China ta lafta haraji kan kayan Amurka

Gwamnatin ƙasar China ta sanar da lafta haraji kan kayan da ake shiga da su ƙasar daga Amurka, a matsayin ramuwar gayya kan matakan Trump na ƙara haraji kan kayan da ake shiga da su Amurka daga China.
Matakin ya haɗa da harajin kashi 15% kan makamashin kwal da man gas da ake shigarwa China daga Amurka.
Sai kuma ɓangaren ɗanyen man fetur, da na'urorin noma da motocin a-kori-kura wadanda su kuma China ta dora wa harajin kashi 10%.
Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan matakin shugaban Amurka, Donald Trump na sanya harajin kashi 10% kan kayan China da ake shigarwa Amurka ya fara aiki.
A cikin wasu ƙarin matakan ramuwar gayya da Chinar ta ɗauka kan Amurka, ta sanar da cewa hukumar sanya ido kan kamfanoni ta ƙasar ta ƙaddamar da bincike kan kamfanin intanet na Google.
Hukumar ta ce ana zargin Google da karya ƙa'idojin gogayya tsakanin kamfanoni.
'Za mu kai ƙara'
A cikin sanarwar da ta fitar ta ɗaukar matakan ramuwa, China ta zargi Amurka a ƙarƙashin Donald Trump da karya ƙa'idojin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.
"Gaban-kai da Amurka ta yi ita kaɗai ta lafta haraji ya saɓa ƙa'idojin Hukumar Kasuwaci ta Duniya. Wannan ya saɓa wa yarjeniyoyin kasuwancio da tattalin arziƙi tsakanin China da Amurka."
Trump ya amince ya dakatar da ƙudirin ƙaƙaba wa Canada da Mexico haraji

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaba Donald Trump na Amurka ya amince ya dakatar da aiwatar da harajin kasuwanci kan Canada da Mexico na tsawon wata guda.
Yayin wata tattaunawa ta waya da Mista Trump, Firaiministan Canada ya amince ya ƙara matakan tsaro a iyakokin ƙasarsa da Amurka don daƙile kwararar baƙin haure da kuma fataucin ƙwayar Fentanyl.
Shugaba Trump ya ce ya yi na'am ya kuma samu kwanciyar hankali kan matsayar da suka cimmawa.
Tun farko dai Mista Trump ya cimma yarjejeniya da shugabar Mexico Claudia Sheinbaum wadda ta amince ta ƙara sojoji dubu 10 a iyakar ƙasar ta arewa yayin da Amurka kuma za ta taƙaita shige da ficen makamai zuwa Mexico.
Shugaba Trump dai ya sanar da matakin dakatarwar lokacin da yake magana da ƴanjarida a fadarsa ta White House.
Ya ce "mun yi magana mai ma'ana da Mexico kuma muna da kyakkyawar dangantaka amma dole ne mu dakatar da shigo da ƙwayar Fentanyl ... kuma dole mu hana baƙin haure shiga Amurka".
Kazalika Mista Trump ya tattauna da Firaiministan Canada Justin Trudeau game da ƙarin harajin da aka tsara zai soma aiki a yau.
Darajar hannayen jari a kasuwannin duniya dai ta yi ƙasa tun bayan da Trump ya sanar da matakin sanya harajin sai dai sun farfaɗo bayan sanar da dakatar da ƙudirin.
Wani tsohon ministan harkokin kasuwanci na Mexico, Juan Carlos Baker ya shaida wa BBC cewa sam bai yi mamakin dakatarwar ba.
A cewar shi, "babu shakka lamari ne na maraba, komai yana zuwa da sakamako sannan Mexico ta amince da wasu matakai na yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi inda za ta tura wasu sojojin ƙasarta bakin iyaka. Ina ganin abin da Trump ke so ke nan, samun wata nasara da zai yi tutaya da ita gaban waɗanda suka zaɓe shi".
Da alama wannan fito na fiton da Trump ya yi da manyan aminan kasuwancin Amurka ya yi tasiri duba da yadda ƙasashen Mexico da Canada suka amince su ɗauki matakai na tsaurara tsaro a iyakokinsu da kuma magance fataucin ƙwayar Fentanyl.
Sai dai har yanzu babu haske kan ko Trump zai aiwatar da barazanar da ya yi wa Mexico da Canada da zarar wa'adin wata ɗayan ya cika. Wannan yanayin na rashin tabbas kuma yana ƙara fargabar da ka iya ganin ƴan kasuwa rage yawan dogaro da suke da kasuwannin Amurka.











