Wane tasiri haramcin fitar da dabbobi daga Nijar zai yi a Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 4

Masu shirin gudanar da ibadar layya musamman a Najeriya sun fara bayyana fargabarsu kan tashin farashin dabbobin layya, sakamakon matakin da gwamnatin Nijar ta ɗauka na hana fitar da dabbobin zuwa ƙasashen waje.

A makon da ya gabata ne gwamnatin ƙasar ta Nijar ta bayyana matakin haramta fitar da dabbobi zuwa ƙasashen waje.

Cikin sanarwar haramcin da ministan ƙasar, Abdoulaye Seydou ya bayyana, ya ce gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da samar da wadatuwarsu a kasuwannin ƙasar a wani mataki na karya farashin dabbobin gabanin bukukuwan Sallar Layya.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen samar da dabbobin layya, a yankin yammacin Afirka.

Dabbobi ne abu na biyu da Nijar ta fi fitarwa zuwa ƙetare, wanda ya kai kashi 70 cikin 100 na kayan noma da kiwo da ƙasar ke fitarwa.

Haka kuma kiwon dabbobin na daga cikin manyan abubuwan da Nijar ta dogara da shi wajen samun kuɗin shiga, a cewar alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya kan bayanan kasuwancin ƙasashe.

Abin da ya sa masu sharhi ke ganin matakin zai yi tasiri wajen tashin farashin dabbobin layyar a wasu maƙwabtan ƙasashen ciki har da Najeriya.

Waɗanne dabbobi Nijar ke fitarwa?

Aliyu Alkasim Mai'Adua wani ɗan kasuwa ne da ke sana'ar saro dabbobi daga Jamhuriyar Nijar zuwa kasuwar Mai'aduwa da ke jihar Katsina, ya kuma ce suna saro kusan duka nau'in dabbobin da ake amfani da su a layya.

''Duk dabbobin da ake amfani da su wajen layya ana samunsu da yawa daga Nijar'', in ji ɗan kasuwar.

Ya ƙara da cewa dabbobin sun haɗar da:

  • Raguna
  • Tumaki
  • Awaki
  • Shanu
  • Raƙuma

Ta yaya hakan zai shafi farashin dabbobi a Najeriya?

Jamhuriyar Nijar - wadda ke yankin sahara - ita ce kan gaba wajen fitar da dabbobi zuwa Najeriya da Cote D'Ivoire.

Alƙaluman cinikayyar ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya, sun nuna cewa a shekarar 2023 kawai Nijar ta fitar da dabbobin da suka kai na dala miliyan 3.93 zuwa Najeriya.

Ministan kasuwancin ƙasar ya ce gwamnati ta umarci jami'an tsaro su ɗau matakan da suka dace a kai da kuma hukunta duk wanda ya saɓawa sabuwar dokar.

Tuni dai ƴan kasuwa a Najeriya suka fara kokawa kan matakin suna masu cewa hakan zai ƙara tsadar dabbobin a ƙasar a daidai lokacin da ake tunkarar sallar layya.

Suma ƴan Najeriya da dama sun koka game da wannan mataki na gwamnatin Nijar, inda suke fargabar samun mummunan tashin farashin dabbobi gabanin sallar layya.

Aliyu Alƙalsim Mai'aduwa mai sana'ar sayar da dabbobi a kasuwar Mai'Adua da ke jihar Katsina, wanda kuma yake saro dabbobin daga jamhuriyar Nijar, ya shaida wa BBC cewa tuni sun fara ganin tasirin matakin a kasuwa.

"Yanzu haka matakin ya fara aiki, domin kuwa mun je amma ba a bari mun sayo dabbobin ba, akwai wasu da suka sayo amma da suka taho jami'an tsaro suka tare su suka ƙwace dabbobin'', kamar yadda ya shaida wa BBC.

'Yanzu haka farashi ya tashi saboda matakin'

Ɗan kasuwar ya ce a yanzu haka farashin dabbobi tuni ya tashi a Najeriya.

''Kuma na tabbata matakin da Nijar ɗin ta ɗauka ne ya janyo haka, domin yanzu mako guda ta ayyana matakin, amma tuni farashin ya sauya'', in ji shi.

''A baya dabbar da ake sayarwa naira 200,000 yanzu za ta iya kai wa 250,000 ko fiye, haka ta 300,000 za ta iya kai wa 400,000'', in ji shi.

Dangane da yawan dabobin a kasuwanni ɗan kasuwar ya ce tuni aka fara ganin raguwar dabbobin a wasu kasuwannin dabbobin ƙasar.

''Hatta dabbobin da ke shigowa kasuwanni an samu raguwarsu, sakamakon wannan mataki, saboda mutane ba sa saro dabbobi daga Nijar'', in ji shi.

A nasu ɓangaren su ma mahauta da ke sana'ar yanka dabbobi domin sayar da nama a kasuwa, sun ce tuni matakin ya shafe su.

Isa Sadau mai sana'ar sayar da nama a kasuwar Shuwarin da ke jihar Jigawa ya ce matakin ya sa farashin dabbobin da yake yankawa ya tashi, lamarin da ya sa shi ma dole ya ƙara farashin naman da yake sayarwa.

''Dole ta sa sai ka ƙara farashi, wanda kuma zai sa mutane su riƙa kokawa, amma ya za ka yi dole idan kana son ka rufa wa kanka asiri kada ka karye'', in ji shi.

''Ita kasuwar shuwarin ana tara mata dabbobi daga manyan kasuwanni da kuma ƙauyukan da ke kewayenta, amma kaso mafi yawa na dabbobin an fi kawo su ne daga manyan kasuwanni'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa sakamakon matakin yanzu an samu raguwar dabbobin da ake kawo su kasuwar, saboda ƴankasuwa ba sa iya sayo ragunan daga Nijar, domin kawo su kasuwar.