Amfanin nonon raƙumi

Lokacin karatu: Minti 3

Wasu masu iya magana na cewa nonon raƙumi ya zama "farin zinare."

Ana tunanin nonon raƙumi na da muhimmanci sosai ga lafiya, inda ake tunanin yana warkar da cututtuka masu yawa.

A rahotanni da dama da aka fitar, musamman a yankunan da suke da sahara sosai, an gano cewa nonon raƙumi na cikin cimakansu na yau da kullum.

BBC ta zanta da masana waɗanda suka yi nazari kan nonon raƙumi domin sanin amfaninsa ga lafiya.

Sinadaran da ke cikin nonon raƙumi

Kamar yadda bincike ya nuna a wata mujallar nazarin ƙwayoyin halitta, nonon raƙumi na da sinadarin vitamin c sama da nonon shanu kusan ninki uku zuwa biyar.

Kamar yadda binciken ya nuna, "ba tare da sinadarin beta-lactoglobulin, nonon raƙumi zai narke cikin sauƙi a cikin mutanen da suke fama da ciwon ciki da ke da alaƙa da gas."

Haka kuma nonon raƙumi ba shi da maiƙo sosai idan aka kwatanta da nonon shanu.

Nonon raƙumi na ɗauke da sinadaran vitamin B1, da B2 da C. Kuma yana ɗauke da sinadarin vitamin C kusan ninki uku zuwa biyar idan aka kwatanta da nonon shanu, wanda hakan ya sa ya zama cimaka mai muhimmanci a yankunan da suke fama da zafi kuma suke da sahara.

Dr Prashant Panara ya shaida wa BBC cewa, "nonon raƙumi na matuƙar kamaceceniya da nonon mutum. Yana ɗauke da sinadarin vitamin B12 da zinc da calcium da maiƙo mai kyau masu yawan gaske. Nonon ba shi da illa, kuma yana rage cutar sukari."

Dr Prashant Panara ya ƙara da cewa nonon yana da amfani ga mutanen da suke fama da matalolin ciki, musamman ɓangaren narka abinci, "sannan yana taimakon jiki wajen yaƙi da cututtuka da ba jiki kariya."

Dr. Purvi Parekh, wanda masani ne kan cimaka ya bayyana wa BBC cewa, "jiki na da yadda nake amfani da kowane irin nono. Amma shi nonon raƙumi yana ƙara ƙarfin ƙashi da gyara tsufa da sinadarai masu kai saƙo a cikin mutane."

Nonon raƙumi nau'in A2 ne, don haka ba ya ɗauke da sinadarin beta-lactoglobulin, yana da sinadarin vitamin C mai yawa da zinc da sauran sinadarai masu gina jiki, kuma ba shi da maiƙo sosai.

Amfaninsa ga lafiya

Mutanen Bedouin da ke tsibirin Sinai a Masar sun yi amannar cewa nonon raƙumi na magance cututtuka da ke da alaƙa da cikin ciki. Suna da yaƙinin cewa nonon yana kashe ƙwayoyin cuta a jiki.

A wani rahoto da hukumar abinci da noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce likitocin Rasha da Kazakhstan suna ba marasa lafiya da dama nonon raƙumi a matsayin magani. A Indiya, ana amfani da nonon raƙumi domin magance cututtuka irin su tarin TB da borin jini da sauran su.

Haka kuma a wuraren da suka saba da amfani da nonon raƙumi a cikin cimakansu, an gano mutanen yankunan ba su cika kamuwa da cutar sukari ba.