Netanyahu zai gana da Trump kan zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta

Asalin hoton, Reuters
Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, zai zama shugaban wata ƙasa da zai fara haɗuwa da Donald Trump a fadar White House, a karo na biyu na mulkinsa, ranar Talata.
Trump dai ya yi iƙrarin cimma yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza, da ta kawo ƙarshen watanni 15 na yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas.
Kawo yanzu dai yarjejeniyar ta janyo sakin ƴan Isra'ila 13 da ƴan ƙasar Thailand biyar sannan kuma an saki Falasɗnawa 583 daga gidajen yarin Isra'ila.
To sai dai Netanyahu wanda ke fuskantar rikicin siyasa ya sha nanata cewa yarjejeniyar ta wucin-gadi ce saboda Isra'ila na da "yancin sake komawa yaƙar" Hamas inda ya ce kuma za su samu goyon bayan Amurka.

Asalin hoton, EPA
A ranar Litinin, Netanyahu zai gana da jakadan Amurka na musamman na yankin Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff wanda ya zama ɗaya daga cikin masu shiga tsakani inda yake aiki tare da Qatar da Masar.
Idan har an samu daidaituwar al'amaura kamar yadda aka tsara, za a saki waɗanda aka yi garkuwa da su 33 ya zuwa ranar 1 ga watan Maris inda za a saki Falasɗinawa 1,900 da ke gidajen yarin Isra'ila.
Tawagar shugaban ƙasar Amurka na dab da tattaunawa da firaiministan Qatar da jamai'an Masar a wannan makon inda za a tattaunawa yiwuwar aikewa da tawaga daga dukkan ɓangarorin biyu domin soma tattauna yadda za a kai ga zango na biyu na yarjejeniyar.
Trump dai ya fayyace cewa yana son kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya. A ranar Lahadi ya ce tattaunawa dangane da tsagaita wuta na "samun cigaba" kuma an shirya wata babbar ganawa da Netanyahu.











