Wane ne Aristotle shahararren masanin falsafa na duniya?

Detail of portrait of the Greek philosopher Aristotle (384-322 BC). Painting by Girolamo Mocetto (1458-1531). The Musée Jacquemart-André , Paris.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Aristotle ya kawo gagarumin sauyi a rayuwar al'ummar duniya , kuma ana ganin tasirinsa a fannonin siyasa da kimiyya da fagen rubuce-rubuce.
Lokacin karatu: Minti 5

Shin a iya cewa Aristotle ne mutumin da ya fi tasiri da aka taɓa gani a doron ƙasa? Wani fitaccen malamin falsafa ɗan Birtaniya, John Sellars na ganin haka.

Ya ce ana iya ganin tasirin masanin falsafar ɗan asalin Girka a fagage da dama da irin yadda ya taimaka da tunaninsa a fannoni daban-daban na rayuwa.

Kama daga fagen siyasa da kimiyya, rubuce-rubuce zuwa tunani da dabaru, ana iya ganin tasirin Aristotle a ko'ina.

Ya yi nazarin ilimin halittun cikin ruwa, wani abu da ya haifar da ilimin 'Biology'.

Ya kuma yi bayanin fannonin tsarin mulki daban-daban, wani abu da ya haifar da ilimin kimiyyar siyasa.

Haka kuma sharhinsa kan iya bayar da labari a cikin waƙoƙi ya taimaka wajen samar da tsarin sinima a yau.

Sannan a fannin tunani, dabarunsa a fannin bayar da hujja ya taimaka a kowane fanni kama daga ilimin falsafa zuwa shekarun fasahar zamani.

Farfesa Sellars na Jamai'ar Royal Holloway, da ke Landan, ya sani cewa maganarsa na da ƙarfi. Amma ya dage cewa tasirin Aristotle ya zarce a yi maganarsa. ''Ya gyara yadda muke tunani'', in ji shi.

Babban iƙirari

A wata muƙala da ya wallafa a mujallar Antigone, Sellars ya yi wani iƙirari da ya ja hankali game da masanin falsafar, in da ya ce: "Aristotle ba kawai babban masanin falsafa ne da ba a taɓa ganin irinsa ba - Shi ne ma mutum mafi muhimmanci da aka taɓa yi a duniya''.

Wannan babban iƙirari ne, kuma wanda ya faɗaɗa a littafinsa mai suna 'Aristotle: Understanding the World's Greatest Philosopher'.

Detail of 'The School of Athens', featuring the Greek philosophers Plato (red robe) and Aristotle (blue robe). Painted by Raphael between 1509 and 1511 (Apostolic Palace, Vatican City).

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, "Plato ne abokina, amma gaskiya ce babbar ƙawata,'' a cewar Aristotle.

"A lokacin da na fara nazarin falsafa, na fahimci cewa Aristotle yana da muhimmanci, amma kamar yana da tsoro," a cewar Sellars . "Duk lokacin da na yi ƙoƙari na karanta rubuce-rubucensa, sai nan da nan abubuwa su ɓace min."

Sai dai bayan lokaci mai tsawo ya fahimci cewa karantar rubuce-rubucen Aristotle na buƙatar haƙuri da juriya. ''Kana buƙatar sanin yadda za ka karanta rubutunsa,'' kamar yadda ya bayyana.

Ya rubuta littafin nasa da nufin taimaka wa masu karatu su san hikimomin Aristotle tare da nuna irin tasirin fitaccen malamin falsafar.

Rayuwar neman ilimi

Aristotle da Socrates da Plato ne suka gina babban fagen ilimin falsafa a duniya.

An haifi Aristotle a arewacin Girka, yana da shekara 18 ya koma Athens inda ya yi karatu a makarantar Plato, ya kuma shafe shekara 20 a matsayin ɗalibi da kuma malami a makarantar.

Duk da girmama Plato, Aristotle ya gina nasa ra'ayoyin. Bayan mutuwar malamin nasa, ya bar Athens zuwa tsibirin Lesbos don karantar yanayi. Ya fice a fannin, inda daga baya aka zaɓe shi a matsayin malamin ɗan sarkin Macedon, wanda ke matsayin yarima mai jiran gado, wato Alexander the Great.

Aristotle. From: Commentarium magnum Averrois in Aristotelis De Anima books, 13th century. Found in the collection of the Bibliothèque Nationale de France.

Asalin hoton, Getty Images

A lokacin da Alexander ya fara mulkinsa, Aristotle ya koma Athens inda ya kafa tasa makarantar, mai suna 'The Lyceum'.

Ya kwashe shekarun ƙarshe na rayuwarsa yana koyarwa, da rubuce-rubuce da bincike kafin rasuwarsa a lokacin yana da shekara 62.

Duk da cewa kaɗan ne daga cikin ayyukansa suka samu wanzuwa, har yanzu suna tasiri, musamman a fagen tunani.

Ƙwararren masanin kimiyya

Ba a ilimin falsafa kawai Aristotle ya yi fice ba, ya kasance ɗaya daga cikin masana ilimin kimiyya na farko-farko.

Da jimawa kafin bayyanar na'urorin microscopes da ilimin halittu, Aristotle ya nazarci halittun duniya, inda ya karkasa dabbobi da tsirrai a wani mataki da ya bayar da damar samar da fagen ilimin biology.

Wasu binciken nasa, daga baya ilimi ya tabbatar da kuskure a cikinsu. Amma Sellars ya ce babbar asarar Aristotle ita ce dabarar da ya bi, yana mai cewa bincike da hujja suke taimaka wa fahimta.

Kuma waɗannan dabaru har yanzu su ne zuciyar kimiyya.

Roman civilization, 1st century AD. Mosaic depicting the School of Athens. From Pompeii, Italy.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Makarantar Lyceum ta Aristotle,ta bayar da leccoci masu yawa ga jama'a kuma a kyauta, saɓanin makarantar Plato.

Gudunmowa a siyasa da rubuce-rubuce

Aristotle ya sanya wasu dabarun ilimi da tunani cikin siyasa

Ya tattara tare da kwatanta kundayen tsarin mulki na birane da ƙasashe daban-daban domin fahimtar dalilin da ya sa wasu ƙasashen suka ci gaba, wasu kuma suka zama koma-baya.

Wannan hanya da aka tsara bisa doron hujja maimakon ra'ayi, ita ce ta bayar da damar samar da ilimin kimiyyar zamantakewa, wato 'social sciences'.

Haka ma tasirinsa a fannin rubuce-rubuce ba zai misaltu ba. Baya ga waƙoƙi ya kuma yi nazarin wasannin girka, tare da karkasa labarai zuwa sassa daban-daban, farko da tsakiya da kuma ƙarshe, wata dabara da masu rubuta littattafai da masu shirya fina-finai na yanzu ke amfani da ita.

Aristotle teaching a student, illustration from a 13th-century Mesopotamian copy of the Kitāb naʿt al-hayawān, attributed to Jabril ibn Bukhtishu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana kallon Aristotle a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka fi tasiri a tarihin falsafal Mulunci.

Masanin dabaru da falsafa

Ayyukan Aristotle a fagen dabaru na ɗaya daga cikin gagarumar gudunmowar da ya bayar.

Ya ɓullo da ƙa'idar cewa kowace magana ka iya zama gaskiya ko ƙarya - abin da a yanzu ake kira 'Law of the Excluded Middle.'

Aristotle ya kuma tunkari manyan tambayoyin rayuwa na: Ta yaya muke rayuwa?

A cikin littafin Ɗa'a na Nicomachean, ya bayar da hujjar cewa mutane na fama a lokacin da suka daidaita hujja da alaƙar zamantakewa da sha'awar ƙoƙƙofi game da hankali.

Rayuwa mai kyau, ita ce inda muke samun iko da kanmu, mu shiga cikin al'ummominmu, don neman ilimi.

Tasirin da ba mu taɓa gani ba

Sellars ya yi imanin cewa fasahohin Aristotle sun zurfafa cikin fasahohin zamani duk da cewa ba za mu iya tantance su duka ba.

"Dabarunsa sun shiga ko'ina," a cewarsa, "amma muna ɗaukarsu yanzu tamkar namu."

Don haka ma iya cewa, Aristotle ne mutumin da ya fi muhimmanci a tarihi?

Sellars ya ce a ƙarshe, ya rage ga mai karatu ya yanke shawara - shin Aristotle babban mai tunani ne kawai, ko kuwa, kamar yadda Sellars yayi jayayya, ɗan'adam mafi mahimmancin tarihi?