Wane tasiri ficewar Amurka daga Hukumar Lafiya ta Duniya za ta yi?

Trump

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 6

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ƙasarsa za ta fice daga jerin ƙasashe mambobin Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, lokacin da ya rattaba hannu kan wasu dokoki.

Masana na yi wa al'amarin kallon wani abu da zai janyo naƙasu ga ƙoƙarin duniya na daƙile waɗansu annoba da ka iya ɓullowa a nan gaba, kamar yadda wakiliyar BBC kan ƙidayar al'umma, Stephanie Hegarty ta rawaito.

Wannan ne karo na biyu da shugaba Trump ya sanar da ficewar Amurkar daga Hukumar Lafiya ta Duniya. A 2020 ma Trump ya sanar da hukumar a lokacin annobar korona cewa ƙasarsa za ta fice daga hukumar, to sai dai bayan ya faɗi zaɓe sai wanda ya gaje shi, Joe Biden ya daƙile faruwar hakan.

Amurka ce dai ƙasar da ta fi kowacce a duniya tallafa wa WHO, inda take bayar da kaso ɗaya cikin biyar na kasafin kuɗin hukumar na kowace shekara, dala biliyan 6.8.

Ƙasashe matalauta da dama sun dogara ne ga hukumar wajen ɗaukar nauyin matsalolin lafiya a ƙasashensu, da suka haɗa da allurar rigakafi. Hakan ne ya sa wakiliyarmu ta ruwaito cewa ficewar Amurkar daga hukumar da tsayar da tallafin da take bai wa WHO ka iya shafar irin waɗannan shirye-shiryen.

Mun yi duba dangane da martanin ƙasashen duniya kan sanarwar ficewar ta Amurka daga WHO.

Wani mai cutar ƙyandar biri a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

Ƙasashen Afirka marasa ƙarfi sun dogara ga WHO

Dorcas Wangira, wakiliyar BBC ta harkar lafiya a Afirka

Masana harkar lafiya a Afirka sun gargaɗi Trump cewa sanarwar tasa ta ficewa daga WHO ka iya mayar da hannun agogo baya dangane da cigaban da aka samu wajen yaƙi da cutuka irin su maleriya da tarin TB da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV a nahiyar Afirka.

A matsayin Amurka na wadda ta fi tallafa wa WHO, ficewarta za ta janyo rage kuɗaden da ake amfani da su wajen yaƙar cutuka da bayar da rigakafi ga ƙasashen na Afirka.

WHO na taka muhimmiyar rawa wajen tunkarar cutuka a Afirka. Cibiyoyin daƙile cutuka masu yaɗuwa na Afirka a 2023 sun samu cutuka a nahiyar har 214 daga 166 ciki har da cutar ƙyandar biri inda ƙasar Afirka ta Tsakiya ta fi zama wadda cutar ta fi ta'azzara a ciki.

A bara Amurka ta haɗa gwiwa da ƙasar Rwanda da Hukumar Lafiyar ta Duniya wajen daƙile ɓarkewar cutar MVD a ƙasar.

An samu ɓarkewar cutuka irin su zazzaɓin dengue da sanƙarau da kwalara a Afirka a bara. Kuma a watan Disamba ne hukumar ta WHO ta sanar da cewa annobar cutar kwalara ta kasance mai wuyar sha'ani.

 Peshawar, Pakistan

Asalin hoton, Getty Images

Amurka ka iya rasa ƙarfin faɗa-a-ji a duniya

Sylvia Chang, wakiliayr BBC a China

Idan Amurka ta fice daga hukumar ta WHo to za a samu gurbi na shugabanci, kuma wani abu ne da zai bai wa China damar baza ƙarfin ikonta ya zuwa sha'anin lafiya a duniya.

China dai ta daɗe tana son ƙara ƙarfin ikonta a al'amuran duniya ciki kuma har da sa hannu a harkar gudanar da Hukumar Lafiya ta Duniya da ta kasance wani abu mai muhimmanci da shugaba Xi Jinping ke son cimma.

Da ma dai China ta riga ta ƙara yawan tallafin da take bai wa WHO sannan ta ƙara samun ƙarfin faɗa a ji a sha'anin lafiya na duniya musamman ma lokacin annobar korona.

Ko a ranar Talatar nan sai da ministan harkokin waje na China, Guo Jiakun ya ce ya kamata a ƙara wa hukumar WHO ƙarfi ba a daƙile ta ba inda ya ƙara tabbatar da goyon bayan China ga cigaban hukumar ta lafiya ta duniya.

Aikin fesa maganin sauro a Sri Lanka

Asalin hoton, Getty Images

Tasirin rage tallafi ga WHO

Ishara Danasekara, BBC News Sinhala

Tallafi daga hukumar lafiya ta duniya na taka rawa wajen daƙile cutuka masu yaɗuwa kamar zazzaɓin dengue da tarin TB a ƙasar Sri Lanka, baya ga daƙile yawan mutuwar mata masu juna biyu da jariransu.

Saboda haka idan tallafin da ake bai wa WHO ya ja baya, ƙasar ta Sri Lanka ka iya fuskantar koma-baya dangane da irin nasororin da aka samu na daƙile cutuka a ƙasar.

Ko a 2004, WHO ta taka rawar gani wajen bai wa Sri Lanka tallafi lokacin annobar Tsunami da kuma 2020 lokacin annobar korona.

Yadda ake yi wa yara rigakafin shan inna a Mumbai, India.

Asalin hoton, Getty Images

Tarhub Asghar, wakilin BBC News Urdu

Ga ƙasashen irin su Pakistan da Afghanistan inda har yanzu ake fama da cutar Polio, yunƙurin Trump na ficewa daga hukumar ta WHO ka iya jefa ƙasashen cikin haɗarin rashin tabbas a nan gaba. Ƙasashen biyu dai su ne na ƙarshe da har yanzu ke fama da cutar shan inna a duniya.

Duk da irin gangamin da aka yi na yaƙi da cutar ta polio a Pakistan, an samu koma-baya inda cutar ta ci gaba da shafar mutane. A 2023 fiye da rabin yaran da suka kamu da cutar ba su samu allurar rigakafi ba kamar yadda ma'aikatar lafiyar ƙasar ta bayyana.

Allurar rigakafin polio a Gaza

Asalin hoton, Getty Images

Rawar WHO a Gabas ta Tsakiya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hanan Razek, daga BBC News Arabic

Wannan sanarwar ta mista Trump dai na zuwa ne a daidai lokacin da yankin Gabas ta Tsakiya ke fama da rikici iri-iri da ya janyo bazuwar cutuka da buƙatar kayan jin-ƙai.

Kusan rabin al'ummar da ke zaune a Gaza, mutum miliyan biyu da dubu ɗari yara ne kuma gano cutar polio a tsakanin yara a watan Yulin 2024 ya janyo damuwa sosai.

Ƙwararru kan harkar lafiya sun alaƙanta ɓarkewa da yaduwar cutar da irin illar da rikicin ya yi wa tsarin lafiya na Gaza da kayan more rayuwa tun 2023.

Har wa yau cutar kwalara a yankin na Gabas ta Tsakiya ita ma wata barazana ce, inda a Syria, a sansanin masu gudun hijra na al-Hol da ke da ƴan hijra fiye da 40,000 da ke fama da ƙarancin tsaftataccen ruwan sha ya janyo ɓarkewar kwalara inda a watan da ya gabata aka samu mutum fiye da 200 sun kamu. Kuma hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayar da tallafi ta hanyar yin rigakafi na kwana 10 domin daƙile bazuwar cutar.

Daga BBC News Parsi

Tasirin da janye hannun Amurka daga WHO zai yi kai tsaye ga fannin lafiyar ƙasar Iran shi ne rashin tabbas, amma kuma zai taimaka wajen samar da sauyi ga tallafin kuɗi da diflomasiyyar sha'anin lafiya da harkokin lafiyar na yankin.

Iran dai ta riƙe alaƙar diflomasiyya da hukumar lafiya ta duniya kuma hukumar na da ofis a babban birnin ƙasar ta Iran wato tehran, inda take aiki tare da hukumar lafiyar ƙasar wajen daƙile wasu ƙalubalai na lafiya a ƙasar da kuma inganta tsarin lafiyar ƙasar. Wannan ƙawance ya mayar da hankali ne kan rigakafi da inganta tsarin lafiya da kuma shirya wa ɓarkewar annoba.

Ƙasashe irin su China ka iya kasancewa wadda za ta maye gurbin Amurkar a harkar lafiya ta duniya da kuma ka iya sauya al'amura a siyasar duniya wani abu da ake ganin zai iya bai wa ƙasar Iran dama ita ma.

Abin da hakan yake nufi shi ne Iran ka iya samun cikakkiyar damar ƙulla aminci da Hukumar ta Lafiya ta Duniya, WHO.