Ko Najeriya na buƙatar ƙarin jihohi?

Taswirar Najeriya
Lokacin karatu: Minti 5

Wannan tambayar ce dai a bakunan ƴan Najeriya a yanzu haka tun bayan da kwamitin yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima na zauren majalisar wakilai ya ɓunta cewa akwai buƙatar ƙarin jihohi 31 a ƙasar.

Mataimakin shugaban kwamitin na majalisar wakilai, Benjamin Kalu wanda ya karanta daftarin ya ce ya kamata a ƙirƙiri sabbin jihohi shida ga shiyar arewa maso tsakiya sai huɗu ga arewa maso Gabas, inda ita kuma arewa maso yammaci za ta samu ƙarin guda biyar.

Dangane da shiyyoyin kudancin ƙasar, ɗan majalisar ya ce shiyyar kudu maso kudu za ta samu ƙarin jihohi huɗu sai kuma kudu maso Gabas da za a ƙarawa jihohi biyar yayin da kuma kudu maso yammaci ya kamata ta samu ƙarin jihohi guda bakwai.

Idan dai har majalisar dokokin ƙasar ta amince da wannan shawara, to yawan jihohin Najeriya za su zama 67, fiye da ƙasar Amurka mai 50.

Akwai buƙatar ƙarin jihohi 31 a Najeriya?

'E, akwai buƙata kuma babu buƙata', in ji dakta Bello Maisudan, malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa a jami'ar Bayero da ke Kano inda ya ce amsar wannan tambaya na buƙatar amsar wasu abubuwa guda huɗu:

  • Buƙata: Dole ne sai an dubi cewa shin akwai buƙatar samar da jiha a yankin da ake nema. Misali akan samu buƙatar kafa jiha idan akwai matsalar rikici tsakanin ƙabilu a yanki ko kuma ƙorafin danniya daga babbar ƙabila. Mun ga yadda aka samar da jihohin Bauchi da Nassarawa da wasu jihohin Neja Delta sakamakon irin wannan ƙorafin.
  • Yawan al'umma: Yawan jama'a a jiha shi ma wani abun dubawa ne. Shin jihar da za a yanki wata jiha daga ita tana da yawan jama'a? Sannan ita ma sabuwar jihar da za a samar za ta samu yawan jama'ar da ya dace da jiha? Misali kamar jihar Kano tana da yawan al'umma da yawan ƙananan hukumomi.
  • Girman ƙasa: Ana duba cewa akwai faɗin ƙasa a jihar da za a yanka sannan jihar da za a samar za ta samu isasshiyar ƙasar da za ta dace da jiha?
  • Riƙe kai: Wannan ma shi ne babban abin tambaya a ƙoƙarin ƙirƙirar sabuwar jiha. Shin ko jihar da za a ƙirƙira za ta iya riƙe kanta dangane da tattalin arziƙi? A nan ana duba irin kuɗin shiga da jihar za ta samu a cikin gida ko da babu kuɗin da zai rinƙa zuwa mata daga gwamnatin tarayya.

Dakta Bello ya ce "idan ka dubi halin da jihohi suke a Najeriya dangane da waɗancan abubuwan da na lissafa za ka fahimci cewa babu buƙatar ƙirƙirar sabbin jihohi har 31 domin idan ka duba jihohin 36 da muke da su a yanzu haka nawa suka cika waɗancan sharuɗɗan musamman batun iya riƙe kai ba tare da tallafin gwamnatin tarayya ba?

Ni a ra'ayina idan ma za a ƙirƙiri jihohi ka da su wuce ƙarin guda biyar duba da wasu dalilai na yawan jama'a da kuma ƙorafe-ƙorafen ƙananan ƙabilu na danniya daga manyan ƙabilu." In ji dakta Bello.

Muhimmancin ƙirƙirar sabbin jihohi

Malam Kabiru Sufi da Dakta Bello MaiSudan sun amince cewa ƙirƙirar sabbin jihohi a Najeriya na da alfanu ga ƴan Najeriya kamar haka:

  • Ƙara matso da gwamnati kusa da jama'a ta hanyar bai wa jama'a damar shiga harkokin gwamnati kai tsaye.
  • Bunƙasar tattalin arziƙi sakamakon ci gaban da jihar za ta samu tattalin arziƙin al'ummar jihar ka iya samun bunƙasa.
  • Ƙirƙirar sabbin jihohi ka iya sanya wasu al'ummu samun sauƙin daga danniyar manyan ƙabilu.

Illar ƙirƙirar sabbin jihohi a Najeriya a yanzu

Masanan guda biyu sun ce idan aka dubi halin da ake ciki a Najeriya, za a ga kamar illolin da hakan zai haifar sun fi alfanun yawa. Sun zayyana wasu illoli guda da suka ce za su iya yi wa cigaban Najeriyar tarnaƙi:

  • Kashe-kashen kuɗaɗen gwamnatin tarayya zai ƙaru musamman duba da yadda a yanzu haka wasu jihohin ƙasar ba sa iya riƙe kansu ba tare da kuɗi daga gwamnatin tsakiya ba. "Ya kamata yanzu a duba a ga irin halin da ƙasar take ciki musamman abin da ya shafi tattalin arziƙi da tsaro. Su ya kamata a magance ba batun ƙirƙirar jihohi ba." In ji dakta Bello MaiSudan.
  • Rarrabuwar kai: Za a iya samun yanayin da maimakon a samu sauƙin rikici tsakanin al'ummomin da ke rikici suka nemi a raba su, sai kuma a samu rikici.

Matakan tsarin mulki kafin ƙirƙirar sabbin jihohi

Sashe na takwas tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a 1999, ya gindaya sharuɗɗan da dole a cika su kafin a kai ga ƙirƙirar jihohi ko kuma gyaran iyakoki kamar haka:

  • Buƙatar ƙirƙirar jiha ta samu goyon bayan aƙalla kaso biyu bisa uku na ƴan majalisar dattawa da wakilai da suka fito daga yankin da ke neman jihar, haka kuma sai an samu rinjayen kaso biyu bisa uku na majalisar ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashin yankin da ke son jiha.
  • Dole ne ƙudirin ya samu goyon bayan al'ummar yankin da ke son jiha ta hanyar samun kaso biyu bisa uku na ƙuri'ar jin ra'ayin al'ummar.
  • Sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayin mutane kan ƙudirin ya samu amincewar mafi yawan jihohin ƙasar tare da samun rinjayen majalisun dokokin jihohin ƙasar.
  • Ƙudurin ya samu sahhalewar kaso biyu bisa uku na yawan ƴan majalisun dokokin ƙasar na dattawa da tarayya.

Sabbin jihohin da ake son ƙirƙirowa

Arewa ta Tsakiya

  • Benue Ala daga jihar Benue
  • Okun daga jihar Kogi
  • Okura daga jihar Kogi
  • Confluence daga jihar Kogi
  • Apa-Agba daga jihar Benue
  • Apa daga jihar Benue
  • Abuja daga babban birnin ƙasar

Arewa maso Gabas

  • Amana daga jihar Adamawa
  • Katagum daga jihar Bauchi
  • Savannah daga jihar Borno
  • Muri daga jihar Taraba

Arewa maso Yamma

  • New Kaduna daga jihar Kaduna
  • Gurara daga jihar Kaduna
  • Tiga daga jihar Kano
  • Kainji daga jihar Kebbi
  • Ghari daga jihar Kano

Kudu maso Gabas

  • Etiti daga duka jihohin yankin shida
  • Adada daga jihar Enugu
  • Urashi daga duka jihohin yankin shida
  • Orlu daga jihar duka jihohin yankin shida
  • Aba daga duka jihohin yankin

Kudu maso kudanci

  • Ogoja daga jihar Cross River
  • Warri daga jihar Delta
  • Bori daga jihar Rivers
  • Obolo daga jihohin Rivers da Akwa Ibom

Kudu maso Yamma

  • Toru-ebe daga jihohin Delta da Edo da kuma Ondo
  • Ibadan daga jihar Oyo
  • Lagoon daga jihar Lagos
  • Ijebu daga jihar Ogun
  • Oke-Ogun daga jihohin Ogun da Oyo da kuma Osun
  • Ife-Ijesha daga jihohin Ogun Oyo da kuma Osun