Pogba zai dawo taka leda bayan rage dakatarwar da aka yi masa

Paul Pogba

Asalin hoton, EPA

Lokacin karatu: Minti 1

An rage hukuncin dakatarwar da aka yanke wa ɗanwasan tsakiyar Faransa Paul Pogba zuwa wata 18 bayan ya samu nasara a ƙarar da ya ɗaukaka a kotun wasanni.

Wasu majiyoyi na kusa da ɗanwasan na Juventus sun shaida wa BBC Sport cewa zai iya komawa atasaye a watan Janairun 2025 kuma zai samu damar komawa taka leda a watan Maris.

Hukumar yaƙi da shan ƙwayoyi masu ƙara kuzari ta Italiya ce ta dakatar da Pogba a watan Fabrairu bayan gwaji ya nuna cewa ƙwayoyin halitta na kuzarin namiji sun yi yawa a cikin jininsa.

Shugaban kotun ta Cas, Matthieu Reeb, ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa an rage dakatarwar zuwa wata 18 tun daga ranar 11 ga watan Satumba.

Tsohon ɗanwasan na Manchester United ya kai ƙarar ga Cas da kansa kuma ya gabatar da hujjoji yayin wani zama a farkon kakar bana.

Tun a baya ya sha faɗa cewa ba zai taɓa shan ƙwayar kuzari "da gangan ba" kuma hukuncin "ba daidai ba ne".

Da a ce ba a rage dakatarwar ba, ba zai sake taka leda ba har sai a 2027, lokacin yana shekara 34 da haihuwa.