Manyan jam’iyyu za su kafa gwamnatin haɗaka a Pakistan

Asalin hoton, GETTY IMAGES
Bayan shafe kwanaki ana tattaunawa, manyan jam’iiyun siyasar Pakistan biyu sun ƙulla yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗaka.
Sanarwar da jam’iyyar Pakistan Muslim League ta tsohon firaiminista, Nawaz Sharif da kuma Pakistan People's Party, PPP, suka fitar ta kawo ƙarshen zaman ɗar-ɗar da aka shafe kwanaki ana yi, bayan da aka kasa samun wanda ya yi nasara a zaɓen ranar takwas ga watan Fabrairu.
Da yake jawabi a wajen wani taron manema labarai, shugaban jam’iyyar Pakistan People's Party, Bilawal Bhutto Zardari ya ce mahaifinsa, Asif Ali Zardari zai zamo ɗan takarar shugaban ƙasa, yayin da Shehbaz Sharif, ƙanin Nawaz, zai nemi kujerar firaiminista.
Jam’iiyun biyu sun ce sun ƙulla haɗaka da wasu ƙanana jam’iiyu 4, kuma yanzu haka su ke da rinjaye a majalisar ƙasar.
Dan takara mai zaman kansa, kuma wanda tsohon firaiminista, Imran Khan ke goya wa baya, shi ne ya samu kujeru mafi rinjaye a zauren majalisar.
Jamiyyar Mr Sharif ce tazo ta biyu, sai kuma PPP a matsayi na uku.
Jam’iyyar Mr Khan ta yi zargin an tafka maguɗin zaɓe domin hana ta samun nasara tun a zagayen farko na zaɓen.
Sai dai gwamnati da kuma hukumar zaɓen ƙasar sun musanta wannan zargi.
Jinkirin da aka samu kafin ƙulla wannan yarjejeniya dai ya haifar da fargaba, a yayin da ƙasar mai mutane miliyan ɗari biyu da arba’in ke fama da matsin tattalin arziki da ya janyo tsadar rayuwa, ga kuma rikici a wasu sassa.
A ranar 29 ga watan Fabrairu za a rantsar da sabuwar majalisar ƙasar.












