'Ba mu yarda da sallah a matsayin ibada ba' - Musulman Baye Fall

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Rukia Bulle
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Komla Dumor Award winner
- Lokacin karatu: Minti 7
A daidai lokacin magariba a ƙauyen Mbacke Kadior, wani ƙauye da ke tsakiyar ƙasar Senegal, amon wake-waken wasu musulmai masu ibadah sanye da kaya masu launuka daban-daban ya karaɗe ko ina.
Mabiyan Baye Fall da suka taru a harabar wani masallaci, suna rangaji inda suke ɗaga murya yayin da suke rera waƙoƙi a lokaci guda.
Sun kunna wuta a bayan fage da ke ƙara haskaka launukan kayan da suke sanye da su.
Suna baza gashin kansu a yayin da suke motsawa, kuma fuskokinsu sun jiƙe da gumi a lokacin da suke gudanar da wannan tsarkakkiyar al'adar da ake kira,"saam fall" - wanda biki ne kuma ibada a dunƙule a wuri guda.
A lokacin da suke gudanar da waɗannan wake-wake da raye-rayen sukan fita cikin hayyacinsu baki ɗaya, kuma za su iya ɗaukar tsawon sa'o'i biyu a cikin wannan yanayi - sukan kuma gudanar da wannan aikin ibada ne sau biyu a cikin mako.
Mabiya Baye Fall, wani rukuni ne na babbar ƙungiyar Mouride ta Senegal, kuma ba su yi kamar kowace ƙungiyar Musulmi ba.
Sun kasance wani ƙaramin kaso ne daga cikin mutane miliyan 17 da ke Senegal, ƙasar da ke da yawan al'ummar musulmi a yammacin Afirka.
Amma yanayin kamanninsu mai ban sha'awa ya sa sun yi fice, kuma wasu na ganin ayyukansu na ibada da al'adunsu sun yi hannun riga da ka'idoji da kuma koyarwar addinin musulunci.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ga mabiyan Baye Fall, gabatar da salloli biyar a rana ko azumi a cikin watan Ramadan, ba su ne hanyoyin nuna imani ba kamar yadda akasarin Musulmai ke yi ba. Amma sun yarda cewa ana tabbatar da imani ne ta hanyar yin aiki tuƙuru da kuma yi wa al'umma hidima. A ganinsu, aljannah ba makoma ba ce kawai amma lada ce ga waɗanda suka duƙufa wurin gudanar da aiki ga al'umma.
Sau da yawa wasu musulmi ba su yi musu kyakkyawar fahimta ba - haka kuma akwai rashin fahimta a yammacin duniya cewa wasu suna shan barasa da tabar wiwi, wanda ba ya cikin tsarinsu.
"Tsarin al'ummar Baye Fall yana mayar da hankali ne kan aiki. Wani nau'in aiki ne na sadaukar da kai, inda aiki da kansa ya zama ibada ga Allah," Maam Samba, shugabar wata ƙungiyar Baye Fall a Mbake Kadior, ta shaida wa BBC.
Suna ganin cewa kowanne aiki - kama daga aikin noma a ƙarƙashin matsanancin zafin rana, ko gina makarantu, ko ƙera kayayyaki - muhimmin aiki ne na ibada. Aiki nau'in ne nuna sadaukar da kai ga Allah yayin da jiki ke motsawa.
A nan ƙauyen Mbacke Kadior ne al'ummar Baye Fall suka yi imanin cewa wanda ya kafa su Ibrahima Fall ya fara ganawa da Cheikh Ahmadou Bamba, wanda a ƙarni na 19 ya kafa ƙungiyar Mouride, wani reshen musulunci na Sufi, wanda ke da matuƙar tasiri a ƙasar Senegal.
An ce Fall ya sadaukar da kansa gaba ɗaya ga hidimar Bamba kuma sau da yawa ya yi watsi da nasa buƙatun, ciki har da cin abinci, da azumi, da addu'a da kuma kula da kansa.
Mabiyansa sun rawaito cewa da shigewar lokaci tufafinsa suka zama kamar tsumma inda aka yi musu faci a wurare daban-daban, wanda ke nuni da irin sadaukarwar da ya yi. Wannan shi ne yadda mazhabar Baye Fall da al'adar suturar da suke sanyawa suka samo asali.
Irin wannan biyayya ga shugaban addini ita ce abin da mabiyansa ke yi a halin yanzu - lamarin da aka fi sani da "ndiguel" - akasarin mabiyan Baye Fall sukan kai ga amfani da kalmar a cikin sunayen 'ƴaƴansu.
Ana iya ganin tasirin aikin Fall a cikin ƙauyen Mbbake Kadior a wani wurin da ake haɗa kaya inda haɗin gwiwa da ƙirƙira ke bunƙasa wurin ɗinka kyawawan tufafi masu ɗauke da faci iri daban-daban.
Mata suna mayar da hankali kan aikin da su ke yi na tsoma yadudduka a cikin rini. Tare da kowane tsome, yaduddukan na ɗaukar launuka daban-daban, sannu a hankali sai su rikiɗe zuwa yadudduka masu launuka masu matuƙar ba da sha'awa.

Mazan kuma, suna ɗaukar yaduddukan da aka rina, suna dinka su cikin riguna waɗanda ke da amfani kuma suna bayyana ainihin yanayin shiga ta asali na mabiyan Baye Fall.
Wurin na cike da mutane ana ta kai-komo yayin da suke haɗa kayayyakin, fasaha da hazaƙar da su ke amfani da su na nuni da irin sadaukarwan da su ke nunawa. Akan rarraba waɗannan kayayyakin zuwa kasuwanni a duk faɗin Senegal, inda suketaimakawa al'ummar wurin ciyar da kansu tare kuma da yaɗa mazhabarsu zuwa wuarer daban-daban.
"Salon tufafin Baye ya fita daban," in ji Mista Samba, wanda mahaifinsa tsohon shehin Baye Fall ne mai daraja, ko kuma marabout kamar yadda ake kiran shugabannin addini a Senegal.
"Tufafin yana nuna alamar haɗin kai - za ku iya zama musulmi kuma ku ci gaba da riƙe al'adunku. Amma ba kowa ba ne ya fahimci hakan. Mun ce idan ba ku iya ɗaukar suka ba, ba za ku iya ci gaba ba."
Yayin da sauran musulmi ke azumi tun daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana a cikin watan Ramadan, Mabiya Baye ne suka sadaukar da kansu wajen shirya abincin buɗe baki da yamma idan aka sha ruwa a masallatai.
Wannan aikin ibada ba a yi masa iyaka da aikin hannu ba kaɗai.
Mabiya Baye Fall sun kafa ƙungiyoyin haɗin gwiwa da kasuwancin zamantakewa, da ƙungiyoyi masu zaman kansu da nufin samar da ci gaba mai ɗorewa a yankunan karkarar Senegal. A ganinsu, aiki ba hanya ce ta neman abin duniya kaɗai ba, amma hanya ce ta tabbatar da imani.
"Muna da makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya da masana'antu don samar da aiki," in ji Mista Samba. "A cikin tsarin rayuwarmu, dole ne a gudanar da ayyuka cikin girmamawa da ƙauna, da kuma kula da yanayi. Ilimin halittu yana ɗaya daga cikin ginshiƙan tsarin ci gabanmu mai ɗorewa."
We want to create more employment - because young people need it here in Senegal"
Sai dai kuma ƙungiyar ta sha suka kan yadda mabiyanta ke bara a kan tituna.
Duk da yake neman kuɗi bai saɓa wa koyarwar mazhabar Baye Fall ba, ana hakan ne da nufin miƙa abun da aka tara zuwa ga shugaban, wanda ya sake rarrabawa don amfanin al'umma baki ɗaya.
Cheikh Senne, tsohon shugaban jami'ar Alioune Diop ne da ke garin Bambey kuma ƙwararre ne kan ƙungiyar Mouride, ya shaida wa BBC cewa "Akwai hakikanin Baye Fall da kuma abin da muke kira 'Baye Faux'- wato Baye Fall na bogi ke nan."
A cikin birane kamar babban birnin ƙasar, Dakar waɗannan "Baye Faux" ɗin sun zama ruwan dare.
"Waɗannan mutane ne masu yin ado irin namu kuma suna bara a kan tituna amma ba sa bayar da gudummawa ga al'umma. Wannan muhimmin lamari ne mai matuƙar cutar da mutuncinmu," in ji Mista Senne.
Tsarin rayuwar mabiyan Baye na aiki tuƙuru da inganta zamatakewar al'umma yana tasiri har a wajen ƙasar Senegal.
Daga cikin mabiyansu akwai Keaton Sawyer Scanlon, Ba'amurkiya da ta shiga wata al'umma bayan wata ziyara da ta kai a shekarar 2019. Tun daga nan aka sanya mata suna Fatima Batouly Bah kuma ta bayyana ganawar da ta yi ta farko da wani marabout a matsayin wani lamari da ya sauya ma ta rayuwa.
Ta shaida wa BBC cewa "kamar wani haske ne ke fitowa daga jikinsa." "Zuciyata ta gane gaskiya. Wannan babban lamari ne na ya sauya mun yadda na ke tunani baki ɗaya."
Ms Bah yanzu tana zaune a cikin al'ummar Baye, tana shiga cikin ayyukansu tare da koyon ɗabi'ar hidimarsu. Tana cikin ƴan ƙasahen waje da ke shiga wannan ƙaramar al'ummar da ke ci gaba da haɓaka wanda kuma suka karɓi koyarwar wannan mazhaba da hannu biyu.
Mabiyan Baye Fall suna taka muhimmiyar rawa a cikin al'ummar Senegal kuma shigarsu cikin ayyukan noma iri-iri na da muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
A kowace shekara suna yin mubaya'a ga shugaban Mouride mai ci a lokacin, wanda aka fi sani da khalifa ko babban marabout, ta hanyar ba da gudummawar kuɗi, ko shanu da amfanin gona ga ƙungiyar don nuna amincinsu.
Har ila yau, suna taka rawa wajen kula da Masallacin Grande da ke birnin Touba na ƙasar Senegal, cibiyar Mouridism - kuma su ne ke da alhakin kula da shi.
A Touba suna aiki a matsayin masu gadi a babban Masallacin Grande a lokacin manyan bukukuwa, kamar ziyarar Magal na shekara-shekara lokacin da dubban ɗaruruwan mutane ke zuwa birnin.
Alal Misali, suna tabbatar da cewa mutane sun sanya irin tufafin da ya dace, suna kuma tabbatar da cewa ba a sayar da ƙwayoyi ba a wurin, suna kuma tabbatar da tsaron khalifan.
"Baye Fall sun kasance masu ba da tabbacin tsaron khalifa da kuma birnin," in ji Mista Senne. "Babu wanda ya kuskura ya aikata ba daidai ba a lokacin da Baye Fall ke kusa."
Duk da rashin amincewar da wasu ke nuna musu, tasirin Baye Fall a fagen al'adu da addini na Senegal na ƙaruwa - ko da yake suna fuskantar ƙalubale wajen daidaita al'ada da zamani.

Asalin hoton, Getty Images
Rashin isassun kayan aiki na kawo musu cikas a gudanar da wasu tsare-tsaren su.
Amma duk da haka manufarsu a bayyane ta ke: tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da aka gina kan tushen gaskiya da hidima, wanda kuma zai iya taimakawa wasu ɗimbin matasa marasa aikin yi a Senegal waɗanda suka yanke ƙauna na samun abin dogaro da kai.
Da yawa daga cikin dubban baƙin haure da ke tsallakawa teku zuwa Turai sun fito ne daga Senegal.
"Muna son mu yi abubuwa da dama," in ji Mista Samba. "Muna son samar da ƙarin ayyukan yi - saboda matasa na buƙatar hakan a nan Senegal.
"Muna buƙatar haɗin gwiwa da gwamnatoci da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Wannan shi ne fatanmu na nan gaba."
A tunanin su, aiki tuƙuru shi ne zai inganta tattalin arziki ya kuma ƙarfafa imanin al'ummar ƙasar.












