dai kuma mutane sun yi wa hukumar yawa saboda yawan masu gudowa - 700 zuwa 1,000 a kullum. Bi ta ci gaba da jira cikin haƙuri kuma ta dogara da waɗanda aka yi wa rajista don samun abinci - wanda ake yi da dawa da gero da fulawa.

MDD ta yi ƙiyasin cewa kusan mutum miliyan bakwai ne suke gudun hijira a Dimokuraɗiyyar Kongo, adadi mafi yawa ke nan da aka sani.

A ƙauyen su Bi da ke kusa da garin Masisi, danginta na dogara da kansu ta hanyar noma a gonarsu, har zuwa lokacin da mayaƙan M23 suka kore su.

Mayaƙan, waɗanda da farko tsofaffin sojojin Kongo ne, sun zargi gwamnatin ƙasar da nuna danniya ga 'yan ƙabilar Tutsi marasa rinjaye da kuma ƙin tattaunawa da su. Suna ganin tsaunikan da ke kusa da Masisi a mastayin ƙasarsu ta gado.

Shugaba Félix Tshisekedi, da ke neman wa'adi na biyu na shekara biyar, ya yi ta bayyana 'yan tawayen a matsayin "'yan mamaya" da ke samun goyon bayan Rwanda.

Shugaba Tshisekedi ya yi taron siyasa a ƙarshen makon da ya gabata a birnin Goma, inda aka yi ta zanga-zangar ƙin jinin MDD

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaba Tshisekedi ya yi taron siyasa a ƙarshen makon da ya gabata a birnin Goma, inda aka yi ta zanga-zangar ƙin jinin MDD

"Zan faɗa wa Shugaban Rwanda Paul Kagame cewa: tun da ya fi son ya zama Adolf Hitler ta hanyar yin mamaya, na yi alƙawarin ƙarshensa zai zama kamar na Adolf Hitler," in ji Mista Tshisekedi yayin wani taron yaƙin neman zaɓe ranar Juma'a.

"Amma kuma ya gamu da daidai da shi, wanda zai kafe wajen taka masa birki wajen kare ƙasarsa."

Mista Kagame bai mayar da martani ba, amma wata mai magana da yawun gwamnatin ta ce kalaman "barazana ce ƙarara".

Ficewar dakarun MDD daga gabashin Dimokuraɗiyyar Kongo za ta ɗauki shekaru
Bayanan hoto, Ficewar dakarun MDD daga gabashin Dimokuraɗiyyar Kongo za ta ɗauki shekaru
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaba Tshisekedia ya damu kan yadda aka kasa daƙile mayaƙan na M23, waɗanda suke tazarar kilomita 35 kacal daga Goma, babban birni a gabashin ƙasar da ke mazauna kusan miliyan ɗaya.

Ƙwace ƙauyen su Bi da maƙwabtansa a Masisi - ya sake nuna ƙarfin mayaƙan.

Yayin da sojojin Kongo ba su da ƙarfin da za su iya yaƙarsu su kaɗai ba, shugaban na ganin Sadc a matsayin zaɓinsa kuma ya nemi ƙungiyar ta tallafa masa ganin irin nasarorin da suka samu a baya.

Ƙungiyar mai mamba 16 - ciki har da Afirka ta Kudu, da Angola - ta amince ta tura dakaru duk da cewa babu cikakkun bayanai kuma ba a san lokacin da za su isa ba.

Matakin da shugaban ya ɗauka na neman dakarun MDD su fice daga yankin ya biyo bayan zanga-zangar da aka daɗe ana yi ne a Goma saboda gaza daƙile 'yan tawayen.

Amma wasu mutanen da BBC ta yi magana da su sun ce ficewar tasu za ta jefa su cikin rashin tsaro kwatakwata.

"Duk lokacin da 'yan tawayen suka kawo hari a gidaje da gonakinmu, sansanonin Monusco muke guduwa don samun mafaka," a cewar Elizabeth Ssebazungu da ke sansanin Shasha mai nisan kilomita 30 daga yammacin Goma.

Sai dai kuma ba za su fice nan take ba kuma za su yi hakan ne rukuni-rukuni, ƙila a cikin shekaru masu yawa.

A watan Janairu mai zuwa sojojin Pakistan za su fara barin Kudancin Kivu, abin da zai ɗauki wata huɗu.

Masu tserewa zuwa sansanin Bushagala sun kai 700 zuwa 1,000 a kowace rana
Bayanan hoto, Masu tserewa zuwa sansanin Bushagala sun kai 700 zuwa 1,000 a kowace rana

Wannan ne abin da da yawa daga cikin mazauna yankin ba su sani ba, musamman yadda 'yan siyasa ke ci gaba da kamfe ɗin ƙin jinin MDD.

A wajen Bi, tana ganin wannan abu a matsayin maras tasiri yayin da aka yi watsi da wahalhalun da suke ciki - duk da alƙawuran zaɓen da aka yi musu.

Sauran 'yan gudun hijira a Bushagala, kamar Uzima Sadro, wanda ya rasa gonarsa kwanan nan saboda M23, sun jaddada irin tunanin Bi.

"Wahalahalund da muke ciki ba sababbi ba ne. Su ne dai suka ƙara ƙamari," in ji shi.

"Da gaske 'yan siyasar nan ba su damu da mu ba kuma ba su iya samar da zaman lafiya ba, kuma abin da muke buƙata ke nan."

Map