Shin siyasar Imran Khan ta kare bayan ɗaure shi a gidan yari?

Imran Khan

Asalin hoton, Reuters

A karo ba biyu cikin 'yan watanni an kama Imran Khan, sai dai a wannan karon martanin da ya biyo bayan kama shin ya sha banban. Ko me ya faru?

Babu wani abu da ya fito karara daga ranar 9 ga watan Mayu zuwa 5 ga watan Agustan bana.

Yayin da aka fuskanci zanga-zanga a kan titunan Peshawar da Karachi tare da gine-gine da jibge sojoji a lokacin da aka kama Imran Khan a karon farko, abin ya banbanta a kamen da aka yi masa ranar Asabar da dare don kuwa babu wani canji da aka gani a Pakistan.

Yanzu haka Mista Khan yana tsare, bayan yanke masa hukuncin shekara uku a gidan yari saboda kin bayyana kudin da ya samu daga siyar da wasu kaya da aka ba shi kyauta.

Hukuncin zai haramta masa tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Kiran da ya yi cewa mutane su fito don yin zanga-zangar lumana bai yi aiki ba kawo yanzu. Ko me ya sa?

Idan ka tambayi ministocin gwamnati za su ce maka jama'a ba su son yin biyayya ga Imran Khan ko jam'iyyarsa ta PTI saboda ba su son alakanta kansu da wadanda suka janyo tashin hankali a baya. Sai dai magoya bayan Mista Khan suna da ra'ayi na daban.

Fiye da shekara daya kenan da alaka ta yi tsami tsakanin Imran Khan da hukumomim siyasa da na sojin Pakistan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana dai ganin cewa hukumomin sun taimaka wajen dora Mista Khan kan mulki kuma ana ganin sun saba ne bayan tafiya ta fara yin nisa.

Yunkurin rage masa karfi?

Tun daga wancan lokacin, maimakon ya jira har lokacin zabe mi zuwa, ya ci gaba da sukar shugabannin sojojin kasar.

Ko a lokacin da aka kai wa ginin sojin hari bayan kama shi cikin watan Mayu, sojojin sun fito karara sun bayyana cewa ba za su daga kafa kan wadanda ke da hannu a kai ba.

Matakin da ya biyo baya ya tarwatsa jam'iyyar Imran Khan.

An kama dubban magoya bayansa kuma wasunsu za su fukanaci shari'a a kotun soji duk da kiraye-kirayen da kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke yi cewa bai kamata a gurfanar da fararen hula a gaban kotun soji ba.

Wasu kafofin yada labaran Pakistan sun shaida mana cewa daga karshen watan Mayu, bayan ganawar masu gidajen talabijin da sojojin, an haramta wa yan jarida kiran sunan Khan ko nuna hotonsa ko kuma wallafa sunansa a jikin jarida.

Haka nan kuma, magoya bayansa da dama sun shaida mana cewa sun daina wallafa labari a kan PTI ko jagoranta a kafar sada zumunta, sun kuma goge wadanda suka wallafa a baya tare da jin tsoron kallon jawabinsa a talabijin saboda tsoron ko wani yana bibiyar su.

Gwamnatin dai ta shaida wa BBC cewa ba ta kama masu zanga-zangar lumana ba.

Sai dai kuma, wakilin BBC ya ga lokacin da 'yan sanda suka tafi da magoya bayan PTI da suka taru a kofar gidan Mista Khan da ke Lahore a ranar Asabar amma babu tabbacin ko kama su suka yi.

Wani da bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa BBC cewa yan sandan sun kama magoya bayan PTI 100.

Ya ce an umarci 'yan sandan su kasance cikin shiri, kuma kada su bari magoya bayan Imran Khan su yi wani taro.

"Ina tunanin martanin da hukumomi suka dauka na tarwatsa magoya bayan Imran Khan ya firgita su, ya kuma tilasata masu saduda," In ji Michael Kugelman, daraktan sashin kudancin Asiyaa na cibiyar nazari ta Wilson Center da ke Washington.

PTI supporters protest

Asalin hoton, EPA

"Ina zaton masoyansa ba su son sake daukar kasada irin wadda suka dauka a ranar 9 ga watan Mayu.

"Daga gefe guda, sojojin sun tsara abin daidai. Sun yi amfani da karfi kuma sun yi nasarar hana yin bore saboda Imran Khan a yankin da yake yana da magoya baya sosai."

Tawagar lauyoyin Imran Khan ta bayyana cewa za ta daukaka kara kan hukuncin daure shi. ta.

Gwajin karfin iko a jama'a da kuri'a

A cikin watannin da suka gabata, lauyoyinsa sun rika samun sassauci daga kotuna ta hanyar jinkirta yanke hukunci a kan shari'arsa.

Babu tabbacin ko za a ci gaba da samun hakan. A cikin watan Mayu kotu ta hana kama Mista Khan amma a wani yanki na daban.

Imran Khan daya ne daga cikin tsoffin shugabannin Pakistan da suka kare suna fuskantar tuhuma a kotu. Ya bi layin irin su Nawaz Sharif da Benazir Bhutto da kuma Pervez Musharraf.

A lokacin da yake firaminista, Mista Khan ya daure abokan hamayyar siyasarsa da dama.

Idan har aka jaddada batun haramta wa Imran Khan tsayawa takara, za a samu ayar tambaya a kan makomar jam'iyyar siyasarsa.

A baya dai Mista Khan ya shaida mana cewa PTI za ta ci gaba da kasancewa ko an zabe shi ko ba a zabe shi ba. Babu dai tabbacin ganin hakan.

Mista Kugelman ya ce: "Babbar tambaya ta gaba ita ce ta yaya sauran shugabannin PTI za su nemi hada kan jama'a da tattara su waje guda?"

"Za su yi kokarin fitar da magoya bayansu don fitowa zanga-zanga ne, za su iya samun nasarar hakan? gwaji ne mai kyau."

PTI jam'iyya ce da aka kafa kan akidar Mista Khan. Hatta tambarin sandar kwallon kirket da ke jikin jam'iyyar wata alama ce ta wasan da Imran Khan ya yi a baya.

Mafi yawan yan siyasar da ke kewaye da Mista Khan a farkon shekarar nan sun riga sun bar jam'iyyar. Wasu kuma da ke goyon bayan jam'iyyar sun shiga boyo don gudun kada a kama su.

Duk wadannan abubuwa dai babu wanda ke nuni da cewa jam'iyyar za ta iya gudanar da gangamin neman zabe kamar yadda ya kamata.