Cocin Katolika a Kenya ya ƙi karɓar kyautar dala 40,000 daga shugaban ƙasar

Asalin hoton, @NairobiArchdioc
- Marubuci, Basillioh Rukanga
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nairobi
- Lokacin karatu: Minti 3
Cocin Katalika na Kenya ya ƙi amincewa da tallafin dala $40,000 (kusan naira miliyan 67) daga shugaban ƙasar William Ruto.
Ya bayar da gudunmuwar ce domin gina gidan fasto-fasto da kuma kyauta ga mawaƙa na cocin a lokacin da ake ibada ranar Lahadi a cocin na Soweto Catholic Church da ke babban birnin ƙasar Nairobi.
Gudunmuwar ta biyo bayan sukar da malaman cocin suka yi ga ƴansiyasa a wata sanarwa, inda suka bayyana cewa jami'an gwamnati ba su cika alƙawarin da suke ɗauka bayan sun haye karagar mulki.
Coci-coci a ƙasar sun shiga tsaka mai wuya a bana, inda matasa masu zanga-zangar ƙarin haraji suka zarge su da kusanci da ƴansiyasa.
Bayan gudunmuwar da shugaban ƙasar ya bayar, wadda aka riƙa yaɗawa, sai mutanen ƙasar da dama suka fara kira da a mayar masa da kuɗinsa.
Shugaban ƙasar ya bayar da gudunmuwar tsabar kuɗi shillings miliyan 2.5 na Kenya, (kwatankwacin $20,000 wato £16,000), sannan ya yi alƙawarin zai cika sauran kuɗin daga bisani, kuma ya ce zai ba cocin kyautar motar bas.
Babban faston cocin, Philip Anyolo, ya ce za a mayar da tsabar kuɗin saboda "wasu dalilai na kare mutuncin cocin domin gudun kada ƴansiyasa su yi amfani da shi domin cin ribar siyasarsu."
Ya kuma ce ba za su karɓi wasu kyaututtukan ba, ciki har da shillings 200,000 na Kenya wanda gwamnan Nairobi, Johnson Sakaja ya bayar a lokacin taro, wanda a cewar shugaban fastocin, tuni aka mayar masa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Cocin Katolika ba ya amincewa da amfani tarukan ibada domin tara kuɗi da siyasa," in ji Anyolo.
Ya kuma ƙara da cewa irin waɗannan gudunmuwar sun saɓa da ƙa'idar cocin da ma dokokin Kenya.
Alaƙar da ke tsakanin coci-coci da ƴansiyasa - a ƙasar da sama da kashi 80 na mutanenta Kirista ne - ya fara samun tangarɗa.
Shekara uku da suka gabata, manyan coci-coci a ƙasar sun hana ƴansiyasa amfani da su suna yin siyasa domin su bayar da gudunmuwa.
Sai dai ana tunanin har yanzu akwai alaƙar mai kyau - inda matasan masu zanga-zanga suka zargi coci-cocin da kusanci da gwamnati lokacin da ta yi yunƙurin ƙara harajin a farkon wannan shekarar.
Ta hanyar amfani da zanga-zangar kafofin sadarwa da kalmar #OccupyChurch, mutane da dama sun soki coci-coci da ƙin goyon bayansu a lokacin zanga-zangar, wadda mutane da dama suka rasu a sanadiyar yunƙurin ƙara kuɗin haraji.
Sai dai zanga-zangar ta tilasta shugaban ƙasa Ruto ya janye ƙudurin harajin a watan Yuli.
Sannan a makon jiya, a wani taron manyan fastocin Kenya, sun zargi gwamnati ta "yawan faɗi ba cikawa."
A wata sanarwa, ta kuma nuna rashin jin daɗi a kan yawaitar haraji da cin hanci da take haƙƙin ɗan'adam da rashin aikin yi da kuma taɓarɓarewar ɓangaren ilimi da kiwon lafiya.
Sai dai a wani martani da shugaban ƙasa ya mayar, ya yi kira ga malaman cocin, da cewa, "ya kamata mu riƙa bi a hankali wajen fitar da bayanai saboda gudun kada mu aikata abun da muke zargin wasu da aikatawa."
Wani sanata, wanda na kusa ne da gwanatin, Aaron Cheruiyot, shi ma ya zargi cocin da "bayar da bayanai ba daidai ba," sannan ya ƙara da cewa, "dole malaman cocin su guji yaɗa farfaganda da labaran ƙarya."
Yawancin Kiristocin Kenya ƴan ɗarikar Katolika ne - waɗanda aka ƙiyasta sun kai miliyan 10, wato kusan kashi 20 na ƴanƙasar, kamar yadda alƙaluman gwamnatin ƙasar suka nuna.
Sauran Kiristocin ƙasar suna cikin wasu ɗarikun ne, kamar cocin Anglican na Kenya - wanda suma suka goya bayan matakin na cocin Katalokia.
Shugaban cocin Anglican, Archbishop Jackson Ole Sapit ya ce fastocin cocin Katolika sun yi la'akari ne da tunanin mafi yawan mutanen ƙasar.
"Shi kansa kiran sunayen fastocin cocin da watsi da bayyana sanarwar da ba 'daidai ba ce' rashin gaskiya ne," in ji shi.










