Brazil ce za ta karɓi baƙuncin gasar Kofin Duniya ta mata a 2027

h

Asalin hoton, GETTY IMAGES

An bayyana sunan kasar Brazil a matsayin wadda za ta karbi bakuncin gasar kofin Duniya ta mata ta 2027, ta samu nasara kan Belgium da Netherland da kuma Jamus da suka nema suma.

Sune kasashe na farko da suka nemi 'yancin samun kuri'un, sai dai Brazil ta samu kuri'a 119 a taron da aka yi a Bangkok a ranar Juma'a.

Wannan ne karon farko da wata kasar kudancin Amurka za ta karbi bakuncin gasar Kofin Duniya na mata.

"Muna taya Brazil murna", in ji shugaban Fifa Giani Infantino.

"Za mu gudanar Kofin Duniya da ya fi kowanne a Brazil. Muna godiya, muna godewa Belgium da Netherland da kuma Jamus da suka nemi daukar nauyin gasar."

Duka wadanda suka nemi daukar nauyin gasar sun cika ka'idojin da aka shimfida, sai dai Brazil ta samu kuri'a a wasu sassa da suka hada da filayen wasa da wuraren kwana da wuraren kallon kwallo na cikin gari da magoya baya ke kallo da harkokin sufuri kamar yadda rahoton Fifa ya bayyana.

A watan Afrilu ne Amurka da Mexico suka fice daga neman daukar nauyin gasar ta hadin gwiwa, suna cewa za su mayar da hankali kan daukar gasar ta 2031, haka kuma Afrika ta Kudu ta yi a wayan Nuwamban bara.

Brazil ta karbi bakuncin Kofin Duniya na maza a 1950 da kuma 2014.