An sassauta dokar taƙaita zirga-zirga a wasu yankuna na Taraba

Asalin hoton, Taraba State Government
An sassauta dokar hana zirga-zirga da aka kafa a garin Karim Lamido da sauran kauyuka fiye da goma a jihar Taraba, da ke arewa maso gabashin Najeriya sakamakon wani rikici da ya barke kan batun mallakar wasu gonakin fadama.
Ana dai zargin rikicin ya yi sanadin asarar rayuka akalla ashirin, da gidaje da dukiyoyi masu dimbin yawa.
An sassauta dokar ce daga karfe shida na safe har zuwa karfe uku na rana, a maimakon dokar hana zirga-zirga dare da rana, wadda aka kafa 'yan kwanakin da suka gabata, a wuraren da rikicin ya shafa a yankin karamar hukumar.
Wannan mataki ya biyo bayan lafawar da kurar tashin-tashinar da ta auku ne.
Iliyasu Idris Kirim, Ajiyan Wurkum, kuma daya daga cikin dattawan yankin na karamar hukumar Karim Lamido, ya shaida wa BBC cewa an sassauta dokarce domin a bawa mutane damar su fita su nemi abinci da sauran kayan bukatun yau da kullum.
Kuma wannan rikici da ya haddasa sanya dokar, ya taso ne a tsakanin mutane makwabta wanda kuma suke zaune tare shekara da shekaru, sannan suna mu'amala sosai har ma akwai auratayya a tsakaninsu, to amma sakamakon batun mallakar fadama wanda saboda harkar noman ranai ya sa ta zama abar so da amfani sosai saboda za a iya samun kudi da ita to shi ne saboda kowa na son ya ga ya mallaki fadamar anan ne rikici ya balle.
Ya ce," Sakamakon wannan rikici an samu asarar rayuka akalla 20, sannan ga asarar dukiya kamar amfanin gona da kuma gidaje, domin an kona gidaje da dama."
Shugabannin al'umma a yankin ma dai sun yi kira ga jama'arsu da su kwantar da hankulansu.
Shugabar karamar hukumar Karim Lamido, Honarabul Virginia Baba Bambur, ta shaida wa BBC cewa, baya ga takaita zirga-zirgar jama'a, an dauki matakai da dama don shawo kan rikicin.
Ta ce," Mun zauna da sarakunan gargajiya da inda muka basu shawarar cewa kowa ya tara matasansa a shaida musu cewa su kwantar da hankalinsu domin babu amfanin tashin hankali don su zauna lafiya."
Shugabar karamar hukumar ta Karim Lamido ta kara da cewa, an kama yara da dama masu sace-sace da sauran ayyukan da ba kyau, kuma suna nan tsare a hannun hukuma.
Jihar Taraba ta yi ƙaurin suna a kan rikice-rikicen ƙabilanci da na addini, da na makiyaya da manoma abin da kan rura wutar zaman gaba da rashin yarda tsakanin ƙabilun da ke zargin juna.














