An sayar da rigunan da Messi ya sa a Gasar Kofin Duniya fam miliyan 6.1

fg

Asalin hoton, Getty Images

An sayar da shida daga cikin rigunan da Messi ya sanya a Gasar Kofin Duniya ta 2022 a kan dala milyan 7.8, kwatankwacin naira biliyan tara a wani gwanjon kaya da aka yi a birnin New York.

Messi ne ya sanya wa Argentina kambu a wasan ƙarshe na gasar da suka buga da Faransa, wanda fenariti ya raba.

Rigunan da aka yi gwanjon sun hada da waɗanda ya sanya a farko da wasan ƙarshe da na daf da kusa da na ƙarshe, da kuma daf da na ƙarshe da biyu daga cikin waɗanda ya sa a wasan rukuni da kuma ta wasan zagayen ‘yan 16.

Rigar da ta fi kowacce tsada a tarihi, ita ce wadda Diego Maradona ya sanya wadda ya ci ƙwallo “da hannu”, inda aka sayar da ita a kan fam miliyan 7.1 a 2022.

Messi wanda ya lashe Ballon d’or sau takwas a tarihi, shi ne ɗan wasan farko a tarihin kofin duniya da ya ci ƙwallo a duka matakan gasar, tun daga matakin rukuni har wasan ƙarshe.

fg

Ya buga duka wasa bakwai da Argentina ta yi a Kofin Duniya na 2022, amma biyu cikin rigunan da ya sa a wasannin rukuni aka yi gwanjonsu.

Bayan Cammy Devlin na Australia ya yi musayar guda ɗaya cikin rigunan da Messi ya sanya a gasar.

Kamfanin Sotheby ya ce “wani ɓangare na kuɗin da aka tara, za a bayar da su tallafi ne ga wata gidauniyar Messi mai taimakawa yara masu fama da rashin lafiya da ke da wuyar magani a asibitocin Barcelona.”