Wane ne Sheikh Ibrahim Saleh da ya jagoranci jana'izar Sheikh Ɗahiru Bauchi?

..

Asalin hoton, BBC GRAB

Lokacin karatu: Minti 4

Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayi Sheikh Ɗahiru Bauchi, Naziru Ɗahiru Bauchi, ya shaida wa BBC cewa mahaifin nasu ya bar wasiyya dangane da mutanen da za su yi masa sallah idan ya riga su rasuwa.

''Da ma ya yi wasiyya cewa Sheikh Shariff Ibrahim Saleh, wanda amininsa ne, shi ne zai yi masa sallah, idan kuma ba ya gari Sheikh Isma'il Khalifa ya yi masa sallah," a cewar Naziru.

Amma kasancewar Sheikh Isma'il Khalifa ya riga ya rasu, Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ne ya jagoranci sallar jana'aizar da aka yi wa marigayin bayan sallar Juma'a a garin Bauchi.

Wane ne Sheikh Shariff Saleh?

Sunansa Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Ibn Muhammad Al-Husaini wanda aka haifa a birnin Maiduguri, ranar 12 ga watan Mayu 1938.

Iyaye da kakannin Sheikh Shariff Larabawa ne da suka sauka a wani wuri da Larabawa ko kuma Shuwa Arab suke sauka da ake kira Alfadha'u da ke kusa da Dikwa a birnin Maiduguri.

An haifi Sheikh Sharif Ibrahim Saleh a ranar Asabar, 12 ga watan Mayun 1938 a garin Aredibe, da ke kusa da Dikwa ta Jihar Borno.

Mahaifinsa, shi ne Sheik Muhammad Al-Salih bin Yunus Al-Nawwy, wanda wani babban malami ne da ya yi fice a fagen ilimin addinin Musulunci.

Ilimi

..

Asalin hoton, BBC GRAB

Sheikh Shariff ya shaida wa BBC a shirin Ku San Malamanku a shekarar 2023 cewa ya fara karatu a gaban mahaifinsa a jihar Borno.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Babana shi ne matattarar makaranta kuma malami ne da ke da salsalar ijazar ilimin Alƙur'ani har zuwa manyan sahabban Annabi SAW. Kuma kafin ya rasu ya yi min wasiyya cewa na ci gaba da karatu a wurin abokinsa kuma haka aka yi."

Sheik Ibrahim Saleh ya fara koyon Al-Ƙur'ani mai girma tun yana ɗan ƙaramin yaro, inda a kullum yake tare da mahaifinsa da dare wanda kullum aikinsa shi ne yin nafila cikin dare.

Wannan ne ya sa Malamin ya fara haddace ayoyin Ƙur'ani tun kafin ya shiga makaranta gadan-gadan. Sau da dama ɗaliban da ke karatu a wurin mahaifinsa na yawan mamakin Ibrahim kan irin ƙoƙarinsa da basirarsa sakamakon yadda yake cin su gyara a karatu duk da sun sha gabansa.

Daga shekarun 1944 zuwa 1964 ne malamin ya matsa ƙaimi wajen haddace Ƙur'ani da koyon wasu litattafai da darusa.

Ya kuma fara neman ilimin Ƙur'ani ne tun a cikin gidansu, wanda daga baya ya koma sauran tsangayu inda ya je wurare kamar Tarmuwa da Gulumba da Gide da Maishumari da Maiduguri.

Akwai manyan malamai da dama da suka yaba da ƙoƙarin Sheik Ibrahim Saleh tun yana ƙarami kamar irin su Sheik Ahmad Muhammadul Habib, wanda jika ne ga Sheik Al-Tijani, akwai kuma Sheik Muhammad Mustapha Alawi da Sheik Tijjani Usman da dai sauransu.

Sheik Ibrahim Saleh ya shafe shekara 20 yana neman ilimi a matsayinsa na ɗalibi, kuma ya koyi kusan dukkan karatunsa a Najeriya, amma ba hakan ke nufin duka malamansa ƴan Najeriya ba ne.

Karatun Sheik Ibrahim ya fi ƙarfi a ɓangaren Hadisi da Usulul Fiƙihu da Ilmun Kalam da kuma Tafisiri. Misali, duk wata aya daga cikin Ƙur'ani idan aka ambato ta, malamin zai iya faɗin idan tana da alaƙa da wani hadisi a tattare da ita. Malamin ya kuma yi nisa ƙwarai a karatun Tauhidi da Fiƙihu.

Rubutu da shahara

..

Asalin hoton, BBC GRAB

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya, Sheik Sharif Ibrahim Saleh ya ce ya rubuta litattafai fiye da 400 na addinin Musulunci da hannunsa.

Sheik Sharif Ibrahim Saleh, ya yi karatu a wurare da dama da suka haɗa da Makka da Madina da Masar da Pakistan da sauran su, a wajen manyan malaman Musulunci, ciki har da babban makarancin Ƙur'anin nan Mahmud Khalilul Khusari a Masar.

Sheikh Shariff Saleh shi ne shugaban kwamitin fatawa ta addinin musulunci a Najeriya.

Sheik Sharif ya ce ya fi sha'awar ɓangaren ilimin Ƙur'ani da Hadisi kuma a nan ne ya fi ƙwarewa. Sannan ya haddace Hadisan da suke cikin Bukhari da Muslim da sauran manyan litattafan hadisai.

A cikin hirar, Sheikh ya ce ya kamata malamai su daina hauragiya da zage-zagen juna. "Kamata ya yi su haɗa kai wajen ilimantar da mutane.''

Sheik Ibrahim ya yi aiki da gwamnatoci daban-daban tun daga 1976 musamman gwamnatin tarayya.

Ana yawan saka Sheikh Shariff a duk wani kwamitin addinin Musulunci da zai bayar da shawara kan wasu tsare-tsare da gwamnati ke son ɓullowa da su da suke da muhimmanci ga addini ko kuma waɗanda za su iya jawo matsala.

Ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda gwamnatin Najeriya ke yawan tura wa zuwa ƙasashe a matsayin wakilan gwamnati ko kuma cikin wata tawaga zuwa ƙasashe kamar Saudiyya da Iran da Masar da Turkiyya da Libiya da Moroko da dai sauransu.