Mutanen da girgizar ƙasa ta kashe a Tibet sun haura 120

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Laura Bicker & Koh Ewe
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Beijing and Singapore
- Lokacin karatu: Minti 4
Aƙalla mutum 126 aka tabbatar da mutuwarsu sannan 130 suka jikkata bayan afkuwar wata girgizar ƙasa a yankin Tibet mai cike da tsaunuka a safiyar yau Talata, a cewar kafofin yaɗa labaran China.
Girgizar ƙasar ta afku da misalin karfe 9 na safe agogon yankin, yana kuma da maki 7.1, a cewar alkaluma da hukumar kula da yanayi ta Amurka ta fitar, lamarin da ya sa jama'a su riƙa kwararowa kan tituna domin neman tsira.
An kuma jiyo ƙarar motsin ƙasa a makwabciya Nepal da wasu sassan Indiya.
Girgizar ƙasa dai ta sha afkuwa a yankin.
Ana ɗaukar Shigatse a matsayin wurin bauta mai muhimmanci a yankin Tibet. Wuri ne da shugaban gargajiya na Panchen Lama, wanda jigo ne a addinin Buddha na Tibet, inda yake biye ma Dalai Lama.
Ɗan yankin Tibet Gedhun Choekyi Niyima wanda ake ɗauka a matsayin Panchen Lama, ya ɓace a China lokacin da yake da shekara shida. Daga nan ne China ta zaɓi wanda zai maye gurbin Panchen Lama a wurinta.
Shugaban addinin Buddha na Tibet ɗin a yanzu Dalai Lama ya tsere zuwa Indiya a 1959 kuma ana ganinsa a matsayin wanda zai ƙwato wa yan Tibet ƴanci waɗanda ke cikin fushi sakamakon iko da yankin da Beijing ke yi.
Mutane da dama na tunanin cewa China za ta zaɓi shugabannin addinin Buddha na Tibet wanda take so, idan wanda yake kai yanzu ya mutu.
Hotunan bidiyo da gidan talbijin na China CCTV ya wallafa, sun nuna yadda gidaje suka lalace da kuma yadda wasu suka rufta, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da duba cikin ɓaraguzai.
Yanayi a lardin Tingri, kusa da wurin da girgizar ƙasar ta afku, ya kai maki 8 na ma'aunin celcius kuma zai sauka zuwa maki 18 zuwa yammacin yau, a cewar hukumar lura da yanayi ta ƙasar China.
An samu katsewar ruwa da wutar lantarki a yankin.
Yankin da ke kusa da tsaunin Everest, wanda shi ne mafi tsawo a duniya, lardin Tingri sanannen wuri ne ga masu son hawa zuwa kololuwar tsaunin.
An soke masu yawon buɗe ido zuwa Tingri domin hawa tsaunin Everest da aka tsara yau Talata, kamar yadda wani jami'in hukumar yawon buɗe ido ya faɗa wa kafofin yaɗa labaran yankin, inda ya ce an rufe ɗaukacin wurin buɗe ido a yankin.
Akwai wasu mutum uku da aka tseratar waɗanda tun da farko suka je buɗe ido a yankin, in ji jami'ai.
Kafofin yaɗa labaran China sun ruwaito cewa girgizar ƙasar ta janyo lalacewar gidaje sama da 1,000.

Asalin hoton, Getty Images
Wani mai bincike a cibiyar kula da afkuwar girgizar ƙasa ta China, Jiang Haikun, ya faɗa wa gidan talbijin na CCTV cewa ko da yake akwai yiwuwar sake samun wata girgizar ƙasa mai maki biyar, "sai dai da wuya a samu girgizar ƙasa mai karfi".
Tun bayan da China ta ayyana Tibet a matsayin yankinta a 1950, ta tsaurara ikonta, ciki har da kafofin yaɗa labaran yankin da kuma hanyoyin samun intanet.
Wani mutum da ke zaune a wani otel a Shigatse, ya faɗa wa kafar yaɗa labaran China Fengmian News cewa ya farka daga barci lokacin da ya ji ƙasa na girgiza. Ya ce daga nan ya ruga ya fita kan titi, inda ya ga jirage masu saukar ungulu na shawagi a sama.
"Ji nake kamar ana ɗaga gadona," in ji shi, inda ya ƙara da cewa daga nan ya san cewa girgizar ƙasa ce saboda Tibet ya fuskanci ƙananan girgizar ƙasa a baya-bayan nan.

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin saman China sun kaddamar da aikin ceto zuwa yankin da abin ya shafa ta hanyar amfani da jirage marasa matuki.
Shugaban China Xi Jinping shi ma ya ba da umarnin kaddamar da aikin ceto domin rage barazanar waɗanda abin zai shafa da kuma sake tsugunar da mazauna yankin da girgizar ƙasa ta shafa.
Yayin da aka ji motsin ƙasa a Nepal, babu wanda ya jikkata zuwa yanzu, kamar yadda wani jami'i a yankin Namche na ƙasar Nepal, kusa da tsaunin Everest ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
A 2015, an samu girgizar ƙasa mai maki 7.8 kusa da Kathmandu, babban birnin Nepal, abin da ya janyo mutuwar kusan mutum 9,000 da jikkata sama da 20,000.












