Likitar da ke kula da lafiyar mutum 13,000

Asalin hoton, BBC/VIRMA SIMONETTE
Dakta Alena ta kasance likita ɗaya tilo da ta kula da lafiyar mutane sama da 13,000 da ke zaune a tsibirin Diit da ke yankin Agutaya a ƙasar Philippines.
Matashiyar likitar ta kasance mai cike da ƙwarin gwiwwa kan wannan gagarumi aikin nata.
Asibiti mafi kusa da tsibirin na da nisan ɗaruruwan kilomita daga ɗan ƙaramin tsibirin da suke rayuwa.
Dakta Alena ta je tsibirin Diit ne daf da ɓarkewar annobar Corona, inda ta rayu cikin barazanar mutuwa a lokacin da ta dage kan dokar killace mutanen da suka kamu da cutar.
Cutar ta Corona wadda ta zame wa duniya gagarumin bala'i ba ta samu shiga wannan tsibiri da ke ƙasar Philippines ba.
A tsawon zaman da ta yi a tsibirin Dakta Alena ta yi yaƙi da cutattuka tsakanin al'ummar yankin
Ta ce ta je tsibirin Agutaya ne domin ta kawo sauyi, to sai dai ta ce ta ji taƙaicin yadda ta samu tsibirin.
Tsibirin ba waje ne da za ka yi tunanin samun wanda ya kammala karatun fannin lafiya a jami'a ko wata makarantar lafiya ba.
Dakta Alena ta yi karatunta a Manila, babban birnin ƙasar Philippine
Saɓanin abokan karatunta - waɗanda suka tafi Amurka da Australiya da Birtaniya domin neman aiki -Dakta Alena ta sadaukar da rayuwarta wajen shiga wani shirin gwamnatin ƙasar da ya yi sanadiyyar tura ta ɗaya daga cikin wurare mafiya talauci a ƙasar.
'Ɓullar annobar Covid ta ƙara jefa ni a matsala'
Tsibirin na Agutaya na da nisan tafiyar kwana biyu da rabi daga Manila, babban birnin ƙasar.
Wannan ya haɗar da tafiyar jirgi da kuma tafiyar ƙasa ta sa'o'i 15 daga tashar jirgin ruwan Iloili zuwa Cuyo, babban tsibiri mai makwabtaka.
Daga nan kuma sai a hau kwale-kwale na tsawon tafiyar sa'a biyu zuwa tsibirin na Agutaya, kuma sai ka jiƙe charkaf!

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dakta Alena ta samu nasarar tsallakawa tsibirin Agutaya a watan Fabrairun 2020.
"A lokacin da na je, ina da shekara 26, kuma mutanen tsibirin da yawa ba su ɗauke ni a matsayin likita ba'', in ji matashiyar likitar.
''Ba su san cewa ni likita ba ce'', kamar yadda ta bayyana cikin murmushi.
Ta fuskancin ƙalubale na farko a cikin watan da ta je tsibirin a lokacin da annobar Corona ta tilasta wa gwamnatin Philippines sanya dokar kulle, inda duka tsiburan suka kasance ba shiga ba fita.
"Shekarata ta farko ban fuskanci wani babban ƙalubale ba'', in ji ta. "ba mu samu ko da mutum ɗaya da ke ɗauke da cutar a tsibirin ba.
To amma shekarar da ta biyo baya (2021), a lokacin da gwamnati ta sassauta dokar zirga-zirga , al'amura sun sauya, domin kuwa mutane da dama sun riƙa komawa ga iyalansu, a tsibirin.
''Kwatsam! sai muka samu mutanen da ke dawowa daga Manila'', In ji Dakta Alena.
Dakta Alena ta riƙa tilasta wa mutane killace kansu a lokacin da suka koma tsibirin daga Manilla.
Ta ce ''mutane sun riƙa nuna ɓacin ransu game da tsarin kulle da na ɓullo da shi''.
''An riƙa yi mini barazanar kisa saboda ƙaƙaba dokar, wasu mutanen kan yi mini barazanar za su harbe ni'', in ji likitar
Ta fahimci yadda rayuwar mutanen tsibirin ke ciki na hannu baka hannu ƙwarya.
Mutanen tsibirin sun dogara kan kifin da suke kamawa, sukan fita da safe don kamo kifin da za su ci da rana, sannan da maraice su fita don nemo abin da za su ci da daddare.
Likitar wadda ta bar saurayinta a birnin Manila, ana yi mata kallon wata jami'ar gwamnati a tsibirin.
''Akwai ranakun da bana iya aikin komai sai kuka saboda takaici,'' in ji ta.

Asalin hoton, BBC/VIRMA SIMONETTE
Ta ƙara fuskantar wani ƙalubalen a lokacin da riga-kafin cutar corona ya bayyana a shekarar 2021.
"Mun riƙa bi gida-gida a tsibirin domin wayar da kan mutane kan riga-kafin'', in ji Dakta Alena.
Ta ƙara da cewa"Tafiyar sa'a uku ce a kwale-kwale zuwa cibiyar da ake bayar da allurar riga-kafin cutar coronan, don haka mutane da dama sun ƙi zuwa a yi musu allurar''.
'Na sha wahala kafin mutane su fahimce ni'
A kowacce rana akan samu mutanen da za su je cibiyar da dakta Alena ke yin allurar riga-kafin a tsibirin.
Ta riƙa gudanar da tarukan wayar da kan jama'a kan muhimmancin allurar riga-kafin, inda daga baya ta ɗauki wasu mutane da suka riƙa taimaka mata wajen gudanar da allurar riga-kafin.
"Kafin na je tsibirin na ɗauka abu ne mai sauƙi, to amma abubuwa sun riƙa rincaɓe min a lokuta da dama'', in Alena.
Mutanen tsibirin sun yi ta samun cutar hawan jini sakamakon yawan cin busasshen kifi da gishiri.
Ciwon siga kuma ya zama tamkar ruwan-dare sakamakon rashin wadataccen ruwan sha.

Asalin hoton, BBC/VIRMA SIMONETTE
Bayan wucewar annobar Corona, Dakta Alena ta ci gaba da amfani da cibiyar lafiyar wajen lura da masu cutar tarin TB.
Matashiyar likitar ta ce sun samu mutum 45 da ke ɗauke da cutar a shekarar 2022, to amma ta ce ta san akwai masu ɗauke da cutar da yawa da ba a gano ba.
Cutar tarin TB na kashe miliyoyin mutane a duk shekara.
Allurar riga-kafin cutar tare da shan magunguna sun taimaka wajen kawar da cutar daga wasu sassan duniya.
Dakta Alena ta riƙa ziyartar tsoffin ma'aurata har gidajensu domin yi musu gwajin cutar ciwon suga kyauta.

Asalin hoton, BBC/VIRMA SIMONETTE
Dakta Alena ta ziyarci wata mata mai kimanin shekara 40 da ke riƙe da ɗanta a wani wurin taruwar jama'a domin duba lafiyar ɗan nata mai kimanin shekara biyar.
Likitar ta shaida wa matar cewa ta zauna a kan kujera, sanan ta fara duba ɗan nata.
"Yaronki na buƙatar tiyata," in ji likitar. Fuskar uwar yaron ta karye sakamakon jin waɗannan kalamai na matashiyar likitar.
Dakta Alena ta ce''A duk lokacin da na ce musu za a yi musu tiyata, za ka ga tsoro da razana a fuskokinsu, domin tunaninsu shi ne ba ni da maganin da zan ba su da zai warkar musu da cutarsu''.

Asalin hoton, BBC/VIRMA SIMONETTE
Bayan aiki na kusan shekara uku a ƙarshe Dakta Alena ta koma birnin Manila, inda makonni bayan komawarta ta bayyana takaicinta kan yadda ake gudanar da aiki a wasu ma'aikatun lafiyar ƙasar.
Bayan komawarta birnin Manila an ba ta aiki a shalkwatar hukumar lafiya da ke birnin, to amma ta ƙi karɓar aikin.
A maimakon haka ta fara aiki da wata gidauniya ta kungiyoyi masu zaman kansu.
A makon da ya gabata ta sake komawa tsibirin Agutaya a wani ɓangare wani shiri da ƙungiyoyi masu zaman kansu ke gudanarwa.
To amma a wannan karon bulaguran Dakta Alena bai haura kwanaki biyu ba a tsibirin.
Kungiyoyi masu zaman kansu sun shafe gomman shekaru suna aika wa da ƙwararrun likitoci zuwa tsiburai, tare da haɗin gwiwar gwamnati da masu bayar da taimako na duniya.











