Wanne irin wa'azi limamin coci mai sa azumin mutuwa ke yi wa mabiyansa?

Kenyan Pastor

Asalin hoton, YOUTUBE

Bayanan hoto, Fasto Mackenzie sau da yawa na yin wa'azi cikin ƙaraji ga ɗumbin mabiya

Shugaban ƙungiyar Kirista mai ayyuka irin na asiri a Kenya zai bayyana a gaban kotu cikin makon gobe, yayin da ake ci gaba da aikin tono kaburburan haɗaka da aka binne matattu. Aƙalla gawa 90 aka gano zuwa yanzu.

An ba da rahoton cewa Fasto Paul Nthenge Mackenzie ya rufe cocinsa mai suna Good News International Church, shekara huɗu da ta wuce bayan ta shafe kusan shekara ashirin tana aiki.

Sai dai BBC ta bankaɗo ɗaruruwan wa'azozinsa da har yanzu suna nan, ana samun su a intanet, wasu ma ga alama an naɗe su bayan wancan lokaci.

Shin wanne labari suke bayarwa game da mutumin da ke sanya mabiyansa su zauna da yunwa har su mutu?

Cikin wata buɗaɗɗiyar murya mai ingiza zuciya, Fasto Mackenzie yana gabatar da wa'azinsa ga ɗumbin masu ibada da suka yi dandazo don jin bayanansa a kan tashin duniya.

"Mun kusa cin yaƙi… Kada wanda ya waiwaya…. mun kusa kai wa gaɓa," abin da aka rubuta kenan a kan wani ƙyalle da ya ratsa allon bidiyon.

An yi wa wani rukunin bidiyo a tashar cocinsa da ke dandalin Youtube taken: "Yara Lokaci Ya Zo Ƙarshe" inda suke nuna ayarin wasu yara suna gabatar da saƙonni a cikin ƙyamara.

'Babu waiwaye'

Kenyan Pastor

Asalin hoton, YOUTUBE

Bayanan hoto, Ƙarshen duniya da gargaɗi game da aukuwar bala'i su ne suka fi bayyana a wa'azozin Fasto Mackenzie

Waɗansu kuma suna kai wa ga ruƙiyya, inda mabiya - mafi yawansu mata - suke murƙususu a ƙasa lokacin da yake "gana azaba" ga shaiɗanun da suka shiga jikinsu.

Waɗannan tashoshi na YouTube na da dubban masu kallo, kuma wani shafin Facebook da cocin ya kafa na da layukan shiga bidiyo masu yawa.

Babu tabbaci ƙarara a kan ko yaushe aka ɗauki bidiyon wa'azi, sai dai an yi bayani game da wani taron wa'azi da Fasto Mackenzie zai yi a Nairobi cikin watan Janairun 2020, abin da ke cin karo da iƙirarinsa na cewa ya rufe harkar wa'azi shekara ɗaya kafin lokacin.

Idan yara suna kukan yunwa, ku bar su, su mutu'

Tsoffin mabiyan cocin sun yi iƙirarin cewa ana tursasa musu yin azumi, a matsayin wani ɓangare na koyarwar mujami'ar.

Babu shaida kai tsaye a cikin gomman bidiyon da muka gani, Fasto Mackenzie kai tsaye yana umartar mutane su yi azumi.

Sai dai akwai bayanai masu yawa da ke kira ga mabiyan cocinsa, su sadaukar da abin da ransu ya fi so, ciki har da rayuwarsu.

Kenyan Pastor

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dangi na makokin mutanen da aika-aikar ƙungiyar asirin ta ritsa da su a garin Kilifi na gaɓar teku

"Akwai wasu mutane waɗanda ba ma sa so wa'azi (game da) Yesu. Suna cewa 'ya'yansu suna kuka saboda suna jin yunwa, ku bar su su mutu.

Shin akwai wata matsala a nan?"

A wata hira da jaridar Kenyan Nation, 'yan makonnin da suka wuce, Fasto Mackenzie ya musanta cewa yana tursasa mabiyansa yin wa'azi.

"Shin akwai wani gida ko wani kewaye ko kango a wani wuri da aka gano inda mai yiwuwa mutane suke kulle?" Ya ba da amsa lokacin da ɗan jaridan ya tambaye shi game da batun.

'Ilmi mugun abu ne'

Wani take da Fasto Mackenzie ke amfani da shi a wa'azozinsa shi ne batun cewa ilmin boko, shaiɗanci ne kuma ana amfani da shi ne kawai don cin kuɗin mutane.

"Sun san cewa ilmi, mugun abu ne.

Amma suna amfani da shi don cin moriyar kansu" ya faɗa a wani wa'azinsa.

"Waɗanda suke sayar da tufafin makaranta da rubuta litattafai…waɗanda suke yin fensira… da duk wani nau'in tarkace. Suna cin kuɗinmu don su azurta kansu, ku kuma kuna ƙara talaucewa."

A 2017 da kuma a 2018, an kama shi saboda yana ƙarfafa gwiwar yara su daina zuwa makaranta, lokacin da ya riƙa iƙirarin cewa "Littafin Bayibul bai yarda" da ilmin boko ba.

Fasto Mackenzie ya kuma yi Alla-wadai da ilmin boko saboda kare muradan 'yan luwaɗi ta hanyar shirye-shiryen ilmin jima'i.

"Na faɗa muku ilmi, mugun abu ne…. Ana koya wa yara harkar luwaɗi da maɗigo,'' kamar yadda ya faɗa wa jaridar the Nation.

Kenyan Pastor

Asalin hoton, FACEBOOK

Bayanan hoto, Abubuwan da cocin ke wallafawa ta intanet na nuna hotuna da siffofi waɗanda masu tunanin makirci ke yaɗawa

Likitoci bautar 'wani Ubangijin daban suke yi'

Ya kuma riƙa ƙarfafa gwiwar uwaye mata su guji zuwa asibiti a lokacin naƙuda kuma kada su kai 'ya'yansu riga-kafi.

A wani bidiyo, wata mace ta yi bayani kan yadda ta taimaka wajen karɓar haihuwar jariri ta hanyar addu'a, ba tare kuma da an yi tiyata ba. Ta ƙara da cewa daga bisani ta samu wani "saƙo" daga ruhi mai tsarki da ke gargaɗin maƙwabciyarta kada ta yarda ta kai jaririnta allurar riga-kafi.

Limamin cocin daga nan ya yayata maganar cewa ba lallai ne sai an yi wa yara riga-kafi ba, ya yi iƙirarin cewa likitoci "bautar wani Ubangijin suke yi daban".

Ya kuma yi ta ƙarfafa gwiwar mata, su guji yin kitso, da ƙarin gashi da sa yari.

Tamburan shaiɗan da makircin duniya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mafi yawan wa'azozin Fasto Mackenzie na da alaƙa da zuwan maganganun alƙawari da Bayibul ya yi game da Ranar Alƙiyama.

Bayanai da bidiyon da cocin ke yaɗawa a intanet na nuna rubuce-rubuce a kan ƙarshen duniya da aukuwar wani bala'i da ke tafe da kuma haɗurran da ake jin ilmin kimiyya na da shi.

Kuma akwai gargaɗi lokaci-lokaci a kan baƙaƙen iblisai da ake jin cewa sun yi kutse cikin harkar ƙololuwar mulkin duniya.

Ya sha yin nuni da "Sabuwar Alƙiblar Duniya" - wata daw'awar masu tunanin makirci ne cewa akwia wata maƙarƙashiya da wasu manyan duniya ke yi don kawo mulkin kama-karya da zai maye gurbin tsarin ƙasashe - inda cikin iƙirarin ƙarya ya ce Cocin Katolika da Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka na da hannu a ciki.

Yana kuma da matuƙar shakku game da ƙere-ƙeren zamani inda a baya yake iƙirari a kan wani shiri da gwamnatin Kenya ta yi don samar da wata lambar shaidar 'yan ƙasa da za ta ba da damar cin moriyar ayyukan gwamnati, inda ya ce "tambarin dabbobi ne".

Ƙarin rahoto daga Paul Brown da Shayan Sardarizadeh da Jemimah Herd