Brazil za ta fuskanci Uruguay a kwata fainal a Copa America

Copa America

Asalin hoton, Getty Images

Brazil za ta kara da Uruguay a zagayen daf da na kusa da na karshe a Copa America, bayan da ta tashi 1-1 a wasan rukuni da Colombia.

Brazil, mai kofin duniya biyar ta kwan da sanin cewar da zarar ta yi nasara a karawar ta California za ta ja ragamar rukunin, kuma ɗan wasan Barcelona, Raphinha ya fara ci mata ƙwallo a bugun tazara.

To sai dai Colombia, wadda rabon a doke ta tun cikin Fabrairun 2022 ta farke ta hannun ɗan wasan Crystal Palace, Daniel Munoz struck.

Colombia, wadda keda Copa America daya ta kusan kara na biyu a raga, saura minti shida a tashi daga karawar ta hannun Rafael Borre.

Da wannan sakamakon Colombia ce ta daya a rukuni na hudu, wadda za ta fuskanci Panama a quarter finals, ita kuwa Brazil za ta kece raini da Uruguay mai kofi 15.

Ɗan wasan Real Madrid, Vinicius Jr ba zai yi wa Brazil karawar zagayen daf da na kusa da na karshe ba, bayan da ya karɓi katin gargadi a karo na biyu.

A ɗaya sakamakon kuwa Costa Rica ce ta doke Paraguay 2-1, inda Francisco Calvo da kuma Josimar Alcocer suka ci mata ƙwallayen.

To sai dai Costa Rica ta kare a mataki na uku a cikin rukuni, hakan ya sa ta kasa kai bantenta.

Za a fara zagayen daf da na kusa da na karshe ranar Juma'a 5 ga watan Yuli, inda mai rike da Copa America za ta kece raini da Ecuador.