Ta yaya mace za ta mori rayuwar jima'i a shekarun ɗaukewar jinin al'ada?

Jami'an tsaro

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Raguwar sha'awa da bushewar gaba da kuma jin zafi a lokacin saduwa, waɗannan wasu ne daga cikin alamomin da mata ke fuskanta a lokacin da suka daina jinin al'ada.

Da dama cikin mata sauye-sauyen kan fara ne tsawo shekara 10 gabanin daina al'adar, wani lokaci da ake kira alamar kusantar lokacin daina haihuwa.

Suzan mai shekara 40 da ɗoriya da ke zaune a Vancouver a ƙasar Canada - wadda a yanzu haka ke cikin wannan lokaci - ta ce tana jin zafi a lokacin saduwa.

''Har yanzu ina jin sha'awa, amma zafin da nake ji lokacin saduwa ya rage min sha'awar, ban san me ke faruwa ba, kuma na ɗauki tsawon lokaci kafin na ga likita kan batun''.

Yayin da aka samu ƙaruwar ƙiyasin shekarun rayuwa (life expectancy), mata kan kwashe shekaru masu yawa bayan ɗaukewar jinin al'ada.

Lokacin tsayawar jinin al'ada, shi ne lokacin da mace ke daina ganin al'adarta, sakamakon raguwar sinadarai a jikinta.

Wannan ne lokacin da mace za ta daina haihuwa, kuma mataki ne da ke zuwa da sauye-sauye masu yawa a jiki da kuma ƙwaƙwalwarta.

Dakta Aziza Sesay, ƙwararriyar likita kuma mai rajin wayar da kan mata a Birtaniya, ta ce abin da ke janyo zafi lokacin saduwa ga matan da suka daina al'ada shi ne bushewar gabansu da ake samu sakamakon raguwar sinadarin oestrogen a jikinta.

A mafi yawan al'adu matsalolin saduwa abu ne da mata ba su iya fitowa su yi magana a kai.

''Amma akwai matan da suka ɗauka cewa jin zafi a lokacin saduwa ba wata matsala ba ce, kuma alhaki ne da rataya a wuyanmu mu mata mu jure wannan zafi domin faranta wa mazajenmu'', in ji Dakta Aziza.

Ta ƙara da cewa saboda wannan amanna da muka yi, ya sa mata da dama ba su zuwa gareta da waɗannan matsaloli, ''sun gwammace su ci gaba da shan wahalar ba tare da sun yi magana ba''.

Sinadarai da ɓoyayyun alamomin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Oestrogen wani sinadari da ke haifar da sha'awa ga mata, tare da taimakon sinadarin testosterone da ke cikin ƙwayayen mace.

Idan waɗannan sinadarai suka fara raguwa, to mata za su fara fuskanatar raguwar sha'awa.

Rosie mai shekara 45 da ke zaune a Jamus, wadda aka yi wa tiyatar cire mahaifa tun lokacin tana da shekara 30 sakamakon cutar kansa, lamarin da ya tilasta mata dakatar daina al'ada.

Ta shaida wa BBC cewa sannu a hankali ta riƙa ganin sauye-sauyen a jikinta. ''A baya ina jin daɗin jima'i, amma daga baya na daina, ba na jin wani sauyi a jikina.''

Dakta Nazanin Maali, likitar nazarin tunanin ɗan'adam kuma mai bayar da shawarwari ga marasa lafiya a Carlifonia, ta ce a lokuta da dama mata da suka daina al'ada saboda matsalolin rashin sha'awa da jin zafi a lokacin saduwa.

"A lokuta da dama, ba su jin sha'awa. Akwai mata da dama da ke son yin jima'in, amma kuma babu sha'awar'', in ji ta.

Amma kuma ba bushewar gaba, ko raguwar sha'awa ne ke mata rashin son jima'i a wannan mataki na rayuwarsu ba.

Ga Yas mai shekara 49 da ke zaune a Birtaniya, matsalolin mafitsara ne suka haifar mata da rashin sha'awa jima'i.

Ta shaida wa BBC cewa ''Na daina sha'awar jima'i ne saboda a duk lokacin da na yi shi wasu lalurorin mafitsara ne ke biyo baya.''

Ta ce likitoci sun dauki lokaci kafin su gano cewa matsalarta na da alaƙa da lokacin daina al'ada.

Dakta Sesay ta ce matsalolin mafitsara na daga cikin abubuwan da raguwar sinadarin oestrogen ke haifarwa.

"Mutane kan ɗauka cewa sinadarin oestrogen, na da alaƙa ne kaɗai ga al'ada da kuma haihuwa, amma sinadarin ya wuce nan abu ne da ya shafi duka sauran sassan jiki, kama daga gashin kai har zuwa fatarmu.''

''Sinadarin Oestrogen shi ne jika gaban mace da mafitsararta, don haka raguwar sinadarin zai sa tosar da ke mafitsara ta bushe, lamarin da ke iya haddasa lalurori a mafitsarar'', in ji ta.

A wasu al'adu da dama, ana alaƙanta jima'i da haihuwa, don haka ake samun kuskuren fahimtar cewa jima'i ya ƙare ga matan da suka daina al'ada.

Dakta Maali ta ƙara da cewa martaba mata saboda ƙarancin shekarunsu zai sa idan suka isa wannan mataki su sha wahala, ''musamman ga matan da ke fargabar zuwa wannan mataki.''

To amma ta ce akwai wata da take dubawa da ta faɗa mata cewa ''bayan daina al'adar ne ta fara jin daɗin jima'i''.

Wata mace ke shafa wani man da ke ɗauke da sinadarai a fatarta.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai magungunan da ake amfani da su na domin ƙara wa jikin sinadarai.

Me ya kamata a yi don magance matsalolin?

A cewar Dakta Maali ''matsalolin da ake fuskanta a lokacin daina al'ada, na da magani, na likitanci da wanda ba na likitanci ba, da za su taimaka wa mata ci gaba da yin jima'i cikn jin daɗi.''

Haldita mai shekara 68 da ke zaune a London ta ce ta fara jin daɗin jima'i ne a lokacin da ta daina al'ada.

Ta shaida wa BBC "Na fara ganin alamomin daina ala'ada a lokacin da nake shekara 45/46, kuma na fara jin daɗin saduwa tun daga wannan lokacin.''

Dakta Maali ta ce abin da ya kamata mata su riƙa yi shi ne nazarin yanayin jima'insu.

''Dukkanmu akwai abin da muka ɗaka saduwa, da kuma yadda muke jin daɗinsa, amma idan jikinmu ya fara fuskantar sauye-sauye, yana da kyau mu sauya tunanin mu kan abin da muka ɗauka jin daɗin saduwa, ki tambayi kanki mene ne daɗin saduwa a gareki?''

Ta bayar da shawarar rungumar wasu hanyoyin tayar da sha'awar a lokacin da aka so jima'in.

"Sauyin da ake samu a tsokar da ke gaban mace na rage motsawar sha'awa, don haka ɓullo da wasu hanyoyin kamar amfani da wasu na'urori da ke tayar da sha'awa zai taimaka''.

Amma idan alamomin tyawara al'ada sun rage miki sha'awa, dakta Aziza ta bayar da shawarar ''neman taimakon likitoci, in ma da buƙata ki sauya likita, ka da ki saduda, kuma kada ki ji kunya.''

Dakta Sesay ta ce akwai hanyoyi masu yawa da ake amfani da su wajen inganta sinadaran ko ma sauya su, ciki har da amfani da magunguna kamar ƙwayoyi da mayukan shafawa da sauransu.

Dakta Aziza ta bayar da shawarar sauya ɗabi'un rayuwa ga matan da suka daina al'ada.

''A yawaita motsa jiki, da cin ƴaƴan itatuwa da ganyayyaki, rage ko ma daina shan basara, daina shan taba, da rage nauyi,'' in ji ta.

Babban abu da Dakta Sesay ke kira a yi shi ne kula da kai "Kula da kai ba son kai ba. Ki yi ƙoƙarin cire duk wani abu da zai sanya ki damuwa. Mata da dama kan ɗauki damuwa masu yawa, har ma wadanda ba nata ba, sukan ara su yafa, to ki sani cewa ba abin da hakan zai haifar miki sai illa.''