CAF ta sanar da ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar 2025 da 2027

Caf

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Caf, Patrice Motsepe ne ya sanar da kasashen

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Afrika - CAF Patrice Motsepe ya sanar da ƙasashen da za su ɗauki baƙuncin gasar cin kofin ƙwallon Afrika, Afcon a shekara ta 2025 da kuma 2027.

An sanar cewa Moroko ita ce wadda za ta karɓi baƙuncin gasar a 2025.

Wannan ne karo na biyu da za a buga gasar a ƙasar, wadda ta taɓa karɓar baƙuncin ta a shekarar 1988.

Ƙasashe kamar Algeriya da Zambia da Benin da kuma Najeriya ne suka janye wa Moroko.

Har wa yau Moroko ɗin na takarar ɗaukar baƙuncin gasar cin kofin duniya a 2030.

Hukumar ta Caf ta kuma sanar cewa Kenya da Tanzania da kuma Uganda za su haɗa gwiwa domin ɗaukar baƙuncin gasar a shekarar 2027.

Rabon da a buga gasar a gabashin Afrika tun a shekarar 1976 lokacin da Habasha ta dauki bakunci.

A ranar 13 ga watan Janairun 2024 ne za a buga gasar Afcon ta 2023 a ƙasar Ivory Coast.