Abin da ya sa Hausawan Ghana suka yi 'jinkirin' shiga karatun boko

Lokacin karatu: Minti 5

Karon farko a zaɓen shugaban ƙasar na 2024 a Ghana, manyan ƴan takara biyu a lokacin zaɓen sun fito ne daga arewacin ƙasar, inda nan ne al'ummar Hausawa suka fi yawa.

Kuma dukkanin ƴan takaran biyu na da alaƙa da al'ummar Hausawa ta ƙasar.

Hausawa malaman addini sun je Ghana tun kafin zuwan Turawa, sun kuma samu karɓuwa sosai wajen al'umomin ƙasar da sarakuna da attajirai da dama da suka karɓi addinin Musulunci.

Sai dai duk da cewa Hausawan na da dogon tarihi a ƙasar, wani ɓangare da ake ganin nakasu ne ga gudumawarsu a lamurran ƙasar shi ne rashin ƙarfinsu a harkar karatun boko.

Ko mene ne ya haifar da hakan?

Alhaji Baba Sharif, shugaban gidan rediyon Marhaba FM, ya shaida wa BBC cewa bayan zuwan Turawan mulkin mallaka, sun riƙa buɗe makarantun 'Mishan' domin bai wa yara karatun zamani.

''To sai ya zama kowane Basarake da Attajiri, yana da wani malamain addini da ya yarda da shi wajen neman fatawa ko shawara a kan kowane abu da zai yi'', in ji shi.

''Asalin malaman (addinin Musulunci) a Ghana ƙabila biyu ne: Wangarawa da Hausawa, kuma duk in an zauna da kowane sarki to malaman ne ke rubuta musu, saboda ba su iya karatu da rubutu ba a lokacin''.

To bayan buɗe makaratun 'mishan' da Turawa suka yi, sai ya zama ana koya wa ɗaliban da suka je addinin kiristanci.

''To hakan ne ya sa Hausawa suka guji makarantu, kuma suka riƙa bai wa sarakunan Hausawa shawarar cewa kada su shigar da yaransu makarantun'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa hakan ne ya sa yankin da Musulmai suka fi yawa ya samu koma-baya a fannin ilimin Boko a ƙasar.

''Domin a lokacin da aka buɗe makarantar Boko ta farko a arewacin Ghana, akwai Farfesoshi masu yawa a Yammacin ƙasar, saboda sun jima da yin nisa a karatun Bokon'', in ji shi.

Ya ce an buɗe sakandire ta farko a yankin bakin teku na ƙasar tun a shekarar 1874.

Ya kuma ƙara da cewa wani abu da ya ƙara sanya Hausawa musulmai suka guje wa karataun Boko tun da farko shi ne a makaratun mishan - da aka fara buɗewa a kusa da zangoninsu - "akan tilasta wa ɗaliban makarantun ɗaura alamar gicciye (kuros), kuma duk ranar Lahadi dole ɗalibai su je coci".

''Har sai bayan samun ƴancin kai, zuwan shugaban Kwame Nkurma ya soma kafa makarantun ƙasa, sannan aka soke waɗancan dokoki, daga nan ne kuma Hausawa suka soma tunanin sanya ƴaƴansu a makarantun bokon'', in ji shi.

Ya ce ba ilimin zamanin ne Hausawan suka guje wa tun da farko ba, "al'adun addinin kiristanci da ake cakuɗawa a makarntun Turawan suke guje wa."

Sai dai a cewarsa, yanzu haka Hausawa sun dage a ɓangaren karatun boko, "yanzu babu wani gida da za ka je ka ga babu mai digiri ɗaya ko biyu."

Tagomashin harshen Hausa a Ghana

Duk da cewa babu wata jiha guda ɗaya tilo da za a iya bugun ƙirji a ce ta Hausawa ce a ƙasar Ghana, amma da wuya a samu gari ko ƙauyen da ba a magana da harshen na Hausa.

Kamar yadda aka san harshen Hausa da mamaya tare da haɗiye ƙananna yaruka, haka batun yake a ƙasar Ghana inda harshen ya shiga cikin harsunan ƙasar da dama ya kankane.

Alhaji Baba Sharif ya ce kusan duka ƙabilun da ke arewacin ƙasar, da arewacin Togo da Nijar da Benin da Mali da Burkina Faso da Gambiya da Senegla da ke rayuwa a cikin ƙasar Ghana suna magana ne da harshen Hausa.

Ya ƙara da cewa baya ga waɗannan, duk wasu ƙabilu da ke da alaƙar tsatsonsu daga Najeriya za ka tarar sun iya harshen Hausa kuma suna magana da shi.

''Alal misali duk wani Bayarabe da aka haifa nan Ghana ya iya Hausa kuma yana magana da shi, ya fi iya Hausa maimakon Yarabancin'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa da harshen Hausa aka yi amfani wajen yaɗa addinin musulunci a ƙasar, musamman kudancin ƙasar, don haka ne ma ya zama harshen da duka musulmin Ghana ke magana da junansu da shi.

''A kudancin Ghana kusan duka masallatan yankin idan ka je za ka tarar kashi 95 na huɗubarsu da harshen Hausa ake yin su, duk kuwa da cewa asalin limamain ba Hausawa ba ne'', in ji shi.

Alhaji Baba Sharif ya ce duk ɗan wata ƙabila da ya je karatu ƙasashen Larabawa, to idan ya je ƙasar domin yaɗa da'awar Musulunci, dole ne ya yaɗa shi da harshen Hausa.

''Idan babu Hausa ko kaɗan ba za ka iya yaɗa da'awar musulunci ba, don haka dole ne ya koyi harsen Hausa'', in ji shi.

Harshen Hausa a kafofin yaɗa labarai

Shugaban gidan rediyon na Marhaba FM, ya ce tun lokacin da aka fara buɗe gidan radiyo a Ghana a shekarar 1935 lokacin Turawa "da harshen Hausa aka soma yaɗa shirye-shirye".

''Ko a kwanakin baya ma hukumar kula da kafofin yaɗa labaran Ghana ta gudanar da bikin cika shekara 99 da fara yaɗa shirye-shiryen radiyo da harshen Hausa'', kamar yadda ya bayyana.

Ya ce an samu tasoshin rediyo masu ɗimbin yawa da ke yaɗa shirye-shiryensu da zallar harshen Hausa.

Harshen Hausa ya shiga yarukan hukuma

A gwamnatance ya ce babu wani abu da za a yi a ƙasar ba a sanya harshen Hausa a ciki ba.

Tun shekarar 1874 sojojin ƙasar ke amfani da kalmomin Hausa wajen tsuma kansu da aika saƙo.

''Akwai Infantry Brigade da ke wajen birnin Accra, a ƙofar shiga barikin ko yanzu ka je za ka tarar an rubutu kalmomin ''Kullum Shiri'', waɗannan kalamai suna nan har yanzu''.

Haka ma ya ce a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu sojojin ƙasar Ghana da suka je, duka alƙawuran da aka yi musu da ba a cika musu ba a 1948, sun shirya zanga-zanga da suka yi wa Turawan mulkin mallaka a lokacin, kuma duka waƙoƙin da suka rera a lokacin da harshen Hausa suka rera su.

Haka kuma ya ce a ƙarƙashin dokokin ƙasar, harshen Hausa na daga cikin harsunan da aka amince a yi magana da su a zauren majalisar dokokin ƙasar.