Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da gaske ne an yi yunƙurin kashe Lt. Yerima a Abuja?
Da yammacin ranar Lahadi ne rahotonin yunƙurin kashe Laftanar Ahmed Yerima - matashin sojan da ya yi sa-in-sa da ministan Abuja, Nyesom Wike a makon da ya gabata - suka cika shafukan sada zumunta.
Rahotonnin sun yi iƙirarin cewa wasu matasa ne da ba a san ko su wane ne ba suka yi yunƙurin halaka sojan ruwan a Abuja, babban birnin ƙasar.
Laftanar AM Yerima ya ɗauki hankalin ƴan Najeriya a makon da ya gabata bayan da ya jagoranci tawagar wasu sojoji da suka hana ministan Abuja, shiga wani fili da ya yi zargin ana gina shi ba bisa ƙa'ida ba.
Ministan ya yi zargin cewa ana gina filin ne - wanda ake zargin mallakin tsohon babban hafsan sojin ruwan ƙasar ne - ba bisa ƙa'ida.
Lamarin da ya sa ya yi yunƙurin zuwa da kansa domin hanawa, to amma sai sojan - wanda aka ce an tura su ne domin gadin filin - ya dakatar da shi daga shiga wurin.
Da gaske an yi yunƙurin kashe shi?
Rundunar ƴansandan birnin Abuja, mai alhakin kare samar da tsaro a birnin, ta musanta wannan iƙirari, tana mai cewa iƙirari ba shi da tushe balle makama.
Cikin wata sanarwa da rundunar ƴansandan Najeriya, reshen birnin na Abuja ta fitar ta hannun kakakinta, SP Josephine Adeh, ta ce babu inda aka samu irin wannan iƙirari.
''Rundunar ƴansanda reshen Abuja ta lura da abubuwan da ke yawo a shafukan sada zumunta, da ke zargin an yi yunƙurin kashe Lt. Ahmed Yerima.
"Rundunar na son bayyana wa al'umma cewa ba mu samu wasu bayanai game da iƙirarin da ake yaɗawa ba ɗaukacin yankin Babban Birnin Tarayya,'' in ji SP Josephine Adeh.
Daga nan sai rundunar ta shawarci al'umma su guji yaɗa labaran da ba su da tabbaci a kansu, saboda a cewarta babu abin da hakan ke haifarwa sai tayar da hankula.
Wane ne Laftanar Ahmed Yerima?
Sunansa Laftanar Ahmed Yerima kuma sojan ruwa ne wanda aka haifa a birnin Kaduna kuma ya girma a can da kuma birnin Fatakwal na jihar Rivers, duk da cewa ɗan asalin garin Fune ne da ke jihar Yobe.
A shekarar 2011 ne Ahmed Yarima, mai shekaru 33 da haihuwa ya fara karatu a sashen koyar da aikin jarida a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Wani abokin karatun Yerima ya shaida wa BBC cewa suna yi wa matashin laƙabi da MD.
"Tun a lokacin matashi ne marar tsoro sannan kuma mutum ne mai iya hulɗa da abokan karatunsa."
To amma Yerima ya bar jami'ar Ahmadu Bello bayan shekara ɗaya sakamakon samun gurbi a kwalejin horas da sojoji ta NDA da ke Kaduna a 2012.
Yerima ya fito a matsayin Laftanar na sojan ruwa a shekarar 2017.
A 2018 ne Yerima ya fara atisayen haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa domin yaƙar ta'addanci da ake kira "Exercise Flintlock" a birnin Agadez da ke Jamhuriyar Nijar.