Cutukan da ke yaɗuwa lokacin zafi da dabarun kauce musu

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da yanayin zafin ke tunkaro wasu yankunan Kudu da Hamadar Sahara, akwai sauye-sauye da dama da ake samu na yanayi da irin sauyin da gangar jikin ke fuskanta, lamarin da ke janyo bazuwar wasu cutuka tsakanin al'umma.
Hakan ne ma ya sa hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMET, ta yi gargaɗin cewa sakamakon yanayin tsananin zafi - na maki 41 da aka fuskanta a mafi yawan jihohin arewacin ƙasar, da kuma maki 39 da aka fuskanta a jihohin kudancin ƙasar - zafin zai iya ci gaba da ƙaruwa cikin kwanaki masu zuwa.
Lokacin da zafi ya shigo, yawancin abubuwan na sauyawa, kamar tsarin cin abinci da shan ruwa, wanda kuma hakan ke sanya hatsarin kamuwa da cututtuka masu yawa a wannan lokacin.
Sai dai kamar yadda likitoci suka yi bayani, galibi cututtukan da za a iya ɗauka a lokacin zafin, cutuka ne da za a iya kauce wa kamuwa da su.
Wannan ya sa muka tuntubi masana harkar lafiya don su bayar da shawarawari kan irin cututtukan da ake ɗauka a lokacin da kuma yadda za a iya kauce musu.
Yanayi na zafi na sa gajiya da ƙishirwa, tare da ƙona ruwan jiki. Don haka jiki na buƙatar abincin da abin sha mai sanyi wanda zai sa a maƙutar da ruwan da ke ƙonewa a kuma sami yanayi mai sanyi.
Hukumar NiMET ta yi gargaɗin cewa wannan yanayi na barazana ga kamuwa da cutuka kamar kurajen farankama, da kyanda da kuma ƙurajen zafi.
Sauran matsalolin da za a iya fuskanta sakamakon yanayin zafin sun haɗa da ciwon jiki, zazzaɓi da bushewar leɓɓa da cutukan da ke da alaƙa da numfanshi da sauran cutukan da ke da alaƙa da zafi.
Dakta Balarabe Sulaiman Aminu, wani likita dan salin jihar Kano da ke aiki a Saudiyya, ya ce akwai cututtuka da suka fi yaduwa a lokacin zafin, su ne:
- Zazzabin Maleriya
- Zazzabin Taifod
- Farankama
- Kyanda
- Sankarau
Likitan ya ce wadannan cutukan kan yadu a lokacin zafi sakamakon a lokacin jiki ba ya samun abubuwan da yake bukata.
Zazzabin Maleriya
Maleriya, Zazzabi ne da sauro ke yadawa, kuma shi sauro ya fi samun sake a lokacin zafi, inda yake ci gaba da hayayyafa, sakamkon saken da yake samu.
Galibi a lokacin sanyi sauro kan samu kansa cikin kunci, ta yadda ba ya samun saken da yake bukata.
To idan lokacin zafi ya zo sai ya baza komarsa, inda yake cin karensa babu babbaka, wajen takura wa mutane da cizo, wanda hakan ne kuma ke janyo yaduwar cutar Maleriya.
Farankama
Wannan wata cuta ce da galibi ke kama kananan yara sakamakon zafin da fatar jikinsu ke dauka a lokacin zafi.
Galibi rashin wadatacciyar iska ne ke janyo cutar.
Farankama wasu nau'in kuraje ne masu zafi da ke kama fatar kananan yara, wanda a wasu lokuta ma sukan janyo wa yaran zazzabi.
Sankarau
Sankarau ma wani nau'in cuta ne da ke kama mutane, musamman a lokacin zafi.
Galibi abin da ke haddasa cutar shi ne rashin wadatacciyr iska a cikin dakunan kwanan mutane, kamar yadda likitoci suka yi bayani.
Cuta ce da ke sanya wani sashe na jiki yin ciwo, ko ya sankare sakamakon rashin gudanar iska a cikin jikin dan'adam.
Shawarwari
Hukumar NiMET ta zayyano wasu shawarwari da ta ce za su taimaka wa mutane wajen kula da lafiyarsu musamman a wannan lokaci na zafi.
Cikin wani saƙo da hukumar ta wallafa shafinta na X ta ce waɗannan shawarwarin za su taimaka wa mutane don kauce wa kamuwa da cutuka a lokacin zafi.
Shawarwarin da hukumar ta bayyana sun haɗar da:
- Yawaita shan ruwa
- Fakewa a inuwa
- Amfani da fanka
- sanya tufafi marasa nauyi
- Kauce wa fita tsakar rana
Shi ma Dakta Balarabe Sulaiman Aminu, ya ce yana da kyau mutane su rika kokarin tsaftace unguwanninsu, musamman kwatoci ta yadda ruwa ba zai taru ba, don kauce wa yaduwar sauro.
Haka kuma ya ce akwai bukatar mutane su rika kunna fanko a dakunan kwanansu, ko su rika bude tagogin dakunansu ya yadda iska za ta samu damar shiga dakunan.
Likitan ya kara shawartar mutane da surika yawaita shan ruwa, domin jiki na bukatar ruwa musamman a lokacin zafi.











