Nasarori da ƙalubalen da ke tattare da abotar Trump da Netanyahu

Asalin hoton, Alex Wong/Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun sake zama domin ci gaba da gyara alaƙar da ke tsakaninsu bayan amincewa da tsare-tsaren Amurka guda 20 kan tsagaita wuta a Gaza a ganawar da suka yi ta ranar Litinin.
Trump yaba da ƙoƙarin Netanyahu, inda ya bayyana da shi a matsayin "jarumi", sannan shi kuma ya ce Trump ne "babban abokin da Isra'ila ta taɓa samu a fadar White House."
Shugabannin biyu sun daɗe suna da alaƙa mai kyau, duk da cewa suna samun saɓani a wasu lokuta.
Trump ya sha bayyana cewa shi ne shugaban Amurka da ya fi ƙaunar Amurka, amma masana suna ganin ya fi alaƙa mai kyau da Isra'ila a zangon mulkinsa na farko sama da na yanzu.
Amma duk da haka, Dr H.A. Hellyer na cibiyar masana ta Royal United Services Institute da ke Birtaniya ya ce, "alamu na cewa akwai matsaloli jigbe a alaƙarsu sama da abubuwan da ake gani tamkar nasarori."
1. Alaƙarsu mai kyau a tsakanin 2017–2020
A wa'adin mulkin Trump na farko, alaƙar da ke tsakanin Trump da Netanyahu ta fi kyau, abin da ya taimaka wa shugaban na Isra'ila samun nasarorin siyasa a wancan lokacin.
Shi ma Netanyahu ya sha bayyana cewa Trump ne babban abokin da Isra'ila ta taɓa samu a cikin shugabannin Amurka.
Ga wasu abubuwa da suka faru a tsakankanin:
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
6 ga Disamban 2017 – Aminicewa da Jerusalem a matsayin babban birnin Isra'ila
Trump ya sanar da cewa Amurka ta amince da Jerusalem a matsayin babban birnin ƙasar Isra'ila. Netanyahu ya yaba da matakin a matsayin kafa tarihi, duk da cewa hakan ya haifar da zanga-zanga a Gabas ta Tsakiya.
8 ga Mayun 2018 – Ficewa daga yarjejeniyar nukiliya da Iran
Trump ya fice daga yarjejeniyar nukiliya da Iran, lamarin da Netanyahu ya yaba, har ya ce, "Trump ya yi abin da ya dace."
14 ga Mayun 2018 – Mayar da ofishin jakadancin Amurka Jerusalem
Netanyahu ya yaba da wannan matakin na mayar da ofishin jakadancin ƙasar Jerusalem daga Tel Aviv. Sannan a ranar Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 60 masu zanga-zanga a Gaza.
25 ga Maris na 2019 – Amincewa da ƙwace tuddan Golan da Isra'ila ta yi
Trump ya sanya hannu a dokar amincewa cewa Isra'ila ce ke da Tuddan Golan bayan Isra'ila ta ƙwace tuddan daga sojojin Syria a shekarar 1967, sannan ta mayar da yankin ƙasarta a shekarar 1981, lamarin da ƙasashen duniya suka yi fatali da shi.
15 ga Satumban 2020 – Ayyana yarjejeniyar Abraham Accords
Ƙasashen Isra'ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahrain sun amince a fadar gwamnatin Amurka da yarjejeniyar Abraham domin ƙulla alaƙa mai kyau tsakanin Isra'ila da ƙasashen Larabawa. Daga bisani Morocco da Sudan suka bi sahu.

Asalin hoton, HAIM ZACH / GPO / HANDOUT
2. Saɓani a tsakanin 2020–2021
Shugabannin guda biyu sun fara takun-saƙa ne bayan Joe Biden ya lashe zaɓen shugaban ƙasar a shekarar 2020.
Netanyahu na cikin waɗanda suka fara taya shi murna, lamarin da ya ɓata wa Trump rai.
7 ga Nuwamban 2020 – Taya Biden murnar lashe zaɓe
Netanyahu ya taya Biden murnar samun nasarar lashe zaɓen shugaban Amurka a shafin Twitter cikin awanni kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen.
Disamban 2021 – Takun-saƙar ta fito fili
A wata tattaunawa da ɗanjaridar Isra'ila, Barak Ravid, Trump ya bayyana kasancewar Netanyahu gaba-gaba wajen taya Biden murna a matsayin "kuskure babba."
3. Sake gyara tsakani a 2025

Asalin hoton, Getty Images
Bayan Trump ya koma mulki, sai Netanyahu ya sake kusantarsa domin gyara alaƙa.
Shi ne shugaban ƙasa na farko da ya ziyarci Washington bayan rantsuwar mulki, sannan zuwa yanzu ya sake komawa sau uku, wanda shi ne ziyara mafi yawa da wani shugaba ya kai wa Trump a wa'adinsa na biyu.
Yanzu shugabanin biyu sun ce suna aiki tare ne domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza, da kuma samar da zaman lafiya a yankin baki ɗaya.
"Babu wani wanda yake farin ciki da Netanyahu. Ina tunanin ko a cikin gwamnatin akwai waɗanda ba sa jin daɗin abin da yake yi," in ji Dr. H.A. Hellyer says.
Haka kuma ƙungiyar Make America Great Again (MAGA) da take da matuƙar tasiri a Amurka ta soki yaƙin Isra'ila a Gaza, in ji Hellyer.
"Isra'ila ba wai ci gaba da yaƙin Gaza kawai ta yi ba, ta ma karya yarjejeniyar da aka cimma, ba tare da fuskantar matsala ba. Ta kuma kai hari a ƙasar da ƙawar Amurka ce a nahiyar wato Qatar, kuma ta yi luguden wuta a Lebanon da Syria."
Janairun 2025 – Taya Trump murna
Netanyahu ya taya Trump murnar sake komawa fadar White House, inda ya kira shi a matsayin babban abokin Isra'ila a cikin shugabannin Amurka.
Fabrailun 2025 – Fara tattauna tsagaita wuta a Gaza
Trump da Netanyahu sun gana a karon farko kan batun.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan tsagaita wuta a Gaza da sako waɗanda Hamas ke garkuwa da su da kuma tsarin mayar da waɗanda suka rasa muhallansu.
Afrilun 2025 – Yaƙin Gaza
Trump ya sake ganawa da Netanyahu, inda ya ce akwai buƙatar a dakata da yaƙin Gaza.
Netanyahu ya nanata cewa dole Isra'ila ta ƙwato waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su, sannan ya "gama aikin" da ya fara kan Hamas.
Yunin 2025 – Amurka ta kai hari a Iran
A daren 21 zuwa 22 na watan Yunin 2025, Amurka ta ƙaddamar da hari a cibiyoyin nukiliyar Iran a Fordow da Natanz da Isfahan.
Yulin 2025 – Tsarin Trump na tsagaita wuta a Gaza na kwana 60
Trump da Netanyahu sun sake ganawa a Washington, inda Trump ya gabatar da buƙatarsa ta tsagaita wuta a Gaza ta kwana 60.
9 ga Satumban 2025 – Israel ta kai hari a Qatar
Sojojin Isra'ila sun kai hari a Qatar, inda ta ce ta kai harin ne a kan wasu shugabannin Hamas a ƙasar duk da cewa Qatar ƙawar Amurka ce.
25 ga Satumban 2025 – Layin da Trump ya shata
Trump ya fito fili ya bayyana cewa ba zai bari Isra'ila ta ƙwace Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ba, lamarin da masu tsattsauran ra'ayi a gwamnatin Netanyahu ba su ji daɗi ba.
26 ga Satumban 2025 – Jawabin Netanyahu a MDD
Netanyahu ya sha alwashin "ƙarasa aikin" da ya fara a Gaza a jawabinsa a Majalisar Ɗinkin Duniya, duk da cewa kusan wakilai 100 sun fice a lokacin da yake jawabin.
29 ga Satumban 2025 – Tsare-tsaren Trump na kawo ƙarshen yaƙin Gaza
Ziyarar Netanyahu ta huɗu zuwa White House ita ce wadda suka tattauna tsare-tsaren da Trump ya yi domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Sun ƙunshi sako Isra'ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su da kafa gwamnatin riƙo a Falasɗinu da sauran su.
Haka kuma Netanyahu ya nemi afuwar Firamaninistan Qatar Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim al-Thani kan harin Isra'ila a ƙasarsa.











