Sitta Shawwal ko ramuwa: Wanne ya kamata a fara yi?

Sitta shawwal

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Bayan ƙarewar azumin watan Ramadan akwai wasu azumin nafila masu ɗimbin daraja, wato sitta shawwal.

Akwai hadisi sahihi daga Manzon Allah (S.A.W) da ke cewa ''Wanda duk ya azumci watan Ramadan, sannan ya bi shi da azumin kwana shida ciin watan Shawwal, to za a rubuta masa ladan wanda ya azumci shekara guda''.

Azumi ne mai ɗimbin lada da mutane da dama ke kwaɗaituwa da samunsa.

To sai dai mutane da yawa kan shiga ruɗani, musamman idan sun sha azumin watan Ramadan kan wane ya kamata su fara yi tsakanin rama wanda suka sha ciin Ramadan da kuma Sitta Shawwal.

Kan haka ne BBC ta tattauna da malaman addini domin jin yadda batun yake.

Ra'ayin malamai ya bambanta

Malamai

Asalin hoton, Getty Images

Sheikh Sulaiman Datti, babban limamin masallacin Juma'a a sunna da ke Birnin Kudu a jihar Jigawa ya ce ra'ayoyin malamai sun bambanta dangane da wanda mutum zai fara gabatarawa tsakanin sitta shawalal da kuma ramuwar azumi.

''Akwai masu ganin cewa a fara rama na Ramadan, akwai kuma masu ganin cewa a fara da Sitta Shawwal''.

Kuma ya ce kowane ɓangare suna da hujjojin da suek dogara da shi dangane da matsayin da suka ɗauka.

Masu ganin a fara ramuwa

Wani masallaci

Asalin hoton, Getty Images

Limamin Juma'ar ya ce wasu malaman na ganin cewa ya kamata mutum ya fara rama abin da ake binsa na wajibi kafin gabatar da sitta shawwal, wanda shi sunna ce.

Sheikh Sulaiman Datti ya ce masu wannan ra'ayi suna kafa hujja da hadisin Annabi S.W.A da yake cewa ''bashin Allah shi ya fi cancanta a biya''.

Don haka suke ganin cewa shi Sitta Shawwal ba bashi ba ne, wani ƙarin Lada ne, amma shi ramuwar bashin azumi - da mutum ya ɗauka bisa dalilan da addini ya yarje- wannan wajibi ne a gare shi.

'A iya farawa da Sitta Shawwal'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sheikh Sulaiman Datti ya ce akwai kuma malaman da ke da ra'ayin cewa a iya farawa da azumin Sitta Shawwal daga baya kuma a rama azumi.

''Masu wannan ra'ayi na ganin cewa shi Sitta shawwal na cikin ibadan da ake ce musu 'zawatul asbab', wato ibadu masu sababi, waɗanda wani sababi ne ya kawo su'', a cewar malamin.

''Misali ba don zuwan watan Shawwal ba, da ba za a yi shi ba, ka ga kenan yana da wani ƙayyadajjen lokaci''.

Ya ce don haka masu wannan ra'ayin ke ganin duk ibada mai ƙayyadajjen lokaci, idan an fara yinta daga baya aka yi ramuwa suna ganin ba a yi laifi ba.

''Don haka mafi rinjayen malaman hadisi sun tafi a kan wannan ra'ayi, suna ganin a fara yin sitta Shawwal daga baya a rama azumi'', in ji shi.

Ya ce suna kafa hujja da mashahurin hadisin annabi da ke cewa ''Duk wanda ya azumci watan Ramadan sannan ya bi bayansa da azumi shida na Shawwal to Allah zai rubuta masa ladan azumin shekara guda".

Malamin ya ce a wannan hadisin ba a yi maganar ramuwa ba, don haka malaman da suka ɗauki wannan ra'ayi ke ganin a iya fara Sitta Shawwal daga baya a yi ramuwa.

Limamin Juma'ar ya kuma ce mafi rinjayen malamai sun fi tafya a kan wannan ra'ayi.