Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta bai wa AC Milan aron Kyle Walker
AC Milan ta cimma yarjejeniyar karbar aron kyaftin din Manchester City Kyle Walker zuwa karshen kakar bana.
Yarjejeniyar ta hada da damar sayen dan bayan a bazara idan ya kammala zaman aron.
A yanzu Walker, wanda ya yi wa City wasa 316 ya kuma dauki manyan kofuna 15 da kungiyar zai tafi Italiya domin a gwada koshin lafiyarsa.
Dan wasan mai shekara 34 ya yi wa City wasa na karshe a karawarsu da West Ham ranar 4 ga watan Janairrun nan, inda a lokacin ya gaya wa kociyansa Pep Guardiola yana son jarraba sa'arsa a wata kasa kuma.
Walker ya nuna cewa ya fi son tafiya Italiya maimakon Saudiyya inda tun da farko ake jita-jitar cewa zai je.
Haka kuma ana maganar cewa AC Milan din za ta dauki dan gaban manchester United, Marcus Rashford to amma doka ta kayyade cewa kungiyar za ta iya daukar dan wasa daya ne kawai daga Birtaniya a wannan lokacin na kasuwar 'yan wasa.
A shekara ta 2017 ne dai Walker ya koma man City daga Tottenham a kan fam miliyan 50..
Haka kuma a 2023 ne dan bayan wanda kuma ya yi wa tawagar Ingila wasa 93, ya zama kyaftindin hadin gwiwa na City.